_YA ZANYI.?_
_FARIN CIKIN ƳATA SHI NE BURINA_By.
_Usaeenah b. Abubakar_
_(Mrs Abubakar)_Washe gari
Sama sama nake jin kamar ana hayaniya a falonmu, tsaki nayi a zahiri nace wannan mutumin sam bai da dadin zama wallahi kullum cikin rigima. fuskata na wanke tass kana na fito falon wata macece a tsaye akan Ummana yayin da ita kuma take zaune akan kujera, nuna ta take hannu bakinta na kumfa...
" me yake faru?.." Na tambaya lokacin da na iso tsakiyar falon..
Murmushi Ummana tayi mun kana tace" Baby na kin tashi?. "Eh Umma ina kwana?.."
" Lafiya kalau yar gatan Abba!.." ta fada cike da zolaya, dariya na sanya domin har ga Allah abun yayi mun dadi...Matar ta sauki ajiyar zuciya had'i da cewa" Saude dake nake magana, kika wani shareni kina magana da tsohowar killakin da ta ajiye miki shegiya! in ba.."
Marin da Sauddat ta sauke mata a fsuka shi ya dakatar da ita ga abinda take son cewa, idanunta sun kad'a sunyi jawur yayin da jikin ta ke rawa ta sake kiffawa Sadiya mari game da hankadata tun karfin ta, tana fad'in ban haifi kilaki ba kuma insha Allah bazan haifa, kaddarace kuma tana kan kowa daga yau sai yau in na sake ganin kafarki a gidan nan wallahi tallahi sai na lahira yafiki jin dadi, ki bar ganin a baya ina kyaleki a yanzu kin tabo inda ko ubanki ba isa ya taba mun y'a na kyale ba bare wata ke can kuchaka, wawuya marara kamun kai da daraja, wace bata san mutuncin kanta ba bare na y'ar cikin ta, daga yau kika sake shigowa shaanina sai na an daureki wallahi!.." Cike da zafin ra Sauddat take maganar yayin da Sadiya take tsaye hannunta akan kuncinta itama zuciyarta na raradi, gashi ta kasa magana gudun kar sauddat ta sake marinta...Ummana ta juyo gareni bana wajen, gabanta yayi mummanar faduwa cike da bakin ciki tace" wallahi in baki fita ba zan fitar dake da mari ko na saka wayar chaza na zaneki har waje!.." Ta fada a tsawace..
Sadiya da sauri ta nufi kofar fita tana fad'in " inda ina numfashi a duniya zakiga abinda zanyi muku wallahi!.."
Dakina ta biyoni samuna tayi a zaune ina aikin kuka, jikin ta yayi sanyi kalau zatayi magana nayi saurin katsita da fad'in" dan Allah Umma ki rabu dani! dama na san wannan auren naki ba abinda zai jawo mun sai kaskanci da cin mutunci, da ace bakiyi ba ya wa isa ya shigo har cikin gidan ubana ya kirani da kilaki? kije kawai bana son jin komai daga gareki Umma!.." cike da tsiwar nayi maganar wanda tunda nake a duniya ban tab'a mata haka ba...
Kasa magana tayi zuciyarta nayi mata soya a haka ta fice a d'akin, ni kam kuka na sha tun yanzu ma kenan ina kuma ga yarinyar ta girma nan gaba me zaa kirani dashi...
Ko minti talatin da fitar Sadiya baayi ba Najibu ya shigo cike da hargowa, tun kafin Umma ta fito yake surfa mata ruwa jaraba, banda ke ba y'ar mutunci bace shine zaku hadu ke da karuwar y'arki kun jabgar mun mata kamar Allah ya iko ku, to wallahi yau itama zaki ga gatan ta, ba kince kiga wanda ya tsaya mata ba to gani nazo..."
Da gudu Sauddat ta fito hankalinta a mutuk'ar tashe bata kwantar da wannan wutar ba ga wata taso, " najibu kana da hankali kuwa y'ar tawace karuwa?.." Idanunta har sun kawo ruwa!
" Eh karya nayi ba karuwar bace? ya akayi ta haihu ba tare da aure ba? ko a ruwa ta sha? wallahi dukan da kukayi wa Sadiya bazai tashi a banza ba kema sai kinji a jikinki dagake har shagiyar yar taki!.. Ya fada yana shirin kai mata duka tass tass tass kukeji sauddat ta k'ame a wajen idanunta a waje, tsor hadi da mamaki ya hanata motsi shima Najibu ya kame fuska yana gwalalo ido waje ganin irin kokarina da masifar taurin idona...
" Ni ba karuwa bace! in kuma kana neman karuwai ka koma gida zaka samu domin can ka baro su, shin menene lefin yarinyar da akayi wa fyade har Allah yasa ta samu rabo ta dalilin haka? shin kai baka san kaddara ba ne ? a kaina faru ko a kaina k'aru? ko nina kai kaina ne shikenan ku mutane baza kuna mana uziriba mu da mummunar kaddar ta fad'o mana, kayi tunanin a matsayin ka na uban kuma y'ay'a matan nan sune a gidan ka dah ni y'ar cikin kace ya zakaji? ya zakaji in matarka tazo har gida ta kirani da kilaki ? me kike tunanin da ubana yana raye? nayi imani da Allah da sai ya saka ana daureta wallahi domin son da yake mun ya ninka wanda kake kira da shirme, dan kana aurenta shine zaka daketa a wanna hadisi aka ce ka dake mace? kar ka manta kaddara tana kan kowa kuma a ko wanne lokaci ka ma zata iya fado maka cikin ahalinka a lokacin zaku gane ni kilaki ce ko karuwar da ka kirani dashi, auren uwata kawai kake amma karka wuce gona da iri akan ka kawai na kasa rike hakurina na dauki na matar ka amma bazan dauki naka ba har abada..." Na juya cikin kuka na wuce dakina...
YOU ARE READING
YA ZANYI farin cikin yata shine burina
Short Storylabari ne me tab'a zuciya hadi da cakwakiya me zafi