_YA ZANYI!!...??_
_(FARIN CIKIN ƳATA SHI NE BURINA)__BY_.
_USAEENA B ABUBAKAR_
*(MRS ABUBAKAR)*
🅿6⃣
Wani irin karfine yazowa Abba na cikin kwarin gwiwa ya tsinke igiyar da suke d'aure shi da ita, wani tsalle ya daka ya shake wanda yake k'ok'arin zuwa inda nake, kokawa ta sake barkewa a tsakanin su, dama da kyar suka d'aure shi da yake sarkin yawa yafi sarkin k'arfi, sai gashi suna k'ok'arin kai shi kasa a karo na biyu, wani mugun naushi ya azawa na gefen shi sai gashi warwas a k'asa, fad'a ya sake kaurewa a tsakanin su, ran ogan su in yayi duba ya baci ganin irin barnar da jabeer ke mai, kai tsaye ya saita Sauddat da binding cikin rashin imani yace" Jabeer muddin baka bamu had'in kai ba bamakawa sai na fasa kan ta da harsashi, ya fad'a yana shirin danna kunamar...
Cak ya tsaya zuciyar sa na wani irin bugu a zahiri kuma fuskar nan tashi fal murmushi yace" ka duba da kyau ita ta ai ta kare, bana jin kana gani sosai in ka fasa fasa kanta kai ba dan halak bane, yana kaiwa nan ya fizgi binding na kusa dashi kafin yayi wani motsi tuni ya habe na kusa da d'akin da nake ciki, gaba d'aya su tsoro ya kama su suka fara kallon junan su, ko wanne ya saita Father a dai-dai lokacin kuma Sauddat ta farka cikin mayuwacin hali take bude idanun ta, a hankali kallon ta ya sauka akan mijinta dake rik'e da bindiga take zuciyar ta ta buga da k'arfin bala'in, ta shiga tari abinda ya mayar da hankali su gaba d'aya kanta, shima cikin azama ya jefar da bindiga yayo kanta da mugun sauri baiyi taku uku masu kyau ba, yaji wani irin sauti marar dadin jin ya giftashi, Sauddat ta saki wata muguwar kara me hawa kai cikin tsantsar tashin hankali marar musaltuwa ta kira sunan shi muraran " Jabeerr!!.."
tana me daura hannun ta akan lips dinta...Sai yanzu yaji wani irin zugi a gefen cinyar sa cikin tsananin kaduwa yake duban waje, jini ya fara zubuwa cikin juriya ya sake takowa zuwa inda Sauddat take, babu imani a zuciyar shugaban Yan fashin ya sake dirka mai harbi a lafiyayiyar kafar Jabeer ya zube a k'asa hawayen takaici na zubo mai, duk da irin azabar dake ratsa shi haka bai hana shi zuwa ga Sauddat ba, bashi da burin da ya wuce yaga ya kareta d'aga muguwar niyyar su, ya shiga jan jikin sa kafar sa na fitar da jinin, gaba d'ayan su suka kwashe da muguwar dariya

YOU ARE READING
YA ZANYI farin cikin yata shine burina
Short Storylabari ne me tab'a zuciya hadi da cakwakiya me zafi