_YA ZANYI.?_
_FARIN CIKIN ƳATA SHI NE BURINA_By.
_Usaeenah b. Abubakar_
_(Mrs Abubakar)_Jin kaina ya fara sarawa ga wani irin ciwo da yake min, dole na tashi a wajen wanke fuskata nayi ina karewa kaina kallo a hankali na shafa inda shatin hannunta ya kwanta mun, hawaye masu zafi suna sake bin kuncina cikin wata dashashiyar murya nace" Yaushe zanyi farin ciki!..
Sauddat wayarta kawai ta dauka sai tarkacenta na zuwa aiki, ba wanda tayiwa sallama ta fice a gidan kai tsaye gidanta ta nufa zuciyarta a cunkushe, tamkar da mutane a cikin sa komai tsaf yake kamar sun san yau zata dawo, d'akin ta wuce bakin ta d'auke da addu'a...
Kimanin kwana biyu kenan ban saka Ummata a idanuna ba, gashi sai bin umarnita nake tsakanin da yarinyata shayarwa kawai da nagama bata zan ajiyeta na fice, fahimtar me nakeyi ne yasa Kaka take zama a kusa dani..
Hajiya ce ta shigo domin itama ta koma gidanta, yarinyar ta dauka cike da nuna mata kauna take mata rawa da wak'e-wak'e su irin na tsufafi, a cikin wak'en nata naji sunan yar tawa...
Ajiyar zuciya na sauke cikin raina ina jin dadi a hankali na maimaita KAUSAR!! sunan ya dace da ita sosai..
Hajiya ta dube Kaka cike da girmamawa tace'" Niko Sauddat tazo? naji anace ta koma bakin aikin ta tun ranar Monday, ga Kausar na buk'atar wasu kayan..."
Murmushi Kaka tayi kana tace'" Ok Allah ya taimaka, zan bada a siyo mata ki fita a zance Sauddat zata dawo ne, niko kina kula da yanda Kausar take sauya kamannin?"
Shiru nayi ina sauraron su "eh na kula wallahi, gaba d'aya yanzu ta chanza da farko kamar baby amma yanxu na ma rasa da wanda zan dangata..."
" Dariya tayi kana tace" Allah yasa ta kamanin ta ubanta ya bayyana..."
Cikin sauri na miki a wajen, d'aki na na shige domin nima abinda yake damuna kenan, nak'i barin zuciyata tayi wanna tunaninne sabida gudun wata matsalar, ina Ummana ta tafi? yanzu duk da nayi mata biyayya sai da ta tafi ta barni? wai yaushe zata fara sona ne? akanta na rasa duk wata kimata da daraja irin ta y'aya mata masu mutunci, akanta rayuwata ta shiga garari, me yasa bazata jure abinda nake ji ba? shikenan ni kullum akan k'aunar ta zan iya komai amma banda ita! akan mahaifiyata na zab'i rabuwa da y'ata duk da irin matsanancin k'aunar da nake mata, sabida farin cikin ta kawai yar cikina fa?..."
Wani irin kuka ya kufce mun hawaye masu zafi na zuba mun, Ya Allah ka bani ikon cinye wanna jarabbawar! Allah ka zab'a mun mafi alkhari a rayuwata!...""
Suko su Kaka suna waje sai duduba KAUSAR suke ko zasu ga wani abu a jikinta, amma kalau da ita...
Watanin sun jah kamar yanda kwanaki suke gudu, Allah cikin ikon sa yanzu K'ausar na da wata goma sha d'aya cif, yarinyace me wayon tsiya a yanzu nono na baya isarta kunu Hajiya take bata, wani lokaci sai ta wuni bata sha ba tana can gidanta, niko in ba nononne ya isheni ba bana zuwa inda take ko nemanta, kewar Ummana ke damuna duk nabi na zafge ba kamar farkon jigona ba, a yanzu kullum lefina nake gani...
Muna zaune da Kaka fuskar nan tawa a had'e domin yanzu ko su sun saba da da fushina, a zaune kawai nake amma zuciyata batayi min dadi, gyara zaman tayi cikin sanyi murya tace'" baby! wai har yanzu baki gaji da zama wuri d'aya ba? ya kamata ki fara aiki tunda kinga tun kafin wanna tsautsayin takarddunki sun jima da fitowa gashi shekaru kara jah suke, kina buk'atar abokin rayuwa sannan abinda nake so dake dan ALLAH ki rage tsangwamar kainki da kike haka ba dai doctor ya sheda min da bakin shi baki da ciwon komai ba, tsaf zance ciwon zuciya yajima da kamaki, dan ALLAH ki saki ranki ASIYYA!.."
Ko kallon inda yake banyi ba a hankali nace" ban fara wanna mafarki ba tukuna, abinda yasa na zauna a falon ma ina so na sheda muku ne na yaye K'ausar d'aga yau, tunda nonon ma sau d'aya take sha a rana...
YOU ARE READING
YA ZANYI farin cikin yata shine burina
Short Storylabari ne me tab'a zuciya hadi da cakwakiya me zafi