_YA ZANYI.?_
_FARIN CIKIN ƳATA SHI NE BURINA_By.
_Usaeenah b. Abubakar_
_(Mrs Abubakar)_🅿3⃣5⃣
Gaba d'aya wajen ya d'auki tafi tambayoyi fal zuk'atan mutane, cikin sauri na dauke y'ata muka bar wajen dukko da irin kiran da ake mun, ranar haka na wuni sukuku, yarinyata kam ta wuce gidan Hajiya ban damu ba domin ina bukatar hutu nima, washe gari da sasafe Ummana ta kirani na dauka muryata a dakushe na gaidata shirune ya biyo baya na wani lokaci zuwa chan tace" Baby yaushe zaki dawo gida?.."
" zanzo amma ba yanzu ba.."
" a'a na san kina bukatar hutu kizo dawo gida yau kinj!!." "Umma!! bana son abinda zai d'aga miki hankali a halin yanzu dan Allah ki bar maganar zuwa ba yanzu ba!.." "Ok ina fatan kina cikin farin ciki ? ya khausar?.."
Na amsa mata da duk lafiyar mu lau, sallama mukayi da ita inda akarshe na ajiyar wayar, shiru nayi ina tunani tashin hankalin da na shiga a lokacin da zamu shiga office menene matsala ? Me yake shirin faruwa dani? gaba d'aya na mayar da hankalina kai abun!..Tamfatsitsin gida ne na gani na fad'a, duk wani jin dadi na duniya a zuba shi a cikin sa, babban falon ne wanda yake dauke da satin kushin biyar kuma ko wanne da bangaren sa, wani had'ad'an gaye ne a zaune cikin wata luntsimemiyar kujera me bala'in laushi da santsi, wata karamar yarinyace ke wasa a kusa dashi ta rarafo wajen kafarsa tana washe baki ta kamo gefen wandon sa cike da yarinyata tana son mikewa tsaye, cikin wata dakakiyar murya ya kwala mata kira ran shi na k'una, tamkar wanda wani mugun abun ya tab'a shi, ya sake cewa" Sarah!! Sarah!!.."
Da gudu ta fito a d'akin ta kamar zata fad'i jikinta sai b'ari yake cikin karkarwar baki tace" gani yallab'e." Cikin tsawa yace" dama na kiraki ne dan jin dadi ko baki san maanar kiran ba da zaki tsaya mun kai, zakizo ki dauke shegiyar yarinyar nan taki ne ko sa na had'aku na ci ubanku!.."
Idanunta ne ya sauka a inda Khausar take jikinta na rawa ta sunkuya domin daukar y'ar cikin kwarewar mugunta ya take mata hannu da kafar shi har da murzawa, ta saki wata gigitaciyar kara sabida tsanani azaba da hannu daya ta dauki khausar dake kuka gani uwarta nayi, Cikin zubar da hawaye tace" ka gafarce ni Fauwass! wallahi ban san ta fito ba , nayi alk'awari bazan sake bari haka ta faru ba!.."
" Good!! da kinyi kyan kai!.." yana dauke kafar sa ta mike da sauri ta bar wajen jikinta na kad'awa, hannunta na zugi..Ko da ta shigo daki kuka take kamar ranta zai bar jikinta bayan ta samu yarinyar tayi shiru tana shan mama, ta dube hannunta hawaye na digowa sannan ta dube yarinyar dake shan mama hankalinta a kwance, kukanta ya karu akan na farko cikin sharb'e tace" Allah ya raya min ke cikin aminci, Allah ya bani ikon jurewa Allah ka yafe mun Allah ya baiyyana gaskiya, Ya Allah kana ganin halin da nake ciki ba danni ba ba dan na isaba, Allah dan fiyyanyyen halitta ka dubu lamarin mu, Allah kaga zuciya ban da niyya nayiba ya Allah ka taimakeni!..." Ta sake fashewa da kuka me cin rai musamma da ta tuna dalilin da kukanta...
Yarinyar dake cinyata ta sa hannu kamar ta san uwar na kuka ta share mata hawaye cikin tsagwaron shirme tana ta gwaranci kamar me magana, kaunar yarinyar ne ya sake cika mata zuciya ta sake rugumera tsam a jikinta tana jin kaunarta na ratsa mata jini da jijiya...
Wayar sa ya dauka bayan barinta wajen, wani karamin video abokin sa hamza ya turo mai, siririn tsaki ya saki har ya fice a ciki sai kuma wata zuciya ta bashi shawarar budewa, budewa yayi ya fara kalla sam baya gane me take nufi, shiru yayi game da lumshe idanun sa a hankali sauttin kukanta ya fara fita cikin sauri da barin jiki ya mike zaune da kyau yana daukar wayar hannun shi har rawa yake, sabida tsabar kaduwa bai gama fahimta ba kiran waya ya shigo wayar tashi, tashin hankali wanda baa saka mai rana sai gashi yana gumi zufa na karyo mata ta ko ina, jikinsa na rawa kamar bazai bari ba, ya katse kira cikin azama so yake yaga fuskarta amma ina ba hali domin ta sunkuyar da kainta kasa, kitt video ya yake....
Shiru sauddat tayi lokacin da Aliyu ke mata bayanin abunda ya faru jiya, ta sake fad'ad'a murmushinta a lokacin da taji y'ar ta ta samu gurbin zama cikakiyar y'ar jaridda, tace nuna mun abinda ya faru jiyan?.."
" Ok matsu to!.." ya fad'a yana dago wayar sa..Ina kwance kiran waya ya shigo mun cikin murna da jin dadi na ajiya wayar sai na nemi damuwata na rasa gaba daya, dadi ya maye gurbin su ina cikin wannan halinne khausar ta shigo, da sauri na dagata sama ina juye cike da murna ina mata wasa aiko muka shiga kyakyata dariya kamar mahaukata, a haka Kaka da hajiya suka same mu ko wace ta saki murmushi, zuciyarsu fal farin ciki...
Gaba d'aya na ajiya damuwa da tunani a gefe na saka aikina a gaba ba dare ba rana tunani yanda zan zamo wata nake, a duk lokacin da zan tafi shigar da nake me daukar hankalice jikina wani mayyen jikina wanda duk irin kayan da na saka sai ya amsheni ni kaina ina mamakin sauyawata, a yanzu rashin kunyar da akw ganina da ita na ajiyata a gefe Khausar y'ar ta kullum da tsarabar ta sai dai in ban samu fita, labare iri-iri nake samu musamma masu irin matsalata wani abun in naji sai naga ni ba komai bane nawa matsalar, na sake samu matsayi sabida kwarewata daga karamar maaikaciya na zamo sakatariya a yanzu ba ko yaushe nake samu zama ba yau in muna chan goba muna nan..
A yau ne na samu damar ganawa da babban manajen ba laifi na

YOU ARE READING
YA ZANYI farin cikin yata shine burina
Short Storylabari ne me tab'a zuciya hadi da cakwakiya me zafi