_YA ZANYI.?_
_FARIN CIKIN ƳATA SHI NE BURINA_By.
_Usaeenah b. Abubakar_
_(Mrs Abubakar)_Runtsi idanunta tayi tana jiran saukar marina, a hankali na saki siririn tsaki kana na koma na kwanta, a zuciyata ina jin dadin ganinta wani bangare kuma yana jin kona da rarad'ad'inta, gadon ta hayo tana dariya cike da hard'ewar zancen ta tace" Antii aaniya! oyoyo!.."
A hankali na tureta ina cewa" jeki wajen mamanki ni barci zanyi.." Nok'e kafada tayi tana hawaye tsawwa na azamata cike da masifa nace" fice mun a daki dan ubanki ko na yanka ki!.." Abin tausayi da sauri ta sauka ta fice ko waigowa batayi ba, tana fita sai naji ina ma banyi mata haka ba, tashi nayi zan biyo bayanta aka kirani a waya Ummace yamusta fuska nayi zuciyata a jagule na kara a kunnee na..
"Hello babyna kina jina ? Dama zance miki Khausar ta'ki zama ki shirya zuwa Monday Abbanki zaizo ya daukoki, baya son jira Asiya ki shirya tun kafin ya iso na fadawa Kaka babu matsala kina jina kuwa?"...
Sai a lokacin na magantu cike da jin haushinta tace" Abbana kuma? wanda ya mutu yana dawowa ne?.."
" Asiya bana son sakarci, kiyi abinda nace kawai in kuma bakya son zama dani ne to ki fada mun.""
"No zan shirya Allah ya kai mu..."
Kafin tayi magana na katse kiran, wurgar da wayar nayi ina tunanin mafita...
A cikin satin nan gaba daya khausar ta bace mun bana ganinta ko a falo, da farko nayi tunanin ko bata da lafiya to har gidan hajiya na shiga amma ban ganta ba, kuma hajiya batace min komai ba, ga nauyin baki na da bakar zuciyata nak'i tambayar ina take, har Monday din tayi...
Mutun kamar mayye da sasafe dan ko7:00 bata karasa ba sai gashi a kofar gida wai na fito, nace to sannan na haye gadona barci me dadi ya dakeni bani na tashi ba sai wajen 9:00 lokacin Kaka ta gama kulewa dani domin bugawar duniya sunyiwa dakina nak'i budewa, shi kuma kamar mayye yak'i tafiya yana waje y'ar uwarsa wato hajiyan jabeer, wajen shirin kayan nawa ma na dauki lokaci sosai kafin na fito nan ma nace sai na karya zan tafi ba yanda sukayi dani dole suka zuba mun ido...
Kayan na ajiye a falo na wuce na bude gidan baya na shiga a tsakiyar kujerar na zauna ina me bubud'ewa ni a lallai zanyi wulakaci, amma sosai abin yayi mun kyau ya kuma hau da yanayi na, Kaka ta bude baki zatayi magana Aliyu ya rigata da fad'i " Hajiya ba wani damuwa bane mafakasari yara sunfi son zaman baya, akan gaba ko dan kalle-kalle, mun mun wuce"..
Ko da ya shigo motar fuskar shi cike da annuri yace" Babynmu ba gaisuwa ba komai sai shigewa mota, to ni bari na gaidaki..."
Sai naji jikina yayi sanyi a hankali nace" ina kwana! ya aiki!.."
Murmushi yayi kana yace" lafiya kalau ya zaman waje daya?.."Shiru nayi ban sake kulashi ba, yatai magana nayi banza dashi, dan kan shi ya gaji yayi shiru, tun a lokacin fuskaci waceceni amma in yayi duba da labarinmu sai ga banda laifi duniyata koyar dani komai!! Ummana tayi farin cikin gani na sosai dan gata komai ta hada mana mu kawai take jira gashi mun b'ata lokaci, kadan naci domin na koshi shine ya zauna yaci da yawa sai kallon gidan nake cike da yanga...
A hankali na mik'e nace" a ina zan zaune ina so na huta?.."
Murmushi tayi kana tace" sai mun gama tukuna zaki tafi daki ki zauna ki jiramu!.."Na had'e fuska ina kallon gefe a hankali aliyu yace" Baby ni ko a wanne mataki kika tsaya a karatunki na addini?.."
Shiru nayi ina kare mai kallo a zuciyata nake tunanin sam bashi da zuciya, Ummana ta zungureni da kafarta ina kallonta tayi mun nuni da ido aka na bashi amsa, a yanzu muryata a nutse nace " nayi sauka tun ba yanzu ba!."

YOU ARE READING
YA ZANYI farin cikin yata shine burina
Short Storylabari ne me tab'a zuciya hadi da cakwakiya me zafi