_YA ZANYI_
_(FARIN CIKIN Y'ATA SHINE BURINA)_BY.
_HUSAEENA B. ABUBAKAR_
*(MRS ABUBAKAR)*
💫 *DA BAZAR MU WRITER'S ASSOCIATION* 💫
*We _are here to make you happy, smile, educate and to realized that we are the best among all...DA BAZAR MU MUKE TUN'KAHO.*
🅿3⃣
Da sauri ta wuce Hajiya a falo d'akin da yake mallakin ta ta shige, a bakin kofa ta zube numfashi ta na fita da kyar, kukan ta na tsananta a haka dattijuwar ta same ta fuskar ta cike da alhaini, a b'angare guda kuma soyayyar jikar ta ya gama kashe mata zuciya, cikin sanyin murya tace" ASIYA!!!..
" Dan Allah ki rabu dani! bana son kowa ya rabe ni a halin da nake ciki a yanzu, ku rabu dani in yaso bakin cikin ta ya kashe ni kad'ai!..." Cike da hargowa tayi maganar a zafefe kuma ta ida shigewa d'akin had'i da banko kofar...
Cikin tsananin tausayawa take duban kofar tamkar tana wajen a tsaye, a sanyaye tace" Allah ya shiriyeki Allah ya saka miki, Allah ya baki ikon jurewa!.."
K'aramar yarinyar dake bayan ta wace bazata wuce shekara uku ba tace" ameen Hajiya!..."
Da sauri ta dago tana duban ta cikin hikima tace" yarinyar momy yaushe kika shigo?..."
Murmushi tayi cike da yarinta tace" yanjun nan, naga ANTY aniya zata shigo shine na biyo ta!..."
Hannun ta kama tana murmushi suka bar wajen!...
Lumshe idanun ta tayi zuciyar ta na lafawa a hankali jin murya dake kawo mata nutsuwa a duk lokacin da take cikin damuwa, cikin salbin harshe tace" ki gafarce ni Umma! zan so kema ki soni kamar yanda nake ji a yanzu, ina kaunar farin cikin ki ko da ko zan rasa rayuwa tane...
" Hajiya me yasa ANTY aniya take kuka??.."
Da sauri ta dube ta domin batayi tsamanin yarinyar karama irin kausar zata iya zaro zance haka ba, ta d'aure cikin wayo tace" bigewa tayi da kofar mota shine take kuka!.."
Shiru tayi kamar me tunani can kuma tace" to me yasa wani lokaci take duka na? jiya cewa tayi zata kasheni in na sake zuwa inda take!..." A yanzu cikin tsoro da zubar hawaye tayi maganar..
Zaro ido Hajiya tayi cike da kadawar ciki tace" kul na sake jin irin wannan zance a bakin ki!.."
Kuka Kausar ta saki tamkar jira take, Hajiya ta gigice domin ta san wani saban bala'in ne zata kuno...
Da wani mugun sauri ta hantsilo d'aga bed din tamkar ana turata da iska haka ta iso falon idanu nan jawur dashi, cikin sauri Hajiya ta boye Kausar a bayan ta tana fad'in" ya akayi ASIYA?..."
Bata amsa mata ba ila lik'a bayan ta da tayi hadi da cewa" *me ya same ta Hajiya!..."*
A karo na farko kenan a rayuwar da ta tab'a tambayar lafiyar Kausar! Tsananin mamaki ya hana ta magana sai binta da kallo take, a hankali ta d'ago Kausar gaba d'aya zuwa jikin ta, tana fad'i " me akayi miki?" wanda yake tare da ita ne a koda yaushe kawai zai fahimci a tsawace tayi maganar..
Cikin sauri Hajiya ta amshe Kausar tana fad'i " kin gama tsoratar da yarinyar mutanen kuma ina tambayar me akayi mata, kullum Ina fad'a miki yara irin su Kausar baa gaya musu irin kalaman ki, gashi nan yanzu har ta iya fad'ar kin ce zaki kashe ta in ta sake zuwa jikin ki!..."
" *Sorry Baby bazan sake ba*..."
Kausar ta miki-miki da ido sabida tsoron ASIYA kukan ma tun fitowar ta ya dauke, tamkar ta rungume dutse haka Kausar ta zama a jikin ta...
Hajiya ta saki murmushi a zahiri zuciyar ta na sake tsunduma cikin matsanancin farin ciki, da sauri ta bar musu falo hadi da kiran Sauddat a waya...
Wacece Sauddat?
Wacece Kausar?
Shared
Comments
Dinku shine BURINA
Ku ci gaba da k'asance wa dani domin jin yanda zata kaya!
Nice Taku har kullum MRS ABUBAKAR
YOU ARE READING
YA ZANYI farin cikin yata shine burina
Short Storylabari ne me tab'a zuciya hadi da cakwakiya me zafi