Chapter 10

8 0 0
                                    

_YA ZANYI.?_
_FARIN CIKIN ƳATA SHI NE BURINA_

By.

_Usaeenah b. Abubakar_
_(Mrs Abubakar)_

🅿1️⃣0️⃣

A ƙwance take a jikin Hajiya hawaye na zuba a idanun ta, cikin sanyin murya tace" banyi tunanin abinda ta faɗ'a zata iya aikata shi ba Hajiya, ina san Asiya so me tsananin ina ji a jikina in narasata mutuwa zanyi, me yasa zata tafi ta barni ? me nake mata wanda bai mata daɗi ? ita yarinya ce ƙarama Hajiya, nafi kowa sanin halin da nake ciki so take naje na aikata kuskure da girma na?..."

A hankali Hajiya tace" me yake faruwa ne Sauddat?.."

Cikin kuka da nuni da hannu ta gaya mata duk abinda ya wakana a tsakanin su, a ƙarshe tace" dole ne nayi aure Hajiya nima ba wai dan ina son shi kamar Abban ta zanyi ba, zanyi ne kawai sabida larura dan Allah ki amince dani!!.." ta faɗa tana roƙo hannun Hajiya cike da marairaicewa..

Kare mata kallo tayi cikin nazari tace" ba wai zan tauye miki hakin ki bane Sauddat yana da kyau ko zakiyi auren ki bari sai kin mika ƴarki gidan mijinta, ita ƴa macece ASIYYA tana buƙ'atar kulawar ki fiyye da ta kowa a duniya, kibi shawara kiyi haƙuri da maganar aure!..."

" Hajiya aure na ba wai yana nufin zan banzan tar da Asiya bane, aa ina tare da ita a koda yaushe kuma Salisu yana ƙaunar Asiya tamkar ƴar cikin sa, na san bazai taba cutar da ita ba, kuma fa a gidana zan zauna ba wai gidan shi zan bishi ba, dan Allah ki amince dani Hajiya!..."

" Ni dai shawara na baki in kin ɗauka kanki, inƙi ma ruwanki ki tashi kije ki nemo musu yarinya bana son wannan maganar!..." daga haka ta miƙe ta wuce ciki abinta zuciyar ta cike da sake-saken Ina na tafi?

Na gama cin abinci kenan Hajiya babba ta shigo cike da soyayyar data take kallo na, a wayence ta goge hawaye dake bin ƙuncin ta, gefe na ta zauna cikin hikima tace" ƴar gatan mu! ki saka hijabin ki zamu shiga gidan Hajiya, tunda kikazo baki leƙata ba haka ma Umman ki bata zoba kamar yanda ta saba, ina ji a jikina ba lafiya ba duk da kin ki gaya min gaskiyar abinda ya kawoki!..."

Murmushi nayi nima Ina ƙaunar tsohowar nan domin ta iya bi da mutun duk ta inda yazo mata, nace " Hajiya  dan Allah ki barni ni ba zani ko ina ba!.."

Nan ta sakani a gaba da lalashi cikin kalamai masu daɗi wanda dole zuciya ta karaya da kai na na shiga bata labarin halin da nake ciki, a ƙarshe nace" Hajiya bana son Alhaji salisu Ina mishi kallon mugune ɗ'aga yanayin sa na gane ba son Umma yake da zuciya ɗaya ba, gaba ɗaya yanzu ya sauya ta, bata kula da kowa sai shi shi kaɗai take bawa lokaci me tsaho yanzu, ko ɗakin na bata zuwa hira kamar dah, duk daren duniya wayace abokiyar hirarta bata  damu da halin da nake ciki ba, Hajiya ko tahowar nan tawa da nayi mata sallama amma ko amsani batayi ba, a haka nee take so na? wannan shine alƙawarin da ta ɗauka? tun yanzu ma ana haka ya kike ganin inda ta aure shi? dan Allah Hajiya ki ƙwaceni!.."
cikin kuka na karke maganar...

Tausayi na ne ya kamata, bata ce min komai ba sai rarashi na da take sai da taga nayi shiru sannan tace"  amma kin san hukucin wanda ya aikata Zina ko?.."

Eh nace cikin muryar kuka, ta ɗora da cewa" so kike Umman taki ta kasance a cikin su? da sauri na girgiza kai alamar aa tace yauwa abinda nake so dake a nan, ki kasance me mata fatan alhairi a ko da yaushe, kiso abinda take so ko dah hakan zai taba naki farin ciki ne, iyaye ba abin wasa bane ki kasance me biyayya duk runtsi kar ki raina ta, ita uwace tana da ikon tayi duk abinda ya dace akanki, na san Sauddat kware da gaske tana sonki tana ƙaunar ki, ko a yanzu ina ji a jikina duk inda take hankalin ta da nutsuwar ta yana  tare dake, kin san soyayyar dake tsakanin  uwa da ɗa kuwa Asiya? ki shiga nustuwar ki ki nemin yafiyar ta, baki kyauta ba da kika guje mata, aure kuma da kike magana akai Allah ne ya halata mata shi babu wanda ya isa ya hanata, tashi ki ɗauki kayan ki na mayar dake gida yanzu ko ta samu barci cikin nutsuwa..."

