Chapter 12

9 0 0
                                    

_YA ZANYI.?_
_FARIN CIKIN ƳATA SHI NE BURINA_

By.

_Usaeenah b. Abubakar_
_(Mrs Abubakar)_

🅿1️⃣2️⃣


Fitowa ta kenan d'aga dakina, ina buda wayar hannu na, kawai jina nayi a jikin  mutun ya rungume ni tsalama har yana  rabani da kasa, cikin gigita da tsoro na kai mishi naushi da gwiwar hannu na, ba shiri ya sakeni na fad'i kasa a matuk'ar fuskace nake duban shi idanuna har ruwa suka kawo dan zallah masifa, na bude baki zanyi magana kenan sai ga Umma tazo...

" Sabahallah Baby me kike a k'asa kuma? salan mura ta kamaki ko?..." da sauri ta dago ni..

shima cikin sauri yace" zuwa na kenan ina shirin magana kika rigani, Baby bakya gudun sanyi ko?..."

Waro mai idanuna nayi cike da tsantsar tsanar sa, gaba d'aya haushin su ne ya cika min zuciya, cikin sauri na wuce abu na zuciyata a dagule...

Rungumo Sauddat yayi ta baya, ganin tana niyar bina, a k'asance yace" madam ina san magana dake please..."

Murmushi tayi kana tace" ina sauraronka!..."

" Mu shiga daki to!.."

Da sauri ta dube hanyar dakina cikin kankanta ido tace" please ina so  na sake ganin Baby minti biyu kawai ya isa!..."

" No Sauddat bazan iya jurewa ba in kika gama dani kya je!.."  ba dan ranta yaso ba haka ta bishi ciki..

Ni kam yanzu har Umma haushin ta nake ji, musamma dana bata biyo bayana ba, a yanzu kuka baida amfani a wajena dan haka na cigaba da sha'anin gaba na, amma abinda yayi min ya tsaya min a zuciya...

Babban tashin hankalin da nake fuskata yanzu sai dare ya raba,  yau ma ban jima da kwanciya ba aka haske min fuska da fitila me hasken gaske, zuciyata ta dako da k'arfi amma sai na daure tamkar ina barci haka nayi, duff kuma aka kashe haske zuwa can naji ana jaye min bargo cikin sauri na damk'e shi da hannuna warware murya nayi na kwallawa Umma kira a matuk'ar firgice!..."


Da gudu suka shigo d'akin nawa, ko wanne hankalin sa a tashe kai tsaya inda nake a zaune idona a rufe ina kwala mata kira ta nufo, cikin rawar jiki ta rungumo ni jikin ta hadi da cewa" Baby!! Baby!! menene!??..."" gaba d'aya ta raude...

Salisu ne ya kunna hasken d'akin game da zama kusa damu shima, cike da jimami...

Kankame ta nayi cikin azabar tsoro nace" wani ne! wani ne!..." nama kasa maganar gaba d'aya a tsorace nake...

" Me yayi miki?.." ta tambaya a hargitsi..

Mikewa yayi cike da jin barci yace" Sauddat tunda ba abin da ya faru zo mu wuce barci nake ji!.."

Wani irin kallo ta aika mai akaro na farko kenan da ta fara mayar mai da magana cikin fushi, " kaje kawai ni zan kwanta da y'ata! domin bazan iya tsallake wa na barta ba..."

" Okay sai da safe nima bazan iya jin wanna shirman ba!..."

Da ido kawai ta rakashi...

Tashi tayi ta leka ko ina na d'akin babu kowa ciki, dan haka ta koma falo ba inda bata duba amma bataga kowa ba kuma kofar su a rufe take yanda ta rufe ta tun 8 na dare, to ko dai mafarkin da take ne ya gigita ?...

A zaune ta same ni sai kalle-kalle nake, rufe kofar tayi har da kye sannan mukayi addu'a...

Washe gari tun kafin mu tashi salisu har ya shirya, a zaune muka same shi matar shice kad'ai ta gaida shi amma banda ni da nake aika mai harara, cikin halin ko in kula yace" Sauddat ni zan wuce sai kuma Allah yayi min dawowa, ko nace sai mun had'u a wajen aiki Dan Allah banda makara domin na ga yanzu hankalin ki gaba d'aya ya koma kan shirme!..

Murmushi tayi kana tace" ni kam bana ganin shirme a kulawar da nake bawa y'ata, da kai ka haifeta bazaka ce haka!.."

Ganin taji haushi ne  yasa ya zagayo inda nake a zaune, ban ankara ba sai ji nayi mutun ya manna min kissing a kumatu, had'in da gayeni da hannu shi wai zai min bye-bye, cikin sauri na zulli zuwa kasa cikin fushi nace" bana son kaji! karka kuma tabani ko da wasa! ko ubana kafin ya mutun baya min wanna muguwar aladar bare kuma kai zuwan yau!..."

😒😒

" Nima Ubanki ne Baby, a y'a na daukeki kuma ni wannan ce aladata, bye-bye Maman mu!..."

Cak na tsaya ina kallon shi raina a bace, kalla Umma bata ce min ba har ya tafi, to abinda na fahimta shine muddin salisu yana gidan mu to kullum sai an shigo min dakina, musamma cikin dare a yanzu hata Umma ta fahimci sai salisu yana nan, nake mata ihun neman taimako, to yanzu bata kwana dani sai dai tazo ta dubani tabi mijinta su barni ni kadai...

Gaba d'aya yanzu bana barcin dare kullum kwana zaune nake, zuciya cikeda fargaba kuma ba fashi kullum sai an shigo min sai dai in baya gidan, gaba daya na gama sakawa a raina mijin Ummata ke bibita, ciki wata uku na dawo abar tausayi, gashi Umma ta hanani zuwa ko ina, kullum cikin fargaba nake kwanciya ni da gidan ubana amma zama a cikin sa ya zamemin masifa...

YA ZANYI farin cikin yata shine burinaWhere stories live. Discover now