Chapter 15

13 1 0
                                    

_YA ZANYI.?_
_FARIN CIKIN ƳATA SHI NE BURINA_

By.

_Usaeenah b. Abubakar_
_(Mrs Abubakar)_

🅿1️⃣5️⃣

Nayi saurin riƙe hannun ta ina hawaye haɗi da girgiza mata kaina alamar bana so, murya ta na rawa nace" *ita din uwata ce* tana da ikon aikata komai akai na, nayi imani da ALLAH dah ta san abinda zai faru dani ba inda zata tafi ta barni, dan ALLAH Kaka karki shiga tsakanin ƴa da uwa ina ƙaunar Ummata sosai duk da haka!..."

Jikin ta ne yayi sanyi cikin sauri ta fice a ɗakin baki ɗaya, na kalle gefe ina goge hawayen fuskata,  tausayin kaina da rayuwata na ratsani...

Gefe na ta zauna shiru babu magana sai da tayi kukan ta me isar ta, sannan ta kamo hannu na cikin wani irin rawar jiki tace" Baby na!! tabbas sai yanzu na san na tafka  babban kuskure a rayuwata ji nake gaba ɗaya na tsani kaina, tabbas na cutar dake cuta mafi muni cutar da san har abada bazaki bar tuno ta ba, ban cancanci yafi a gareki ba domin nice silar komai da ya faru dake,  nayiwa mahaifinki alƙawarin kula dake amma kash!! son zuciya da soyayya marar tushe yasa na kasa gane barnar da nake aikatawa, ASIYYA!! ta kira sunan cikin muryar kuka ɗaga rana irin ta yau na yarje miki ki zaɓi duk inda kike buƙatar rayuwa tsakanin gida uku, ba zan sake takura miki ba alkawari nayi wa kaina, ko da dukiya ta zata ƙare sai na bi miki kaɗin ki, fatana ki yafewa wannan wawuyar uwar taki!..."

Cikin sauri na rufe mata bakin ta ina hawaye nace" * sam ba lefinki bane karki manta kaddarar rayuwata ce tazo a haka, kuma na amshi kaddarata da hannu bibiyu, ko kusa ko alama bana ganin lefinki Ummana kuma har yanzu soyayyarki bata girgiza ba ko kaɗan a zuciyata, ke din uwace ta gari kuma ina matuƙar alfhari dake, abinda bazai goge min ba a rayuwata  shine mijinki Umma!...''

Na mayar da kaina na kwanta zuciyata nayi min ƙ'una hawaye masu matuƙar zafi na bin kuncina...

Tun d'aga lokacin Umma na ta cigaba da jinyata inda tsakanin ta da Kaka sai dai kallo domin ta ɗauki zafi sosai, a wajen Hajiya kawai take jin sauki...

Alahmdulillah sati na biyu aka sallamo ni lokacin Umma taje gida ɗauko kaya, Kaka ce kawai a wajena bata tsaya zaman jiranta ba, ta ɗ'auke ni sai gidan ta ita ta cigaba da kula dani da bani duk abinda nake so, sosai take jin tausayi na wani lokaci har hawaye take ganin yanda na sauya cikin ƙanƙanin lokaci, magana in bata zama dole ba bayin ta nake ba...

Ban san me ya hana Umma zuwa ba, domin tunda aka sallamoni ban ganta ba, ashe Kaka ce ta ja mata dogon layin...

Suka sakani a gaba da gata ko wace tana ƙoƙari ganin nayi farin ciki, abinda basu sani ba ni a yanzu nayi sallama da farin ciki a rayuwa ta, tunda bani da wata kimma ko martaba, ina ganin kaina dai-dai nake da macen da bata da daraja a idanun duniya...

Wata irin ƙiba nayi ta fitar hankali ga kyau da haske dana kara, sam bana ƙaunar cin wani abu ko da yaushe ina kwance a kasa domin yanzu sanyi nake buƙata sosai...

Kaka dadi take ji ganin yanda na dawo a tunaninta zallar nutsuwa ce da na samu yanzu, Hajiya ma in tazo sai taƙi tafiya sai dare ta sakani a gaba da surutu duk da ba komai nake amsa mata ba,  ga wani irin kallon ƙurulla yanzu da ta koyo wani lokaci har luluɓa nake in na ganta, haka ba shi zai sa ta fasa kallo na ba...

Wata na uku kenan bana ganin Umma, kuma itama bata zo ba gashi nayi nauyin baki nima ban tambaya ba, ko wayata bana tunanin ɗauka bare  na ƙunna ta, kullum ƙwana duniya bani da tunanin da ya wuce yaushe zan mutu! gaba ɗaya bana jin daɗin rayuwar, a zuciyata ciwo nake da yawan tunanin, amma a zahiri jikina baya nunawa ko kaɗan kullum kara cika nake ta ko ina...

Sauddat na komawa gida ta maka Alhaji salisu a kotu, bai san wainar da ake toyawa ba sai da akazo tafiya dashi, sosai ya girgiza da jin batun da ake zargin shi dashi,  shima lauya ya ɗauka in da suka shiga kotu gadan-gadan...

YA ZANYI farin cikin yata shine burinaOù les histoires vivent. Découvrez maintenant