Chapter 26

3 1 0
                                    

_YA ZANYI.?_
_FARIN CIKIN ƳATA SHI NE BURINA_

By.

_Usaeenah b. Abubakar_
_(Mrs Abubakar)_

'''NA GODE DA KAUNA MASOYA NA NA HAKIKA,  DUK DA YANAYIN YANDA KUKE SAMU POST HAKAN BAI SA KUN DAINA BINA BA,  INA ALFHARI DAKU MASOYA NA'''


Tabbas Sauddat ta shiga matsanancin tashin hankali a lokacin da doctor yace zan iya kamowa da ciwon zuciya a ko wanna irin yanayi, firgicin da take ciki shi ya hanata magana ko motsi meroce kawai ta fahimci halin da take ciki,  da taimakon ta suka fito daga office din doctor...

Kamar yanda ya fad'a Kaka tayi komai nawa kana suka zauna zaman jiran farkawa ta, ga khausar sai kuka take kamar ta san uwarta ba lafiya, gaba daya hankalin hajiya a tashe yake ga matsalata gata y'ata...

Bayan kwana biyu cikin hukuncin Allah yau na fara motsa idanuna tamkar zaka kirani na amsa,  gaba dayan su zagayeni sukayi zuciyoyin su cike da matsananin firgici, ko wace kirjinta bugawa yake zuciyarta na zullo..."

Ina jingine a jikin hajiya kaka wanda tunda na bude idona banyi magana da kowa ba sai ido kawai na zuba musu, a hankali ta miko mun cop din tea tana fadi bude bakin ki,  kisha ko zakiji karfin jiki ki domin har da yunwa ma tana daminki, a hankali na kalleta take naji wasu hawaye masu tsananin zafi da kunar zuciya na zubo mun,  cikin rawar baki nace"akan gaskiyata yau Ummana ta daga hannu akai na, tace wai akaina ta rasa aurenta! kenan ni na kashe mata aure? Hajiya yaushe zan hutane? wai shin ni kadaice nake fuskantar irin wannan rayuwar ne? ta zab'i mijinta akaina Kaka dan Allah ku nisan tan!...

"Shittt! ki nutsu Baby kiyi shiru na san komai kiyi hakuri kinji amshi ki sha,  sai muyi magana ko?.. Cikin rarashi da sanyi murya tayi maganar daga gani ba karamin kad'awa zuciyarta ke mata ba...

A hankali nake amsa zuciyata babu dadi zuwa chan hajiya tace" Baby ya jikin naki?." Shiru nayi mata domin bana son magana yanzu..

Kwanan mu uku muka dawo gida yanzu gidan hajiyar jabeer muka sauka naji sauki sosai amma fuskata babu walwala ko kadan, ga  tsananin tsanar Khausar dake cimun rai sosai bana ko kaunar ganinta ko jin motsainta kusa dani,  a yanda na saka a raina komai da yake faruwa dani ta dalilinta ne da ubanta,  ganin irin tsanar da nake nuna mata a gaban kowa kuma har cikin raina nake jin kyamar ta,  wannan dalilin yasa hajiyar sauddat dawo dani gidanta...

A yanzu ina rayuwane ta y'ancin kai bana shiga sha'anin kowa ko yaushe ina dakina in na fito falo to dolece ta kamani, a haka kwanaki na sake tafiya watanin na shud'ewa shekaru naja Khausar na da shekara biyu da rabi a duniya,  Ummana tana gidan hajiyan jabeer sai dai tazo fisha ta koma duk da ga baki ga hanci, a yanzu wayata itace abokiyar hirana ko yaushe ina makali da ita...

Zaune take a gabanta cikin mutuk'ar biyayya tace" Hajiya duk yanda kikayi dani ni me biyayyace a gareki bana jin akwai abinda zaki nema a waja na gagara cika miki muddin baifi karfina ba fatana dai ku yarda da nadama ta hajiya..

