_YA ZANYI.?_
_FARIN CIKIN ƳATA SHI NE BURINA_By.
_Usaeenah b. Abubakar_
_(Mrs Abubakar)_🅿39
Cikin ladabi da biyayya na gaida su, amsawa sukayi cikin jin dadi, kunyar su ta hanani yin abinda nayi niyya, kawai sai na sake hannun khausar gami da fad'i taje cikin makaranta, to tace tana ware hannuwanta gane me take nufi yasa na rungume ta tsam a jikina kana na sakar mata kiss a goshinta, aiko ta juya ta tafi cike da farin ciki sai yan tsalle² take irin nasu na yara...
Daka nan wajen aikina na wuce nima zuciyata fal farin ciki, dai¹ shiga office zuciyata tayi wani mugun zullo game da dukawa da karfi, gefe na tsaya ina duk addu'ar da tazo bakina, na jima a haka kafin naji wata nutsuwa da k'warin gwiwa yana zuwa min, karfin hali nayi na wuce ciki bakina d'auke da salama...
Ni a wajena a mutuk'ar tsorace nake amma a zahiri za kayi tunanin wani salon tafiyar ne nazo dashi, gashi na sha dogowar riga nayi nad'in tamkar balarabiya, fuskata sai shek'i take da annashewa, a tsaye³ na samu abokan aikina da alama shugaban mune ya shigo domin shi kad'ai akewa irin wannan tsaiwar, ban tsaya jin me sukayi ba na wuce office dina domin ajiye kayan aikina, a yanda nake gifftawa ta cikin su zaka dauka ni wata babbace a wajen, kowa kallona yake cike da mamaki wanda suka san ban san waye a wajen ba kuma suna tausaya mun irin hukunci da zaa yanke mun...
Gani ina da aiki sosai yasa na tsaya na rage wasu kafin na fito, maryam dake kusa da office dinna kuma muna mutunci sosai na gani a tsaye a gaban wani kanta a kasa sai hawaye take sharewa da bayan hannunta, cike da hargowa da nuna isa ya sake zafga mata mari a karo na uku kenan, cikin abinda bai wuce saa d'aya na isa inda suke ganin yana niyyar kara mata wani kuka duk cikar mazan wajen da matan ba wanda yayi k'wak'awaran motsi bare ya hana shi, maryam ta sake sunna kai kasa cike da tsananin jin zafi da zugin tana jiran saukar marin sa, amma sai taji shiru sakamakon damke hannun nashi da nayi cike da karfin hali nace" meye haka? waye kai? me tayi maka da zafi haka da bazaka iya hakura ba sai ka tab'a lafiyar ta? shin baka san ita macece me rauni ba? tukuna ma waye kai?.." Na fad'a cikin izza da nuna isa!!!..
Tsira mun manya idanun sa yayi babu ko kifftawa zuciyar sa na wani irin rawa, tabbass itace eh kware itace yanzu ya sake sheda hakan sabida had'uwar hannun su waje guda, kad'ai ma yatsa tayi cikin bacin rai tace" ba tambayarka nake ba ka tsira mun ido kamar kana kallon TV?.."
Lumshe idanunsa yayi cikin jin wani yanayi na daban a zuciyarsa a hankali ya sake ware idanun shi akanta fess yana kallonta, ita kanta sai yanzu ta gane shi cike da kufula tace" au dama kaine? Ashe haka kake? me ya kawo ka wajen aikina? me ya had'a ka da abokiyata? waya baka izzin marin ta? tukuna ma kai din waye ne wai da kake bibiyar rayuwata?...
Ko wanne ma'aikaci a tsorace yake da abinda zai biyo baya, niko gyara tsiwata nayi cike da kwarin gwiwa, a hankali yace" ki tambayi abokan aikin naki waye ni!!.." Cikin sanyi yayi maganar wanda yaba jamaar wajen mamaki..
"Me yasa ka mareta? shin baka da mata? in baka da mata baka da kanwa? ko mahaifiya ko y'ay'an yan uwa? na dai san bazaka rasa daya a ciki ba, meyasa bakwa tausayin mata ne yanzu duk girman laifin da tayi bazaka iya hakuri dashi ba har sai ka tab'a lafiyar? wai baka san ita din uwa bace ya kake tunani inda yaronta ya ga abinda ka aikata? me yasa ko da yaushe mu akafi cutar wane? malam ka bata hakuri da alkawarin bazaka sake ba!.."
Gaba d'aya na kashe mai jiki, maryam kam tsoro ne ya kamata jin nace a bata hakuri tayi saurin cewa" Anty khausar! shi ne babban manaja a wannan kamfanin kuma na mahaifin sane, in dai dan nice na yafe masa muje ko!.." ta fad'a tana kamo hannuna..
Kallon sa nayi kafin nace" ka kiyayye gaba dan kana manaja bashi ba ka damar marin matar mutuane ba, dan yawa irin ku haka kuke da d'agawa akan dukiyar da bata ku ba, ka guji had'uwar mu dakai a nan gaba..."
VOCÊ ESTÁ LENDO
YA ZANYI farin cikin yata shine burina
Contolabari ne me tab'a zuciya hadi da cakwakiya me zafi