Chapter 31

5 1 0
                                    

_YA ZANYI.?_
_FARIN CIKIN Y'ATA SHINE BURINA_

BY.

_USAEEENAH B. ABUBAKAR_
(Mrs abubakar)



" Da yafi miki kam,  ta fad'a tana kashingid'a akan kushin din,  da idanu nake binta a hankali kuma ina share hawayen da suka zubo mun,  na mik'i duk da jikina ba 'kwari nace Hajiya ni zan koma!.."

"Ok ki gaida mun da Sauddat din!.." Tsayawa nayi ina kallonta ko zata ji tausayina amma sai ta juya mun baya,  haka na ja jikina na fice a falon a ranar k'in komawa gida nayi sai a gidan Kaka na kwana...

Gaba d'aya ban runtsa ba da tunani na kwana jiya sai da safe na samu damar barci, bani na tashi ba sai waje 12:30 gaba d'aya jikina kamar anyi mun duka,  ina gama karyawa Aliyu nazo daukata haushi ya cika mun raina domin tun abin da y'arsa tace mun nake jin haushin sa,  dan yanzu kallon munafiki nake mai da kyar na gaida shi...

Gida ya dawo dani har zan fice yace" Baby!! ranar monday zaki fara zuwa aiki insha Allah,  shiyasa ma na daukoki yau domin zuwa anjima mamanki zata rakaki wajen tantancewa fatana kizo mana da abinda muke so,  Allah ya taimaka!.."
Raina a b'ace nace" umhhu!.." Na fice a motar shiko da idanun ya bini yana hangen zallar rashin kunyata..

Da sauri tazo ta rungumeni tana murmushi kafin tace" oyoyo y'ar albarka!.. "Ina kwana Umma!.." Na fad'a ina sunkuyar da kaina kasa domin Khausarce ta fad'o mun a raina ji nake ina ma nima haka tayi mun lokacin da muka had'u.. bata amsani ba ila kamo hab'ata da tayi tana duben fuskata kana ta turo baki gaba yanda taga nayi a hankali cikin irin maganata tace" me kuma akayiwa Mamanmu?.."

Kasa jurewa nayi ban san lokacin da wani kuka ya kwace mun ba,  rungumeni tayi tana shafa bayana a hankali batace mun k'alaba har nayi shiru,  sai a sannan tace" ya akayi ne yarinyar Abba?.."
Kunyar ta da nauyinta da nake ji shi ya hanni fad'ar ainahin damuwata,  na sake share hawayena cike da shagwab'a nace ni bana son wannan aikin Umma,  bazan iya shiga cikin dandazon mutane ba ji nake kamar duk duniya ta san me na aikata,  bana so bana so umma dan Allah ku rabu dani na wani lokaci!.." na fad'a wasu hawayen na sintiri akan kuncina..

"Ok naji ya isa haka,  amma kin san Aliyu bazaiji dadi ba ko? kina so ki b'ata mai raine?.." " Umma ke kike gani kamar sona yake amma tsakanina dashi babu wannan zancen domin munafikine, duk halin da muke ciki ya kwashe ya fadawa iyalan sa maza da mata,  kin san ma ba cewa yayi kaddarace ta fad'o mun ba haka yace musu cikin shege nayi abinda y'arsa tace mun kenan umma,  ni bana son shi dama chan baa son raina kika aure shi ba,  kuma dole ku rabu bana son shi Umma wallahi bana kaunar sa...

Gaba d'aya ranta ya gama b'aci dani cikin hargitsi ta sharara mun wani mari idanunta jawur tace" kinci ubanki nace kinci ubanki,  shegiyar yarinya ke kenan kullum sai dai abi zab'in ranki,  dan ubanki haka kike so na mutu babu aure duk mijin dana aura kice bai miki ba d'an wannan uba kike so na aura ne,  to ki bude kunne ki da kyau ina son Aliyu a sabida ke bazan iya kashe aurena ba,  mutumin da kullum burin sa shine yaga kin dawo kamar yanda ko wace mace take shine kike kira da munafiki,  to wallahi karki bari nayi fushi dake kinji na gaya miki,  wawuya kawai!.."
Cikin fushi ta wuce a wajen. Niko ina nan tsaya dafe da kunci da bakin cikin da kuma tsoron abinda Umma ta fad'a,  kenan yanzu bata son Abbana ? akan Aliyu zata iya rabuwa dani kenan,  dole ne nima y'ata ta dawo gareni..  Na fad'a a fili..