Cikin sanyi take min maganar amma ita a wajen ta faɗa take min, shiru nayi ina sake sakin wani kukan, ganin da gaske nake bazani ba ta sake sadakarwa zuciyar ta ba ta inda na bar mahaifina, shima haka yake lokacin da mahaifin su ya rasu, ƙimeme ya hanata aure nan ta sakani a gaba da nasiha ta sake nuna min illolin da zan jawo mata, akan dole na haƙura hijab kawai na saka ko wayata ban ɗauka ba, cikin turo baki gaba nace" to muje!.."

Dariya na bata tana ta tsokana ta har muka fice a gidan, ita ta fara shiga ni kuma na makale ɗaga bakin ƙofa, a taƙure ta hangi Sauddat ta kifa kan ta jikin kujera tana rere kuka cike da baigen ƴarta, sabahallah shine abinda ta furta cikin sauri ta isa gare ta a hankali tace" Sauddat!!.."

Da sauri ta ɗago ganin Hajiya babba ba ƙaramin tsoro ne ya kama ta ba, ta shiga goge hawayen ta tana ƙoƙarin aza murmushi a fuskar ta, murya a dakushe tace" ina wuni  Hajiya?.."

Bata amsa ba ila cewa da tayi" hakan ya sake tabbatar min da cewa zaki iya  komai akan Asiya! Sauddat ƴaƴa amanace da Allah ya bamu kuma ranar lahira sai an bincike ki akan wannan amanar da Allah ya baki! me yasa kike son kuntatawa ƴarki ɗaya lelo da Allah ya mallaka miki? Asiya tana buƙata kulawar ki fiyye da ta kowa a duniya har ni kai na kuwa, kema kuma kina buƙatar ƴarki a kusa dake, dube yanda kika dawo a ƙwana biyu kawai da bata kusa dake..."

A nan Hajiya babba ta saka Umma gaba da kalaman ta maso kashe jiki da zuciya, a ƙarshe ta sheda mata tana goyen bayata da tayi auren ta amma sai tayi mata alƙawarin bani kulawa har aure na,  ita kanta Hajiya babba hawaye take domin yaron ta ke faɗo mata arai,  sosai ta nunawa Sauddat yanda maraya yake da kishi a yanda take mata musali ma, ace itace ta mutu ba ABBA ba to ba makawa duk matar da zai auro ni zan zamo mata kishiya, tunda gado nayi a wajen ABBA na...

Cikin mutuwar jiki tace" insha Allah Hajiya bazan sake bari wani abu makamancin haka ya sake faruwa ba, zan bata kulawa da duk kanin ƙarfin da Allah ya bani, ki tayani bata haƙuri dan Allah?..."

Murmushi tayi kana tace" ba haƙuri tsakanin uwa da ƴa, ke dai kici gaba da kulawa da rayuwar ku, Allah yayi muku albarka ni zan wuce...

" Ameen Hajiya na gode na gode sosai Allah ya kara lafiya da nisan ƙwana, bari nayi ma Hajiya magana!.."

" Ba komai ƴata Allah ya zaɓi miki abinda yafi zama alhairi, ki bar Hajiya zanyi zuwa na musamma ina da magana da ita.."

Har ƙofa ta rakota abin mamaki babu Asiya a wajen, Hajiya bata nuna a fuska ba har ta shiga gida, a Falo ta  tarar da ita zaune tana  aikin kuka, bata ce mata komai ba sai kayan ta da ta shiga ɗ'akin ta dauko babu umm babu umum ta ajiye mata a gaba ta tace" ɗauki ki tafi Sauddat na jiranki!.."

" Hajiya kin gaji da gani na ne?.."

Murmushi tayi kana tace" zanfi kowa farin ciki idan zaki zauna a tare da ni, domin ina ji tamkar Jabeer ne a gaba na, amma duk soyayyar da zan nuna miki ba a bakin komai take ba in aka haɗa ta da ta Sauddat domin ita uwace, ki tabbatar kiyi abinda nace miki Asiya!..."

Rungume ta nayi ina hawaye har kofa ta rakoni sai da ta tabbar da na shiga gidan sannan ta koma ciki zuciyar ta cike da kewa ta...

Kai na a ƙasa na shigo falon sai kallon gefe nake, da wani irin sauri Sauddat ta mike tamkar zaa sace ni ta wani yo wajen bakin ta na furta Alhamdulillahi ta rungume ni, ba karya nima nayi missing din my sweet mom dinna, amma na fuske naki rungume ta, kissing ta shiga manna min tana saka min albarka, nayi ƙikam a waje guda ina kallon ta...

Comments

Shared please duk wace ta karanta....

Mrs Abubakar ce

YA ZANYI farin cikin yata shine burinaWhere stories live. Discover now