Chapter 30

7 2 0
                                    

_YA ZANYI.?_
_FARIN CIKIN ƳATA SHI NE BURINA_

By.

_Usaeenah b. Abubakar_
_(Mrs Abubakar)_



A zaune na same su ko wace fuskarta cike da annashewa,  nima sakin fuskata nayi ina musu murmushi kayan na saki a gun nayi wajensu,  fad'i nace" nayi missing din ku tsofafi!.."

A tare suka mun dariya Hajiya tace" kaga y'ar amarya sa yau gaba daya kin manta damu,..."

Nima dariya nayi ina zama kusa dasu,  na sake ware idanuna da kyau ta inda zan hango y'ata,  " da fatan na same ku lafiya?.." Na tambaya idanuna a kofar dakin hajiya da naji motsi...

Da idanu suke gulmata ni ban saniba a tare sukace lafiya kalau ya Sauddat din?

" tana gaishe ku gaba daya,  tace itama tana nan zuwa kwanan,  Hajiya ina!!... sai nayi sauriyin shiru gudun kar nayi abun kunya..

"Ina me?.." Ta tambayeni idanunta akaina...
" aa shikenan bari na shiga ciki zafi!.." na fada cike dabara..

Da kallo suka bini har na shige,  ba dakina na nufa kai tsaye dakin Hajiya na shiga wayam ba kowa,  na fito na koma nawa nan ma banga kowa ba ajiyar zuciya na sauke a hankali nace" ina kuma ta shiga ne?.." kayan da na siyo mata na dauko ina dubawa lumshe idanuna nayi tuno yanda siyayyar ta kasance mun a yau da kuma saban alamarin da yaso faruwa dani!...

Fitowa na sakeyi ina yak'e nace" Hajiya gashi inji Umma tace a bawa yarinyar nan!.." Na fada ina mikewa hajiya kayan,  amsa tayi tana dubawa...
Ta dubeni kafin tace" gaskiya Umma nan naji da khausar irin wannan kaya haka! yanzu ita yaushe ta fara fita har tayo siyayya irin haka? sunyi kyau sosai ta gode!.. ta fada cike da jin dadi..

Shiru nayi ina jiran takirata a gwada mata amma shiru taki ko motsi a inda take,  na muskuta nace" Hajiya to ai baa gwada mata mun ganiba da kika dage kina yabanta!.."

Saurin me kike zata saka ai ba anan zaki zauna ba?.."

" eh" " to kuma ke dai bamu lokaci"

Nafi awa biyu a zaune banji dauriyar Khausar ba gajiya nayi na mike,  zuciyata duk babu dadi nace" Hajiya ni zan tafi gida!!/" cikin rauni nayi maganar domin har ga Allah in na sake jimawa a wajen kuka zan saki..

Da mamaki a fuskarta tace"  wanne gida kuma?..

K'in kulata nayi na wuce ciki abuna,  ban jima da shiga taga na fito da kayana ina tura baki gaba,  ta mike tana tahowa ina tahowa a tsakiya muke had'u sai nayi saurin kawar da kaina gefe domin kwallace kwance a cikin su,  itama ganin haka yasa ta bani hanya na wuce da kyar na daure zuciyata na tafi gidan Kaka,  itama ganin fuskata babu walwala bata wani shige mun ba ta ban waje na shge dakina,  ina zama akan kujerar na saki wani marayan kuka me cin rai,  a hankali nace" mutun da d'an sa a nuna mai iko da k'afafa.."  sai dai nayi me isata sannan nayi shiru...

Kwana biyu ban sakata a idanuna ba,  karshe har kofar get din nake zuwa na zauna na raba kafa ina get din Kaka ina hange na Hajiya,  abun mamaki sam ban ganta ba bana ganin shigar kowa sai ta me aikinta...

  Satina guda duk na gundira da zaman ga haushin su da naji kamar na shak'e su,  duk da ban furta musu abinda nazoyi ba amma ai sun san 'yatace dole zan so ganinta...

Kayana na kwashe tass yau zan koma gida dan babu amfanin zaman!!.."

Ba wace nayi wa sallama a cikin su na fice daga gida raina duk babu fad'i nake" sai ku kwad'ata ku cinye tunda kuka haifa mun ita!.."  Ummana tayi mamakin ganina lokacin da na koma,  sanin halina yasa bata tambaya ba sai sannu da zuwa kawai da tace mun,  wanna abun da akayi mun ya tab'a mun raina sosai na shiga damuwa da tunane tunane kala-kala,  wata zuciyar tana gaya mun ko ta mutune wata nacewa dah ta mutu bazata amshi kayan ba,  na sake sakin tsaki akaro na babu adadi to ina suka kai mun y'ata?.."

Kwana biyu walwata ta ragu gashi Sauddat ta koma bakin aikinta, sai gidan yayi min girma ni kad'ai kal a ciki, na shirya tsaf ban gayawa kowa ba na taho gidan hajiya lokacin suna zaune suna hira sai ganina sukayi akan su,  basu nuna mun mamakin su ba ila washe baki da sukayi suna mun dariya da sannu da zuwa,  hajiya tace" in zaki tafi dai kina mana sallama ba ki barmu da tararabi ba...
Lokacin yamma tayi sosai,  da gudu ta shigo falon tana dariya sanye take cikin kayan makaranta tayi kyau sosai a ciki,  bayanta dauke da jakarta cike da shagwaba ta haye bayan Hajiya tana fadi" oyoyo Mamana!.." Da yake haka take kiranta dashi..

Abun gwanin ban shaawa itama Hajiya oyoyon tayi mata kafin ta juyo da ita gabanta tana tambayar ta hanya,  cike da shauk'i da maganarta wace bata fita sosai ta hau bata labarin karatun da tayi,  hajiya tace baki ga anty asiya bane? sai a lokacin ta dago kallo daya tayi mun tayi saurin boya a bayan hajiya murya a shake tace" ki boyeni zata yankani!.."

Galala na baki ina kallonta,  hajiya tayi dariya tace" ba abinda zatayi miki zo ki gaidata kinji!.." Cikin rarashi ta fada tana mai fito da ita,  jikinta a sanyaye kamar an mata dole tace" inina nana!"..

Gaba daya jikina yai mugun sanyi kasa amsawa nayi har sai da hajiya ta tabo ni,  na sake narke fuskata tamkar zan fashe da kuka nace" Khausar!!.." sai kuma nayi shiru jin kuka na neman kwace mun..

Ita dai ido take bina dashi, a mugun tsorace take dani...

Hajiya kina ji fa!.." Na fada cikin hardewar harshe..
Hannu khausar ta kama tana kwalawa me aikin su kira baa jima ba sai gata ta fito da saurinta,  umarni ta bayar akan a shiryata sanna ta dubeni bayan wucewar su tace" me zance ni yanzu? ko kin manta yanda mukayi dake akan maganar Khausar karki sake sakani a ciki kiyi abinda yafi miki!.."

" Hajiya ki fahimceni tabbas na san nayi wauta amma yanzu ina bukatar y'arta! ta ya zan gyara kuskurena?.."

" ta yanda kika tafka.."

Hawaye na na share a hankali nace to zanyi kokari..."

YA ZANYI farin cikin yata shine burinaWhere stories live. Discover now