Kimanin kwana biyu kenan ina fushi da ita, Monday tazo sabida taga yanayi na ita ma ta fita a harkata,  Aliyu yayi mata zance ta lalab'a shi akan bana jin dadi a bari sai wani satin,  ba wai dan ya yarda ba sai dai kawai yasan bata tab'a mai karya ba shi yasa yayi shiru shima,  amma fa yaji babu dadi...

Kamar yanda nayi tsammani hakace ta kasance tun safe nafito farfajiyar gidan ina jiran fitowar sa,  aiko sai gashi da saurin shi yana k'ok'arin shiga mota da sauri na sha gaban sa idanuna har ruwa suke da tsananin masifa,  nace" kaga malan kai nake jira dama!.." Cak ya tsaya zuciyarsa na bugawa da tsananin mamaki na..
" a ta dalilinka Umma ta kirani da shegiya,  a ta dalilinka uwata ta ce mun wawuya, sabida soyayyar ka wai zata iya hakura dani,  so nake muyi ta takare dan na gano ba dan Allah kake zaune damu ba,  ka sakar mun Uwata in ba haka ba kuma wallahi ka shiga uku dani!..." Na murgud'a mai baki na wuce abuna..

Tsananin fushin da yaji yana zuwar mai ya hana shi magana da idanun kawai yake bina zuciyarsa na ingiza shi,  ji yake kamar ya kamani ya zanne amma tuna matsayin shi yasa ya kasa aikata komai har na b'acewa ganin sa...

Wass nake jin zuciyata,  a zaune na sameta da alama yau bata jin dadi har na wuce sai kuma na dawo a hankali nace" ina kwana Umma? banza tayi dani tamkar bata ji ba,  na shagwab'e fuska ina bubuga kafata nace" Umma kiyi hakuri!.." Duk yanda naso mu shirya a lokacin kin bani fuska tayi dole na hakuri ina jin wani sanyi a raina cewar dole mu dawo zama mu biyu...

To wasa-wasa sai da na d'auki lokacin kafin na shawo kan Ummana ta fara kulani lallai tayi fushi dani sosai,  a tsanake nake fad'a mata abunda y'ar mijinta tace mun,  ta bani hakuri aka tayi imani da Allah sai dai in awaje tajiyo amma aliyu bazai aikata ba,  dole na hakuri nima na nemi yafiyarta...

To a boye nake bin shi kullum safiya nayi mai rashin kunya ko zaiji haushi ya saketa,  yau da saurina na biyu bayan sa,  tsayawa yayi yana kallona na wani lokaci a hankali kuma yace" baby nifa bana sakaki a sahun masu hankali,  dan da kina da hankali da tarbiya yanda iyayinki suka dauraki bazakiyi abinda kike mun ba,  Sauddat da ita ta nemi saki da kanta itama kila na iya,  amma kilace ba wai zanyi ba,  in ma wani ne yake sakaki kije ki fada mai yazo da kan shi,  mamanki tayi gaskiya da ta kiraki da wawuya..." Yana gama fadar haka ya shige motar sa..

Maganganunsa tamkar saukar ardune a rayuwata gaba d'aya ya birkita mun tunanina,  na gigice a mutuk'ar zaburi na kwalla ihu zuciyata na tafasa...

Bayan wata biyu komai ya hargitsi mun,  ganin yanda ma tashi hankalina yasa Umma ta fara tunanin rabuwa da aliyu,  da safe bayan sun gama karyawa ta sunkuya har kasa cikin zubar da hawaye tace me karatu in baka manta a pagen farko mun fad'i abinda ya faru wannan shine asalin labarin su,  yanzu zamu daura a inda muka tsaya fatana jina comment to kuma za kuga nayi typing da wuri...

Mrs abubakarce

YA ZANYI farin cikin yata shine burinaWhere stories live. Discover now