_YA ZANYI.?_
_FARIN CIKIN ƳATA SHI NE BURINA_By.
_Usaeenah b. Abubakar_
_(Mrs Abubakar)_Washe gari da sasafe naje gidan Hajiya a zaune na sameta khausar na cinyyarta tana wasa, sau daya KAWAI NA DUBI YARINYAR NA DAUKE KAI, CIKE DA JIN TSANARTA, A DADAFE NA GAIDATA ITAMA GANIN HALIN DA NAKE CIKI TA DAUKA KAKA TA SANAR MUN NE, NA SAKE GYARA ZAMANA INA DUBANTA A HANKALI NACE" HAJIYA WAYE ALIYUN NAN DA KIKE K'OK'ARIN HA'DASHI DA UMMANA? SHIN YA DANGANTAR MU DASHI?... "
MURMUSHI TAYI ME K'AYATARWA CIKE DA IZZARTA TACE" BA HURIMINKI BANE SANI WAYE ALIYU, ABINDA NAKE SO DAKE SHINE KI FADA UMMANKI TA AMINCE IN BA HAKA BA ZAN CIRE HANNU AKAN KU.."
TSIRA MATA IDO NAYI INA DUBANTA A HANKALI NACE" shikenan Allah yayi mata zab'i mafi alhairi a rayuwarta ba sai na gaya mata baki da baki ba, hajiya na amince har cikin zuciyata domin ina matuk'ar kaunar Ummana bazan so ta aikata kuskure mafi girma a rayuwarta ba, ni ma kaddaratace tazo mun a haka ba fatana kenan ba... na share wasu hawaye masu zafi da suka biyo kuncina a hankali nace" ina fatan zatayi farin ciki duk da ni ta dalilin uban y'ar nan kaddara ta fad'o mun, kuma bazan tab'a yafe mai ba har gaba da abada haka na tsaneki na tsaneki tsana mafi muni khausar!..." Na fada da karfi abinda ya hasala mata wani matsanancin firgici yarinayar ta saki wani irin kuka kamar ta san me nace...
Da sauri naga Ummana ta fito hankalinta a tashe ta amsheta sai rarashinta take, sai a lokacin ta kula dani a zaune da irin kukan da nake, jikin ta ya sakeyi bala'in sanyi a sanyaye tace" ke kuma lafiya?"..
Kasa magana nayi banda ruwan hawaye da nake sharcewa, Hajiya ta amshe zance da fad'in" ta amince akan maganar Aliyu sai banzan zanceta da baa rabata dashi, kije da yarinyar nan ciki ko zatayi shiru.. Ido kawai ummana ta zuba mun amma ba wai dan zuciyarta ta yarda da abinda nace ba, wucewa ciki tayi zuciyarta babu dadi..
Mikewa nayi Hajiya tace" ina kuma zaki? ai ba inda zakije sai kin gaya mun menene lefin wannan mitsitsiyar yarinuar da kika daurawa karan tsana? shin lokacin da abun ya faru kin san zaki same ta? fad'i kike kaddara kaddara to kaddara ta hanaki ki so yarki ne, duk duniya ba wanda ya kaiki a wajenta in baki kaunaceta yanzu ba yaushe zaki kaunace ta ko sai lokaci ya kure? Mun rarashiki iyakar iyawar mu Allah yaga zuciyarmu amma kink'i fahimta, Asiyya bazan sake miki magana akan khausar ba kiyi abinda kike so tunda ba wanda ya isa dake, amma karki manta akwai hakinta akanki ranar gobe kiyyama, a lokacin da komai ya riga ya kare babu wata hanya ko kofa da zaki iya neman yafiyarta, kamar yana kika sani itama amanace Allah ya baki kuma zaa tambayeki ranar gobe, bari na tuna miki kuskurenki na farko da kika tafkka kin cireta a nono a lokacin da bata san menene duniyar ba, kinyi jifa da ita sau babu iyaka duk akan wani banzan kudirinki, duk wani abu da kike gani yana faruwa tsakaninki da mahaifiyar har da hakin wannan baiwar Allahn da ike dauka, kinyi tsamanin Allah zai barki? tun wuri ki farka ki ja y'arki ajikinki in ba so kike itama tace kin cika son kanki ba!.."
Duk wani abu data fad'a sosai ya shigar mun zuciyata tabbas khausar bata da lefi amma meyasa zan sota? abinda bazan iyaba kenan, ina jinta a rainane kawai a matsayinta na yata amma tsakanina da ita ba wata sha'kuwa ko maganar soyayya, na mike a hankali kana nace" NA GODE Hajiya sai anjima..."
Ko hmm batace mun ba har na fice a gidan, ranar wuni nayi tunanin maganar da ta gaya mun, haka na kwana ina juyi...
