_YA ZANYI.?_
_FARIN CIKIN ƳATA SHI NE BURINA_By.
_Usaeenah b. Abubakar_
_(Mrs Abubakar)_Karshe
🅿40
Me d'a wawa ne, a hankali nima na fara magantuwa, sannu-sannu wata fitinaniyar shakuwa ta shiga tsakani mu ya zaman ko a wajen aiki muna tare, hirar tamu bata wuce ta khausar da abinda ya shafi rayuwarta ba..
Zaune yake a gabanta cikin biyayya da jin nauyinta yake wasa da yatsar kan shi a kasa, yayin da nikuma nake gefe a zaune Khausar na makaranta lokacin, a nutse Umma ta amsa gaisuwar shi cike da kamala na manya mata, tace" baby! zaki iya tafiya?.."
"Eh" nace ina mikewa dan barin wajen..
Gyara zaman ta tayi da kyau a hankali cikin sanyin murya da kwarewa wajen sarrafa harshe tace" Fauwas ko? ina so ka bani hankalin ka nan a matsayina na mahaifiya ina so da bakin ka kayi mun bayanin dalilin son auren baby dan Allah ba dan na isa ba kar kayi mun karya, ka fad'a mun iyakar gaskiyar ka domin jikina yana bani tabbas akwai wata a kasa! sannan bincike da nayi akan ka yana kokarin tabbatar min da abinda nake zargi, amma meye gaskiyar lamari?.."
Fad'uwar gabace ta kama shi, cike da diriricewa yace" Umma! ni dai na farko kaunace ta kawo ni wajen Asiya, da kuma neman yafiyar laifin da na aika cikin rashin sani, a gefe d'aya kuma ina so na share zancen b'ata sunan khausar dake a gari akan asalinta, Umma! na san kinyi bincike a kaina ba tun yanzu ba mahaifiyata da kanta tayi miki bayani koni waye, Umma! a yanzu bani da wata saurarn dabara dan girman Allah dan soyayyarki da fiyayyen halitta ki rufa mun asiri kamar yanda Allah ya rufa miki, kar na rasa Asiya da y'ata a yanzu wallahi in hakan ta faru mutuwa zanyi, ina so na goge laifina ta wannan hanyar ina so ni da kaina nayi mata bayanin ni waye amma sai bayan aure, dan na san yanzu in ta sani bazata tab'a amincewa dani ba, alfharma nake nema a gareki Umma! ke uwace kin san abinda y'ay'a sukeji dan Allah dan AN'NABI ku yafe mun bakin cikin da na cusa muku a rashin sani?.." Cikin karayar zuciya da rawar murya yayi maganar...
Wani irin nauyi zuciyar Umma ta sake ji, nisawa tayi kafin tace" Fauwas kayi hakuri bazanyi abinda zan dawo ina da na sani ba, Ya zanyi farin cikin yata shine burina wallahi, dole ne ta sani dole ne na gaya mata sai ta amince da kanta kafin na yarda ta aureka in kuma ba rabonka bace sai nace Allah ya barka da Saranka, dadi daya dana ji cikin sauki Allah ya amsa addu'ar mu ya saka mata cikin gagawa kaima a cikin iyalinka yar uwarka kuma matarka a yanzu ta sanadin abinda ka aikata itama yanzu tana rike da diyar da baa san waye ubanta ba, ko yanzu Alhamdulillahi Allah maji rokon bayinsa, Fauwas ba wai korarka nake ba dan Allah tun yanzu ina neman alfharma ka fita a rayuwar y'ata wallahi bana so na ganta cikin damuwa wallahi azeem a yanzu farin cikin ta kawai nake nema!..."
Zan iya durkusa maka inda hakan zai sa ka rabu da ita! Ta fad'a tana zamowa daka kan kurejar da nufi durkusawa, cikin Sauri na dagota da dukanin karfi na zuciyata na raurauwa, kirjina na bugawa da karfi bala'in cikin danne son kuka nace" Bazan tab'a yafewa kaina ba in nagaki a kasan wanda ya cutar mun da duniyata ya hanani farin ciki na shekaru da dama, ya kuntata mun fiyye da zaton me zato, ya ha'ince ni ya sa mutanan gari sunayi mun mumman furuci, amma akarshe ki roke shi akan abinda shi bai isa ya samu ba, Haba Umma na! sabida farin cikina kawai sai ki kaskantar da kanki? ba sai kinyi haka ba ni da kaina zan kore shi kuma dole ya tafi...
Kallona take fuskarta cike da hawaye, nima hawayen nake a yanzu..
Kallon shi nayi da idanun na da sukayi jazur " mugu azalima maha'inci me yaudari, annamimi, shin ka manta irin rokan da nayi maka a lokacin da kake kokarin keta mun had'i? ka manta yanda ka d'aureni tamakar akuya a lokacin da bani da wata dabara ? shin ka manta irin hawayen na dake fitarwa da tsananin azaba da rud'ani? shin ka manta halin da ka tafi ka barni a lokacin da ka gama wulakanta mun rayuwa? shin ka manta lokacin da ka barni kwance cikin jini halin ko na rayu ko na mutu? me kuma kake nema yanzu a waye me yayi saura? y'ar da kake ikirarin akan ta kace shin ka san cinta bare shanta? ka san wahakar da na sha akan y'ata? wallahi azeem Fauwass ka cutar dani kuma na barka da Allah domin kadan ma ka gani wallahi cikin sakaiyyar da Allah zai mun akan hakina, ka tashi ka fice mana a gida tun da ba da kudinka aka had'a wajen siye ba!..."
YOU ARE READING
YA ZANYI farin cikin yata shine burina
Short Storylabari ne me tab'a zuciya hadi da cakwakiya me zafi