Murmushi tayi cike da jin dadin kalaman ta tace" Sauddat a yanda na fahimci rayuwarki ke macece mabukaciya a shekara daya da watanin naga yanda kike takatsantsan dan gujewa sab'o,  gaba daya har yanzu kina ji da kuruciya ga kofofin sha'awarki ba rufewa sukayi ba, abinda nake so ki sani ranar alhamis insha Allah za a daura aurenki da wani dan uwana Aliyu ina fatan zakiyi mun kyakykyawar fahimta?.." 

Cike da tashin hankali take duban hajiya bakinta har rawa yake cikin azama tace" hajiya nayi wa kaina da y'ata alk'awari mudin zata kasance cikin farin ciki to ba makawa zan hakuri da aure har sai ranar da ta amince mun da bakinta, ko dah ko shaawa zata kasheni a yanzu farin cikin ta kawai nake nema hajiya, bana so ta sake fuskantar wata matsala a ta dalilina nima ki fahimceni dan Allah bazan aure shi ba har da yarda ta..."

"Sauddat kina so ki aikata lefin da girmanki? in abinda ya faru da y'arki ne kike gudu karki manta dangantar dake tsakanin Asiya da Aliyu shi kamar uba haka yake a wajenta in da mutunci,  kuma sa'annine shida jabeer nayi imani da Allah bazai wulakantaku ba ke da Asiya ni dai ki amince mun?.."

" kiyi hakuri hajiya nima FAFIN CIKIN Y'ATA SHINE BURINA a yanzu haka mafarkina bazan iya ba!.." tashi tayi ta shige cikin d'aki..

Hajiya ta gyara zamanta cike da jimammi gashi tayi gaban kanta yanzu in yarinyar ta bijjre mata YA ZANYI?...

Ina kwance kamar ko yaushe hajiya ta shigo kallo daya nayi mata na kawar da kaina gefe,  ta yamutsa fuska cike da tunanin yanda zan amshi zancen ta a hankali tace" takora sarkin daru tashi muyi magana me mahimmaci.."

Cike da izza nace" ina jinki ai hajiya!.." "Iyee yau akaina iya shegen naki zai sauka,  to shikenan na fasa.." tana rufe bakin ta tafice a dakin, na runtsi idanuna a hankali nace me yake damuna ne? ya kamata na bita!...

"Hajiya abinda nake so ki fahimta a halin da yarinyar nan take ciki yakai har surutai takea cikin barcin alamar abun yana ranta sosai ba yanda zatayi ne,  Sauddat irin matanan ne mabukata muddin ba'ayi mata uziri ta sake wani auren ba to komai zai iya faruwa,  gara takora ta ita kaddarar ta yasa aka samu yarinyar kirki khausar bana fatan a sake samo wata ta wannan hanyar dan Allah ki tayani rarashin Asiya yanda zata fahimince mu domin Sauddat tace ita baza taba wani auren ba har sai Asiya ta yarje mata da bakin ta,  ina ganin abune mayiwaci ta amince ta sauki a yanzu ma da na fito a dakinta agatsali ta amsa min, kinga ba yanda zaayi na samu fuskar yi mata wannan maganar..."

" naji duk bayanenki hajiya ba damuwa kar a fasa daurin auren akan wannan bazan dalilin nasu,  da ta kwaso mana wata masifar gara ayi auren daga baya zasu fahimci juna, Baby kuma ki barni da ita!.."

" Kina ganin ba matsala sauddat fa bata taba mun musa ko kin abinda nace ba sai jiya kai tsaye ta gaya mun abinda ke ranta, bana so mu shiga hakin su.."

"Ni nace ayi ai ko hajiya? to kar a fasa!.."

Take wasu hawaye masu zafin gaske suka wanke mun fuska,  ji nayi kamar jiri na shirin kadani na dafe bango ina jin zuciyata babu dadi tausayin ummana yana sake cika mun zuciya, a hankali nace zan amince umma zan amince insha Allah, da sauri na koma d'akina ranar na sha kuka tsorona daya kar abunda ya faru a baya ya sake faruwa a yanzu...

Mrs Abubakar ce

YA ZANYI farin cikin yata shine burinaTahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon