_YA ZANYI.?_
_FARIN CIKIN ƳATA SHI NE BURINA_By.
_Usaeenah b. Abubakar_
_(Mrs Abubakar)_🅿2⃣4⃣
Duk yanda naso danne zuciyata abun gagarata yayi domin Najibu wani irin murd'ad'an mutunne bashi da mutunci ko kad'an baya alkunya wajen ciwa mahaifiyata mutunci kamar yau duk muna zaune a palon cikin nutsuwa hira muke hankali a kwance, yau a gidanmu zan kwana a fusace shigo kamar wanda akayi masa sata...
" Ke Ke saudda ashe baki da mutunci baki da tarbiya yanzu tsabar iskaci ki rasa wanda zaki aika da rashin d'a'arki sai rukky ? to kijini nan ni baa kishi a kaina domin wallahi uban mace zanci, sadiya ba taimaka miki tayi ba na aureki amma shine zaki saka mata da iskaci?"
A wani irin yanayi take kallon shi cike da tashin hankali tace" Najibu yanzu abun naka har ya kai kayi mun a gaban y'ata? wanna irin aike ne nayiwa rukky? sannan menene aka ce nayi?.."
" da yake ni sa'anki ne dolene ai ki sakani a gaba da tambayoyi kamar wani d'an cikinki wallahi saude akan sadiya zan iya rabuwa dake ni ba wani saban abu bane a wajena, ko kibi abunda take so ko na sauwake miki!!.."
Cike da tashin hankali Umma na ta durkusa bisa gwiwar ta tana hawaye tace" ka gafarceni mijina wallahi ba abunda na sani akai, ka fahimci halina duk abinda nake inayine akan y'ata domin farin cikinta zan iya komai wallahi, rukky a mota kawai na sakata aka mayar da ita gidansu shima kuma cewar y'atane domin tana tsoron rukky in dare yayi ni kuma bazan so tana furgitaba...
Cikin sauri da mamaki idanun shi a wajen ya dafe kirjin sa yana sallati, dan sunkuyo yayi yana jan numfashi yace" humm ya sunanki ma?.."Saudata tana hawaye tace" sauddat!.."
" wannan yarinyar waye ubanta a kasar nan? ko ba najeria aka haifeta ba, hasalima kece uwarta ko? yanzu tsabar iskaci da wulakacin yar cikin nawace take bata tsoro? ke wannan ma cin mutuncine kuma da yake baki da d'a'a kika dubeni kika gaya mun babu ma sakayawa! Innalillahi ni ko me zan miki na huce saude? ana cin mun mutunci mafi munne a rayuwata tunda nake baa taba yankata irin wannan ba amma zaku gani dagake har ita!.." a fusace ya wuce dakin shi...
Tausayin Ummana ya cika mun zuciya, ganin yanda take kuka sosai abun ya taba mun rai, tashi nayi nazo gabanta cikin sanyin murya nace" Ummana! Inaga zan wuce yau!.." duk da har cikin raina bana so na barta amma ya zama dole muddin ina son ta kasance a cikin farin ciki..."
Share kwallar tayi ta aza murmushin karfin hali tace" ashe zaki iya tafiya ki barni a cikin wannan halin? ce miki akayi yau na fara gani ko ta dalilinki yayi mun haka, shi haka halin shi yake, mutunne me wuyar shaani da abu ya hadaku sai yace zai sakeka, ba wai ina gudun sakin bane muddin akanki ne zan jure komai y'ata, sabida farin cikinki kawai karki damu dani kinji!.."
Har cikin raina naji maganarta sake danne kukana nayi muryata na rawa ce" na jima da sanin haka Ummana amma kema kina bukatar farin ciki, tabbas zuwana ne kuka fara samun sab'ani na san haka ne ta dalilin furicin shi na ranar nan, dan Allah ki barni naje ko zaki samu nutsuwa a gidan mijinki!.."
" Kar na sake ji muddin na isa dake tare ya ganmu haka kuma tare zai barmu, zan rabu dashi indai sai kin tafine.."
Shiru nayi ina kare mata kallo a hankali nace" to ke ya zakiyi?.." "Dame fa?.." kunyace ta kamani kawai sai na rungumeta ina hawayen tausayinta domin tana cikin babbar jarawaba..
Tunda yace zamu gani shikenan barci me dadi yayi mun kaura a idanuna, duk da baya tashi tsiyar shi sai rana tsaka...
Bayan sati biyu tunanin y'ata ya isheni ina mutukar kewarta haka kawai nake jin kukanta a raina in na kwanta ko ina zaune shiru, walwalata ya ragu sosai gashi kullum ina kiran Kaka a waya amma bata taba mun maganar khausar ba duk na shiga damuna, tsaki nayi a fili ina tunanin wauta ta na bari jariri kamar khausar har na wata guda...