An sake kwashe watanni ba daya ba biyu ba, kullum tsakanina da khaurar sai hantara gata da nacin tsiya duk yanda nayi mata hakan baya hanata ajima ta dawo inda nake, sabida na ringa ganin ko zuciyata zata sako, wuni take a gidanmu sai magariba ake mayar da ita, wayon ta sake fitowa yake ga b'arna kamar me ta sake fitar mun aka amma a zuciyata ina bala'in jinta a kwana biyu nan kawai in baa kawota ba naita fitowa falo ina dubawa kamar me neman wani abu, tabbas ina tsananin kaunar y'arta amma son zuciyata ya hanani gani burina dai shine Ummana ta soni ta kuma zauna dani bana fatan ta sake mun nisa...
Ba laifi yanzu SAUDDAT tana kula ALIYU har ma su dauki lokaci me tsaho suna hira, yana da mata daya yaran su shida kuma duk manya ne shima din babban mutune domin sa'an abbana ne, matar shi mutuniyar kirkice sosai dan ko neman auren da yake ta sani kuma bata nuna komai ba, fatan ta Allah ya hadata da ta gari...
ALIYU mutumin kirkine bashi da damuwa ko kadai yana da mutunci dai-dai nashi, sam bashi da matsala musamma ta fanni gidan sa ko kula da iyali, duk sanda yazo wajen sauddat sai ya tambayeta Asiyya kuma cikin jin dadi zata amsa shi, amma basu taba haduwa ba, ya sha tambayarta yaushe zata hadasu su gaisa sai tace ba yanzu ba...
baayi auren Aliyu da sauddata ba sai da khausar ta cika shekara uku a lokacin ba inda bata zuwa ga wayo da iya surutu, a yanzu ina zama kusa da ita amma bana daukarta sosai ta taso da wani irin tsorona in ina waje gaba daya bata sakewa komai cikin d'arid'ari takeyin sa..
Yau ta kamata jumma'a ranar me mahimmaci a rayuwar mu baki daya, a yau aka daura auren Sauddat da Aliyu ba laifi anayi taro sosai y'an wajen aikinta ma sun mata kara kware wannan auren kam ta yarda kowa naso ba wanda yake kunci a cikin jamaar ta sai ni da aka cika da tambayar khausar yarinyar waye? domin kamar da take dani har ta b'aci sai dai nayi dariya kawai ko nace ta wace cikin wasa, zuciyata kam radad'i take mun amma na daure nak'i nunawa ko a fuska, a cikin taron ne aka samu wani hatsabibin munafikin ya fad'awa wata Khausar 'yatace garin yawon banza na sameta, a hankali ake maganar tun bata fito gaba daya ba har ta fito fili kowa yaji, tun abu yana iyaka cikin gida har ya fita waje magana ta kade gari a cikin abinda baifi awa hud'u ba, wanda basu taba shigowa cikin gidamu ba a ranar sai dai suka shigo suma dan gulmace ta kawo su, labari har ainahin gidamu gaba daya unguwa ta sani wa yanda suka san gaskiyar zance sune kadai suka san ba haka abun yake ba, a hankali gaskiya tai ta fitowa itama masu yarda nayi masu karyatawa nayi, Na shiga tashin hankali marar musaltuwa ban taba tunanin haka zata faru ba shikenan yanzu an samu wanda ya bata mun gobe na, fitar ma sai ta gagareni kwana nayi ina kuka khausar kuwa tuni ta koma gidan mamanta, Sauddat a ranar bata tare ba itama tana nan bakin kofa a zaune tana aikin kuka da tunanin halin da nake ciki domin tuni na kulle kofar...
Bayan kwana biyu Sauddat ta siyar da gidan mu a wata sabuwar anguwa ta manya masu kudi ta siya mana wani dank'areren gida, ba wai dan ranta naao ba sai dai kawai na kasance a cikin farin ciki, a yanzu zuciyata ta jima da bushewa bana jin rarashi kullum tunanina ta ina zan nemo shi?..
Kamar yanda ta bukaci lokacin tarewar ta ya cika ta tare a saban gida daga ita sai khausar domin ni juyin duniya tayi dani nak'i binta ganin ta matsa mun ne ma yasa nace zanzo amma ba yanzu ba, ni kam yanzu dole na janye jikina da gidan umma na domin bana so abinda ya faru a baya ya sake faruwa, mazajen ta sam bana saa wanda zai daukeni a matsayin y'ar cikin sa...
Cikin kwanciyar hakali da lumana suke kullum cikin farantawa juna, bashi da burin da ya wuce ya ga ya sanya Sauddat cikin farin ciki kamar yanda ya san maradin zuciyarta Baby, insha Allah baby zata dawo kusa da ita...
Khausar taki zama dole aka dawo da ita gida, sam ban san da zance dawowar ta ba ina zaune a dakina nayi nisa cikin zurfin tunani naji an shak'oni ta baya irin ruk'on manya, na tsorace sosai a gigice na juyo cike da tsananin matsifa hannu na a sama ina shirin gabzawa koma waye mari, cak na tsaya idanuna a waje tsoro mamaki firgici duk ya rufeni a lokaci gud'....
To my fan's mu hadu a pagen gaba in mu duka ya kaimu, dan Allah a cigaba da hakuri dani insha Allah zan dawo yanda nake dah....

YOU ARE READING
YA ZANYI farin cikin yata shine burina
Short Storylabari ne me tab'a zuciya hadi da cakwakiya me zafi