_YA ZANYI.?_
_FARIN CIKIN ƳATA SHI NE BURINA_By.
_Usaeenah b. Abubakar_
_(Mrs Abubakar)_🅿1️⃣6️⃣
A hankali take bani a baki ina ci, cikin na na sake motsi cikin gajiyawa nace" Hajiya nifa har yanzu ban daina jin motsin ba, kuma kince yunwace amma me yasa dah bana ji?.."
Murmushi tayi cike da hikima tace" karki damu takora zan gaya miki dalili amma sai kinyi mun wani alkawari?.."
Cike da zaƙuwa tace " nayi miki faɗa min?.."
Tausayin ta ne ya sake ratsa su cikin ƙarfin hali Sauddat tace" hajiya ni zan wuce in kin gama ina ciki?.."
Da kallo kawai suka bita domin sun gane nufin ta...
" Asiya a sani na ke macece me hakuri da juriya, kamar yanda kika amshi abinda ya faru a baya a matsayin kaddararki a yanzu ma ina so ki sa a ranki jarabawarki kenan, Ummanki bazata jure ganinki a wannan halin da kike ciki bashine dalilin tashin ta da kuma kukan da kikaga tanayi, Asiya ina me sake baki hakuri akan abunda ya faru da kuma wanda zaki fahimta yanzu, sannan ina so ki cika min alkawarin da kika dauka duk da na san tashin hankali ya zama dole musamma ga ke din to amma bama fatan haka, dan Allah Asiya kisawa zuciyarki salam ki dauki dangana kamar yanda kika rasa abu mafi daraja a rayuwarki har kike kunyar fita, ya zama dole ne mu fada miki domin ko baki sani yanzu ba nan gaba zaki sani, tunda kin fara fahimta Asiya ki kasance me yarda da kaddara me kyau ko akasin haka dan girman Allah, Asiya kina dauke da juna biyu shine dalilin motsin da kike ji in kina jin yunwa ko in ki kayi kwanciya marar kyau!!!...""
Gaba daya jina da gani na ne suka ɗauke na wani lokaci ji nake kamar ba dani take, domin tunda ta fara magana zuciya take zullo ji nake kamar na mutu a take na huta da jin takaici, maganar ta ta karshe ce ta sake ɗimautani a hankali na haɗi wani maiyau me tauri, wani irin kallo nake musu daga ita har Kaka ji nayi gaba daya ban yarda dasu ba, miƙewa nayi zan wuce Kaka tai saurin riƙeni a matuƙar fusace nace" sake ni.." a yanda nayi magana duk taurin zuciyar ka dole ne kayi shakata, magana zatayi nayi saurin fincike hannu tana shirin bina Hajiya tayi saurin dakatar da ita, har na gota zai wuce daki na sai na hango Sauddat a zaune kain ta a tsakakanin cinyoyin ta, a hankalin sautin kukan ta yake fita ji nayi jikina ya sakeyi sanyi kusa da ita naje na zauna duk da bata san nazo ba amma kallon ta nake, na rasa abunda nake ji akanta ajiyar zuciya na sauke duk da wani irin nauyi tayi min ga wani zafi-zafi da zugi da nake ji, hannu na daga har zan tab'a ta sai kuma na sauke cikin rashin sonyi magana nace" Umma!!..."
Da sauri ta dago ganina ba karamin sake d'aga mata hankali yayi ba, tayi saurin kau da kanta gefe a sanyaye nace" hmm bana gane komai yanzu Umma, wasu irin magaganu Hajiya ta gaya mun wai me suke nufi? nifa damuwa ta d'aya ne su kuma naji suna gaya min wani abu da bai shafi rayuwata ba, Umma da gaske ne Ina da ciki?? kuma dama anayi ciki ne haka kawai? nifa kamar bani da hankali nake gani! ji nake kamar mafarki nakeyi shin ya zanyi ne Umma? dan Allah ki fad'a min da bakin ki sai na fi yarda akan nasu! ya za'ayi nayi ciki ni kad'ai??..."""
Har yanzu kuka take kuma tak'i bari mu hada ido, saukuyawa nayi sosai ta yanda zan hango kwayar idanun ta, lumshe idon ta tayi tana jingina da bango, kallon ta nake ina jin wani saban yanayi a tare dani hannu na d'aga na dangwalo hawayen nata tamkar taɓaɓiya haka na zama a gaban ta, a hankali nace " nima zan so nayi kukan Umma amma na kasa, zan so hawaye ya zubo min ko zanji sausauci a zuciyata, ni ya kamata nayi kuka ba ke ba Umma ni kuka ya kama har karshen numfashi na, komai fa a ta dalilinki ne kin auri wanda bai dace damu ba, ke kika jawo komai Umma akan mene zakiyi kuka? wannan damuwa tace ni wai ni nake d'auke da ciki, cikin ma ba'a san waye uban shi ba? to wai ta yaya? me yasa shi baa kamo shi ba? yaushe zan huta ne Umma!? nifa gaba d'aya yanzu na tsani kai na, _na jure na baya amma bazan jure wanna ba dole ne na mutu Umma! Eh a yau kuma bazan iya dakon cikin da ban san uban shi ba_ ..." cikin sauri na bar wajen har yanzu bata dago ba...

YOU ARE READING
YA ZANYI farin cikin yata shine burina
Short Storylabari ne me tab'a zuciya hadi da cakwakiya me zafi