Chapter 1

99 6 1
                                    

_YA ZANYI_
     _( FARIN CIKIN 'YATA SHINE BURINAH)_
 

*BY*.

_Husaeenah b. Abubakar_

_(MRS ABUBAKAR)_

_Alhamdulillahi, Masha Allah, HAPPY SALLAH jamaa Allah ya nuna mana shekarun gaba masu albarka, ina m'a kowa da kowa fatan alhairi Allah ya kara shirya mu bisa tafarki madai-daici,  ku kasance dani a koda yaushe MASOYYA na much love_

🔜

1⃣

Cikin sanyi murya me dad'in sauraro take rera kuka tamkar me busa sarewa, farace tas da ita kallo d'aya nayi mata na hangi zallar hutu a tare da ita, sosai take kuka 'in kayi la'akari da yanda fuskar ta ta kumbura, yayin da idanun ta sukayi jawur dasu, a hankali na matso kusa sosai ta yanda zan iya jin me take cewa...

"  Ka gafar ce ni mijina kafi kowa sanin ba dad'i ne yasa nake k'aunar rabuwa da kai ba, ina son 'yata ina mutu'kar k'aunar farin cikin y'ata dole ne nayi abinda take so ko dan ta kasance cikin farin ciki a ko da yaushe, bani da tamkar ta a cikin duniyar nan daga kaka  sai ita, dan ALLAH dan girman zattin  ALLAH kayi hak'uri ka sauwak'e min ko zan d'an samu nutsuwa a rayuwa ta?..."

Cikin k'unar zuciya yake duban ta, idanun sa sun kad'a sunyi jawur dan tsananin b'acin rai, yace" Sauddat!.." cikin wani yanayi na ban tausayi yayi maganar..

Sare taji shi amma sai ta nok'e tak'i dagowa su hada ido gudun kar tausayin sa ya hana zuciyar ta sakat, shi ma gwanine wajen iya sarafa zance ya sake gyara zama shin da kyau yana fuskantar ta...

Comments

And

Shared

D'iyar Abubakar ce jikar Abubakar  matar Abubakar, kuma uwa ga Abubakar...

YA ZANYI farin cikin yata shine burinaWhere stories live. Discover now