chapter 7

10 0 0
                                    

_YA ZANYI!..?_
_(FARIN CIKIN ƳATA SHI NE BURINA)_


_BY_.

_USAEENA B ABUBAKAR_

*(MRS ABUBAKAR)*


🅿7⃣

Sauddat ta mike zaune cikin k'arfin hali, tana wani irin kuka me mutu'kar cin rai, ta dube shugaban yan fashin ta sake fashewa da kuka cikin murya me raurawa tace" wai shin me kuke buk'ata ne haka? waya aiko ku? ko kashe mu kawai kuka shigoyi?..."

Murmushi yayi me sauti kana ya zaune a daya d'aga cikin kujerun d'akin yana wani langwabar da ka gefe yace" wanda ya aiko mu ba damuwarki bane, in kina buk'atar rayuwar mijikin to ki bude wa can kofar mu dauki abinda ke gaba mu, kema ki tashi da kafarki ki bimu!.." cike da gadara yake maganar...

Ta dube d'akin da nake zuciyar na sake harbawa tace" menene yake gaba na ku? me kuka ajiye a d'akin? inda aka kudi kake aiki nayi muku alkawari ko nawa kuke da buk'ata zan baku amma dan Allah karku tab'a min iyalina duk da kun gama nakasa min miji na!..."

" Ba kudi muke so ba Yar ku mukazo dauka!! da ke kanki!! umarnin da aka bamu kenan duk wanda yayi mana taurin kai kuma mu fasa kan shi da bindiga..." ya fad'a Yana huta mata kurar bindiyar...

Tsantsar rainin hankalin sa take gani, a hankali ta ja jikin ta har zuwa ga mijinta ta dago kan shi tana kallon shi yana kallon ta fuskokin su jike da hawaye, tamkar had'in Baki sukace" mun amince ka kashe mu kawai!!..""

Zuciyar sa ce ta tsinke gani yanda suke bata musu lokaci a banza, gashi basu samu biyan buk'ata ba, kallo daya yayiwa wanda hannun sa ke rike  da gora ya karaso kan ta, babu ko digwan imani ya shiga jibga mata a ta ko ina a jikin ta, wani irin ihu Umma na keyi wanda hankalina yaki kwanciya nima na shiga bugun kofar ko Allah zai sa ta bude, ihu nake ina kiran sunan ta amma a banza ji nake kamar bata jina....

Ta kankame Jabeerr sosai a jikinta ta yanda dole ita zaa daka, tana ihu da kuka shima yana kukan tausayin matar sa ga azabar dake adabar kafagun sa, ko gani sosai bai cikayi ba domin ya zubar da jini sosai, ta dube yanda yake kuka hawaye na fita a fuskar shi kamar karamin yaro itama kukan take tunda har yanzu dukan ta yake, a hankali tace" ina mutu'kar k'aunar ka mijina! nima na sadaukar da rayuwata domin ka!..." ganin tayi yayi wani irin juyi da ita, maana ya mayar da ita kasa shi kuma ya k'asance a k'asa, tasss Tass tass!!! shine sauti na k'arshe da Ummana ta sake ji kuma daga haka bata sake fahimtar komai ba...

Ihun Abba na ne ya firgita kowa ciko har da makwaftan mu, su ma kan su sai da wani tsoro ya ratsa su, duk da baya gani sosai haka yayi ta maza ya cafke wanda ke kusa dashi ya caka mai wukar da ya suka mai a baya,  shugaban ya mike zeyo kan shi shima ya cilla mai wukar bata sauka a ko ina ba sai a makogaron shi, cak ya makale a wajen yaran da suka rage su uku tsoro yasa su ma suka fice da mugun gudu, duk  yanda shugaban nasu  yake neman d'auki had'i da kallon su ta wutsiyar ido, amma ko ta kan shi basu bi ba...

Abba na ya yanke jiki shima ya fad'i a wajen warwass babu ko motsin kirki!....

Abin mamaki tafiyar su ko minting ashirin baayi ba sai ga motar yan sanda da ambulance,  har yanzu Ina bugun d'akin irin yanda nake dukawa shiyajawa hankali mutanen sukayo waje na da sauri, babu yanda basuyi ba amma kofat taki budewa, Sauddat aka daga zaa fita da ita zuwa mota sai ga kye ya fado d'aga jikin ta, babu wanda ya kula sai makocin mu da ya kawo Yan sandan, dauka yayi zuciyar sa na bashi ko d'akin da yaki budewa Aiko yana gwadawa kofar ta bude  suna zuwa kofar bayin nan ma suka budeni, gaba d'aya basu nee a gaba na domin tankade su nayi nayo falo da mugun gudu, cak na tsaya gani Abbana cikin jini male-male na shiga takowa kamar ana turani hawaye na bin kunci na, a haka har na iso gare shi ban damu da jinin dake wajen ba kai tsaye na fad'i a gaban shi hade da kai hannu zan tab'a shi, wani can daban yayi saurin dakatar dani da fad'i malama karki tab'a shi!..

Ko kallon shi banyi ba na rungume Abba na sai a lokaci wani kuka me karfi ya kubuce min, idanuna ya sauka kan wanda ke ta raba ido a cikin bakin kyale ga wuka data ceke mai a makogaro,  ko baa gaya min ba shi ya kashe min Abba na tashi nayi na nufe shi da mugun nufi, cikin sauri makocin mu ya rik'e min hannu da sauri na dube shi cikin mugun zare ido nace" sakeni dan ubanka, shi ya kashe min iyaye ne fa..."

Mafarin kenan

Ikon Allah Fan's ni ko me Asiya zatayi ne?🥺🥺

Comments

Shared duk wace ta karanta ta shared please

YA ZANYI farin cikin yata shine burinaWhere stories live. Discover now