Ummana tayi murmushi a hankali tace" ji kike a ranki kamar kiyi tsutsuwa kije ki ganta ko? kiyi tunani ya naji lokacin da nayi shakara 1 ba tare dake ba matso nan Asiyya!.." ta fada tana nuna mun kusa da ita...
Jikina yayi sanyi kalau a haka na matsa kusa da ita, hannuna ta kama kana tace" lokacin da na fice a fusace daga gida, zuciya na cina akan abunda banda iko dashi, ko nisa daku banyi ba ciwona ya tashi jin alamun shi yasa na tsaya a gefen titi, baby kwana nayi a wajen babu me taimako na sai Allah ni kaina na dauka na mutu a sailin, ba wanda yayi tunanin da mutun a cikin motar sabida kin san yanayinta, Allah cikin ikon sa sai ga Najibbu shi da matar sa su suka taimaka mun har zuwa asibiti, itama bata da lafiya amma ta danne nata domin nawa yafi nata, na takaice miki na sha janyya sosai Sadiya da najibbu suke kula dani tunda na farfado kullum bakina baya rabo da fadar baby, tambayar duniya sunyi mun akan ina a halina naki gaya musu ba dan komai ba sai dan fushin da nake daku, ko da aka sallamo ni har gida su Sadiya suka rakoni ganin ina zama ni kadai yasa najibbu da mukayi soba dashi kamar mun jima da sanin juna ya dauko yarinyar shi rukky baby ya bani, ni kaina a ganin farko na da ita naji wani iri amma na daure sabida wanda zai baka kyautar y'a lallai abun a duba bukatar sane...
Ban san ya akayi ba sadiya ta sauya a yanda na santa, sai ya zamana kusan kullum sai tazo har gida ta ci mun mutunci hadin da kirana maciya amana, abinda bata sani ni kaina ban san mijinta yana sona ba, wani abu da ya daure mun kai kuma bayan kwana biyu sai gata ita dashi sunzo akan suna neman aurena abun ya daure mun kai sosai nayi dogon tunanin a karshe na fada musu ni ba aure a gabana yanzu, akalla sunyi mun suntiri yafi sau ashiri mun dauki watani da su ta sake zuwa ita kadan akan mijinta bashi da lafiya kuma duk akan sone lallai na amince ko dan na ceto rayuwar shi, wallahi baby muddin kin yarda dani ban taba jin son najibbu a rainaba na aure shine kawai dan na taimake shi kamar yanda ya taimakeni a lokacin da nake neman taimako, shine dalilib auren shi.. Sai daga baya na gane duk shirin sadiya ne ita a tunaninta soyayya muke dashi ta bangaren shi ta zubar mai da mutunci a wajena, haka nima sai bayan aure na gane shi wani irin mugun mutunne wanda zama dashi sai ka jure, masifar shi kuwa akan abu kalilan ma fada yake na cin zarafi sam bashi dadin zama, ga guri ko sabo ya siya sai yayi gori akai ke a takaice dai zama dashi din sai sadinyan shi, a wancen ranar nayi kuka ne sabida bacin cikin yanda yake muzan tani a gabanki ne baby, bazan so na bukaci saki da kaina ba amma ina addu'a Allah yayi mun zabi mafi alhairi a zama na dashi, matar shi agaban shi ita cikaciyar me tarbiyace ga hakuri da kawaici amma ni a wajena tafi barkono zafi, in kin san balai'n da take had'a mun sai kin rike baki wallahi, baby har kullum fatana Allah ya kawo mun ranar da zan ku ko dan neman yafiyar ku domun ina jin kunyar zuwa inda kuke, baby ki yafe mun dan Allah?.."
Ta fada cikin sanyin murya murmushi nayi a hankali nace" a tsakanina dake babu wannan umma kin isa kiyi komai, har abada bazan ga lefinki ba dan Allah ki daina neman yafiyar nan tawa haka ya isa, abinda nake so dake daya ne ya kamata kije ga kaka suna kewarki sosai!..*"Taya zan fuskace su baby? bayan nayi musu babban lefi ciki har da aure ba tare da sanin su ba, banzan iya ba gaskiya!.."
" inaga shi yasa ma baku samu daidaito ba ki daure umma Kaka tana jiranki a ko yaushe kuma bazata kullaceki ba!.."
" Na gode baby na! Allah yayi miki albarka!.."
Kutt lokacin girki yayi fa sorryn ku!
Mrs abubakar ce

YOU ARE READING
YA ZANYI farin cikin yata shine burina
Short Storylabari ne me tab'a zuciya hadi da cakwakiya me zafi