Chapter 13

8 0 0
                                    

_YA ZANYI.?_
_FARIN CIKIN ƳATA SHI NE BURINA_

By.

_Usaeenah b. Abubakar_
_(Mrs Abubakar)_

🅿1️⃣3️⃣

Dabara ce ta fado min yau salisu zai kwana a gidan nan, duk yanda za'ayi yau sai nayi ido biyu da me shigo min, dole ne ma sai na kama shi...  haka na k'udire a raina..

Can gefen bed dinna kwanta yayin da na jera filo hadi da lulub'e su, hannu na dauke da fitila wace ta ji chaji hasken ta har yafi na NEPA,  fakare nayi ina jira amma shiru babu labari gajiya nayi na mike da nufin komawa makwanci na a hankali naga ana murd'a min kofar d'aki, cikin sauri na koma na kifa kaina, ba jimawa ya shigo gaba d'aya  gadon ya tsaya kallo yayin da nima nake hangen sa ta tsakan-kanin bed, hannu ya ɗ'aga zai yaye bargon kamar yanda ya saba, cikin wani mugun sauri na haske mai fuska da fitilar hannu na, innalillahi shine abinda ya fito a baki na, wani bakin mutune babu ko kyan gani ni tunda nake ma a rayuwata ban tab'a ganin shi ba sai yau cikin dakewar zuciya nace" Allah ya kamaka mugun bawa,  shin me na tsare maka ne rayuwa? ka adabeni ka hanin sukuni, ka hanin samu kwanciyar hankali ni da gidan ubana, wai menene matsalata da kai ne, me na tsare maka?..."" Cike da juriya nayi tambayar domin shi ko a jikin sa, sai  ma murmushi da naga yana yi mun..

" Ke yarinya ce bazaki taɓa ganewa ba, amma yau nayi farin ciki da na sameki idanunki biyu a yau zanyi abinda yake kawo ni na gama, nima na huta da yawo..."

Yana rufe bakin shi ya kawo min wata muguwar sura, cikin matuƙ'ar sauri nayi kasa a guje ya cafki isakar wajen, cikin bacin rai ya kalle ni kana ya sake juyowa a zafaffe, nima banyi wata-wata ba na raɗa mai gilas cop din dake kan mirro dinna, cikin sa'a ya fashe akan shi, take jini ya shiga zuba wani irin ihun azaba ya saki, inda nima na saki kara haɗ'i da ƙwalawa Umma kira...

Da dukan alamu na ƙure hakurin sa a haukace yayo kaina da mugun nufi, nima ban tsaya kallon shiba na nufi ƙofa da niyyar guduwa, cikin rashin saa ya cafke ni da wani irin mugun ƙarfi ya makani a jikin gini cikin zafin nama ya shiga zare min kayan jikina da mugun nufi, ga wani mahaukacin ruƙo da yayi min, numfashi nake sama-sama cikin tsananin tashin hankali nake nema ɗauki amma shiru ba wanda ya shigo,  hannu nane ya faɗ'a akan  sauran ƙwalbar da ta fashe zuciya ta gama tsinkewa banyi tunanin komai ba na soka mai ita a dantsin hannusa, ba shiri ya sakine na yunƙura zan miƙ'i ya sake dawo dani mari na yake ta ko ina, dan-danan ya haɗa min jini da majina, cikin wahaltuwa na damƙi mai fuska da faratunan hannunna abun mamaki sai gashi na ƙwashe mai fatar fuska, ga mamaki na ko ɗigwan jini babu wani irin ƙarfine yazo mun ban san lokacin da na dakar mai alaurar sa ba, ya dafe gaban shi cikin mutuƙar azaba yana zufa kamar ana watsa mai ruwa, ni kuma na shiga ja da baya ina wani irin kuka,  da ƙyar na miƙi tsaye cikin sa'a hannuna ya ɗanne maƙunnar ɗakin, take haske ya gauraye ko ina zuba mai ido nayi ina karantar yanayin sa amma na gaza ganewa, tabbas ba fuskar sa na yaƙusa ba face ya saka amma shi asalin farine me gemu, " waye kai?..."
shine abinda na tsinci bakina yana faɗa...

Sam kin juyowa yayi, nima daga haka na fice a ɗakin, a mutuƙar wahale kai tsaye ɗakin Umma na nufa ina numfashi sama-sama, duka ɗaya nayi ma ƙofar ta buɗe tana ƙwance kamar gawa, barcinta take hankali ƙwance a hakuce na raɗ'a mata kira amma shiru bata amsa ba, gadon na haye  hankali a tashe ƙarfin hali nayi na dagota sai ji nayi gaba ɗaya jikin ta ya saki, wata irin ƙara na saki me firgitarwa sai yanzu hankalina ya kai kusa da ita, babu mijinta babu dalilin sa a hankali na miƙe zuwa jikin bayinta, motsi naji a ciki alamar akwai mutun a ciki, cikin kuka nace" ka taimaka mana salisu??..."

Wajenta na koma ga mamakina sai gashi ya fito ya sha dogowar Riga me dogon hannu, har da hula a cikin wannan daren, kare mai kallo nayi ko zan ga wata alama amma babu komai a tare dashi, sai ma ɓata fuska da yayi lokacin da ya gani a kusa da Ummata...

" Ke uban me ya shigo dake a cikin wannan dare?..."

Ajiye mamaki na nayi a gefe cikin kuka nace" Ummana bata motsi, dube jikina wannan mutumin ne ya sake shigo min yau, dan Allah ka taimaka min Umma ta tashi tazo muje!..."

Kallon mahaukaciya yai min kana yazo kusa dani murya a shaƙe yace" muje na gani!..."

ALLAH sarki ni taimako nake nema cikin sauri na miƙi Ina gaba yana bina a baya, a haka har mukazo ɗakin cike da tsoro na tsaya ban juyo ba nace" ka shiga a ciki na rufe shi!..."

Shiru naji bai amsani ba, juyawar da zanyi sai naga babu shi babu dalilin sa tsananin kaɗuwa na kaɗu, na firgice Ina cikin wannan halin naji ana dafani ta baya ƙamewa nayi a wajen zuciyata na zullo!...."

Sharda

Comments

Kuyi min hak'uri nayi tafiya ne amma na dawo insha Allah zakuna jina akan lokaci!....

Mrs Abubakar

YA ZANYI farin cikin yata shine burinaWhere stories live. Discover now