_YA ZANYI.?_
_FARIN CIKIN ƳATA SHI NE BURINA_By.
_Usaeenah b. Abubakar_
_(Mrs Abubakar)_🅿1️⃣7️⃣
Hak'ik'a uwa uwace duk yanda take kuwa, haka kawai yau na tashi ina bala'in son ganin ta, ji nake a jikina tamkar ban kyauta mata ba, numfasawa nayi lokacin da doctor yake shirin fita a hankali nace" ina san ganin a'halina doctor!... "
Murmushi yayi kana yacc " nima yau nake shirin baku sallama, fatana kiyi aikin da abinda nace miki ki zama cikakiya me yarda da k'addara, insha Allah wata rana zakiyi farin ciki!..." daga haka ya fice a dakin da sauri...
Shiru nayi ina jin wani iri a raina, na rasa tunanin me zanyi ina cikin wannan halin ne Umma ta shigo dakin, cike da kewata hawaye na bin kuncin ta, duk yanda nakai da zuciyata wajen daurewa kasawa nayi, nima kuka na saka mata a haka su hajiya suka same mu ....
Bayan wata guda a yanzu gata ba irin wanda bana suma a wajen iyaye na, kowa burin shi bai wuce ya ganni a cikin farin ciki ba wanna dalilin ya saka na zama cikakiyar yar gata, basa bari na na zauna ni kad'ai dole Sauddat ta dawo zama tare dani ko barci tare mukayi bata runtswa har sai ta tabbatar nayi barci kana zata kwanta, hata motsi in nayi sai ta tambaya lafiya, cikina yana sake fitowa amma ba sosai ba in ba'ace maka cikine dani ba, zaka dauka tumbi ne na sake murjewa jikina yayi wani luku'i-luku'i, ga wani uban haske da na kara kullum sake kumburewa nake, nayi wata mahaukaciyar kiba...
Shiru nayi tunanin rayuwata ta baya, a haka Umma ta same ni cike da tausayi na tace'" Baby zaman me kike ke kad'ai a nan?.."
Ajiyar zuciya na sauke cike da jarimta nace" ina tunanin ya zanyi ne kawai Umma!.."
" Game da me fa!.."
" Ji nake a raina dama abinda ke cikina yazo a mace, domin Ina tunanin yanda zai k'asance cikin bakin ciki in yaji asalin labarin shi, Umma har cikin zuciyata nake jin tsanar abinda nake d'auke dashi ba dan komai ba sai dan ko uban shi ban sani ba har yanzu!..."
Wata irin faduwar gaba ne ya kama Sauddat cike da jureya tace'" kul na sake jin irin wanna kalaman suna fitowa a bakin ki, kin san yanda d'a yake a zuciyar uwa kuwa? In baki so abinda ke cikinko yanzu ba yaushe zaki so shi? me yasa kike son daura mai lefin da baiji bai ganin ba? shin bakya so kema naki yayi alfhari dake? Ni na san karya kike Asiya kice baki son abinda ke cikin ki, domin d'a ya wuce wasa a duniya! tun wuri ma ki farka in mafarki kike, kamar yanda kika rungume kaddara to ki tallafi abinda ke cikinki da dukkanin k'arfin ki ta yiyu ta hanyar shi zaki samu farin ciki me daurewa, zaki iya fad'a min yanda kikeji inda yana miki motsi?..."
Ta kafe ni da idanun cike da tamke fuska..
A hankali na daura hannuna bisa cikin aiko tamkar yana jira sai wani irin motsi yake, cikin sauri na janye hannu na kwalla na taruwa a fatar idanuna, muryata na rawa nace" wallahi Umma tsoro nake ji, har ya ban fara jin shi a cikin raina ba!..."
Zama tayi kusa dani cike da tausayi na, cikin rarashi tace'" matso jikina Baby!.."
Ba musu na shige jikinta ina daura kaina bisa cinyar ta, haka kawai naji wani irin sanyi a raina, shafa kaina tayi cike da kauna ta tace'" kin san yanda na tsinci kai a lokacin da na tabbatar ina d'auke da cikinki baby? nayi farin ciki marar musaltuwa, na lalab'aki tamkar egg bana wani abu a da na san zai cutar dake, me yasa ke bakayin haka? shifa d'a wata ni'imace da Allah yake bawa bayin sa, zan so abinda zaki haifa kifi kowa k'aunar shi, ki bashi kulawa fiye da yanda zamu bashi, da zakiyi haka zanyi matuk'ar alfhari dake a matsayin y'ata nima!.."
Murmushi nayi domin har ga Allah yanzu na fara jin wani abu daban wanda na gaza fahimtar shi, a hankali na sake gyara kwanciyata alamar hirar tanayi min dadi, itama ganin haka yasa ta sake dagewa wajen jan hankali na akan cikin...

YOU ARE READING
YA ZANYI farin cikin yata shine burina
Short Storylabari ne me tab'a zuciya hadi da cakwakiya me zafi