_YA ZANYI_
_(FARIN CIKIN ƳATA SHINE BURINA)_BY.
_Husaeenah b. Abubakar_
_(Mrs Abubakar)_
*DA BAZARMU WRITTER'S ASSOCIATION*
🅿2⃣
" Ƙyakykyawar yarinya ce ta bugawa a jarida, ta haɗu ta ko ina babu abinda bata mallaka ba na cikar halitta, duk wani abu da ake nema a wajen ƴa mace yarinyar na dashi, cikin izza da taƙama take takowa babu fargaba ko shakar wani a tare da ita, sai da tazo dai-dai saitin su sannan ta saki wani mummunan tsaki cikin ƙaramar murya ta tace" Umma! ni zan wuce!!.." tamkar bata gan shi ba haka tayi maganar...
Cikin sauri ta share hawayen ta murmushi dole ta ƙaƙalo sannan ta juyo a sukwane tana me washe baki tace" My baby har kin shirya? to ki gaida min da ita sosai kice nima ina nan zuwa!!..."
Ko ƙala bata ce ba ta juya zata wuce Sauddat ta ɓata fuska muryar ta a sanyaye tace" shin baki ga Abbanki bane zaki wuce ko gaisuwa babu ?!.."
Cak ta tsaya zuciyar ta na tafasa a fusace ta waigo idanun ta har sun sauya colo tace" mijinki dai Umma! amma ni bani da wani Abba a duniya ta!..." Cikin sauri ta fice a falon gudun kar tayi abun kunya a gaba mahaifiyar ta, me gadi na hango ta ya miki da sauri get ya buɗe mata domin yafi kowa sanin wacece ita a wajen masifa, tamkar zata tashi sama haka ta figi motar, wasu hawaye ne masu zafin gaske suna zubo mata....
Kunya ce tayi bala'in kama ta a wajen ta kasa motsi, ya fahimci halin da take ciki shi ma, in da sabo yaci ace ya saba da halin yarinyar nan, sai ya ɗaure duk da baiji dadin furicin ta ba, ta baya ya rungume Sauddat muryar shi a sauƙaƙe yace" ASIYA! yarinya ce ƙarama har yanzu bata gama mallakar hankalin ta ba, karki damu da abinda tace a hankali zata fahimci matsayi na!.."
" Har sai yaushe zata fara jin magana ta? kullum burina shine na faran ta mata, me yasa ni baza taso abinda nake so ba? nifa uwace a gare ta Aliyu!..."
" Nafi kawo sanin kina mutuƙar ƙoƙari wajen bata tarbiya, karki gaza ki daure wata rana sai labari, shawara ta ɗaya a gareki shine ki rage nuna mata ƙ'auna a zahiri!..."
Dumm gaban ta ya faɗi ba shine karo na farko da ya taɓ'a gaya mata wannan kalamar ba, ta yaya zaka guji abinda shine farin cikin ka?...
" Ba ina nufin ki guje ta bane a'a ina so a koda yashe ki na nuna mata kusƙuren ta komai ƙanƙantar sa! ba komai yara suke nema a wajen iyayen su su samu ba, musamma yara mata a yanzu abune me yuwa ta gyara wasu d'abi'u nata sabida akan haka kuka ɗorata tun yarinta, Sauddat bani da niyar cutar daku kamar yanda bazan so a cutar min da nawa yaran ba, ki jajirce wajen gyara halaiyar ƴarki sosai rayuwar ta tana buƙata gyara! zan jira nan da wani lokaci ko Allah zai sa ku gane d'aga ke har ita! taimakon ku zanyi nima baa son raina nake zaune a gidanki ba!!..."
Har yanzu kallon shi take cike da ruɗ'ani to ya su ke so tayi ne wai? Asiya itace farin cikin ta so ake ta matsa mata ko me? tafi kowa sanin soyayyar da take ma Abban Asiya itace ta dawo kan Asiyan baki ɗaya, kishin da yake dashi shi ƴar sa ta ɗauko sam bata ganin lefin ƴarta, matsala ɗaya shine bata iya riƙe ɓacin ranta, wannan kuma halittace bata isa ta sauya ta ba! _YA ZANYI_ ne wai??
Shi kam ya gama faɗ'ar abinda ke bakin shi, in zuciyar sa za'a tona akwai maganganu iri-iri wanda wani ma baya ƙaunar tuno su, gaba ɗ'aya yarinyar bata da kunya...
" Ina ƙaunar ki sosai Umma! amma ke gaba ɗaya bakya gani, ina jin zafi sosai a zuciya ta in naga gilmawar ki da wani a matsayin ki sake wani auren? shin me yasa bazaki haƙuri ki zauna ke kaɗai ba, me kika nema kika rasa? ABBA ya soki kamar ranshi ya sadaukar da rayuwar shi sabida ke! me yasa kema bazaki haƙuri ki zauna haka kawai ba? zanyi kishi da duk mijin da kika aure har sai ya gaji ya sauwaƙe miki! mijiki na farko ya azabtar dani kamar hauka, ya mayar dani baiwa ya lalata min rayuwa ta duk wannan bai isheki ba, sai da kika sake aure bazan kyale ku ba wallahi!..."
Ta sake sakin wani marayan kuka, zuciyar ta na zafi tuno da mummunan tabon da mijin babar ta yayi mata, a dadafe ta isa gidan Hajiya hawaye na gudu akan ƙ'uncin ta...
Comments
Din ku shine burina nima🥰
Duk wace ta karanta tayi shared please
Kuci gaba da kasancewa dani a cikin wannan tafiyar domin jin yanda zata kaya...
Taku ce har kullum
Mrs Abubakar ce

YOU ARE READING
YA ZANYI farin cikin yata shine burina
Short Storylabari ne me tab'a zuciya hadi da cakwakiya me zafi