_YA ZANYI.?_
_FARIN CIKIN ƳATA SHI NE BURINA_By.
_Usaeenah b. Abubakar_
_(Mrs Abubakar)_🅿9⃣
Kwana biyu tsakani ido na zuba mata kamar yanda ita ma ta zuba min ido, kayana na haɗa sosai nake shirina sai dai tabbatar na kalama sannan na fito falo me aikin na sa ta fita dashi wajen mota ni kuma na shiga ɗakin ta, a zaune ba tarar da ita kamar me tunani cikin wani yanayi nace" Umma! ni zan wuce!.."
Tamkar saukar aradu haka taji maganar tawa, ta dube ni da kyau sannan tace" ina zaki baby?.."
" Inda zaa bani kulawa da na rasa a nan!!!.." Ina fad'a nayi waje da sauri domin ban San amsar da zata bani....
K'amewa tayi a zaune ta kasa ko da motsi tashin motar da taji shi ya dawo da ita d'aga tunanin da ta lula, cikin sauri tayo waje sai dai kafin ta iso har na fice a guje kamar bazan tashi sama, kuka nake zuciya na sake bani shikenan Umma bata so na yanzu, Abba na ya tafi ya barni ita kuma ta Alhaji salisu take ba tawa, da k'arfi na saki wani marayan kuka cikin karaji nace" Ina sonki Umma! me yasa kika sauya? na dauka zaki biyo bayana amma irin ko a jikinki din nan ma kika nuna mun..." A haka na isa gidan Hajiya babba ina kuka, sosai ta shiga tashin hankali sai bayan na nutsu ne nayi nata karyar kaina ke ciwo...
Sauddat ta jima tana jimamin ina tafi a k'arshe ta d'auki shawarar zuciyar ta duk inda naje ma zan dawo ai, wasa² har dare yayi shiru babu ni babu dalili na tun tana duba a gogo har ta gaji ta fito getman ta tambaya dame na fita a nan ne yake fad'a mata, kwati ce guda na wuce da ita tun a gorin ta fara sharce zufa...
Bazan iya fad'a muku tashin hankalin da Sauddat ta shiga a lokacin da taje duk inda take tunanin zanje bata gani ba, hankalin ta yayi masifar tashi haka ma hajiyan ta a cikin su babu wanda yayi tunanin zanje gidan Hajiya babba, shi yasa suma basu je nan nemana ba gudun kar su d'aga mata hankali, tun mutuwar Jabeer ta dawo a lalab'a itama...
YOU ARE READING
YA ZANYI farin cikin yata shine burina
Short Storylabari ne me tab'a zuciya hadi da cakwakiya me zafi