_YA ZANYI.?_
_FARIN CIKIN ƳATA SHI NE BURINA_By.
_Usaeenah b. Abubakar_
_(Mrs Abubakar)_wani irin ɓacin raine ya dirar mun ganin yana ƙoƙarin kamoni amma Umma batace komai, kafata nad'a da dukkanin karfina na naushe mai fuska zuciyata na azalzalata, cike da har gowa nace" idan ka kuskura ka tamɓani wallahi sai nayi maka mugun lahani, ko ka manta nan d'in mallakina ne?.." a masifance nake maganar.. saukar marin da naji akan fuskata shi ya dawo dani a daga duniyar zafin rai.. da hannu take nunani itama da alama ranta ya gama baci a k'ausashe najin muryata" wanna shine tarbbiyyar da na baki? shi din a matsayin uba yake a wajenki ina fatan kin fahimta?.." k'asa nayi da kaina hawaye masu zafi suna zubo min a hankali nace" wai yaushe ne zaki fara gane mahimmancin rayuwata akan ta wani? a wancen lokacin ma kuskurenki ya jawo komai! yanzu ma kina so ki sake taffaka wani kuskure bazan tilasta miki akan raayinki ba amma ki sani ko ke sai da amincewata zaki zauna a gidan nan bare wani Kato, d'aki dai na ubana ne haka gidama nawa ne to duk wanda yake son zaman lafiya dani ya bini a hankali, wannan ba Baby dah bace!..." na koma na kwanta zuciyata cike da rashin jin dadin abinda nayi wa uwata, ina kuka k'asa k'asa a cikin raina nake bata hak'uri... Sororo ta tsaya tana dubana gaba d'aya na sauya mata Baby me kawaici da danne zuciya yau itake fad'ar gidantane! lallai kam ana kaita karshe.. Alhaji dai yana dafe da hancin sa dake mai zugi dan sosai ya daku.. gajiya sukayi da tsaiwa zuwa can kuma na nemesu na rasa, sai wata figagiyar yarinyar da ta shigo mun d'akin ta firgitani, na k'wala uban ihu Ina shigewa bargona fad'i nake na shiga uku Umma aljana aljana!!.." Allah sarki da gudu ta shigo d'akin babu ko fargaba gadon ta hawo cike da fargabar abinda zai biyo baya a hankali ta tabani tana fadin menene wai, ki shiga nutsuwarki a ina?.." jin muryar ta zuciyata ta samu salama na leko da kaina a hankali sake hango yar nayi a tsaya da wasu rankwala-rankwalan idanunta tana kallona, aiko na fashe da kuka hani'a ina wallahi nayi mugun gani, rungume ni Umma tayi a jikinta tana tai min tofi gaba d'aya ta rikice itama, a hankali tace" rukky yi gudu kira mun Babanki!.. kamar bazata wuce ba sai kuma ta tafi tanayi tana murgud'a baki, domin tafi kowa sanin me nakewa ihu a ganinta tsananin rainin wayone... Yace" bazai iya taimakon y'ar da ba y'ar mutunci ba, me dukan ubanta!.. maganar ta dake ran Umma amma ba yanda ta iya, tace" Baby ki nutsu mana a ina take?.." zuciyata na bugawa har ga Allah na masifar firgita, da kyar na dago hannuna na nuna mata saitin wajen, kallon rukky tayi sama da k'asa sai kuma ta sakeni tana cewa" ke yanzu rukky ce aljanar nifa na turota tazo ku kwana tare kafin gobe na sa a gyara miki dakinki ta koma chan.." ai tsalle nayi na dire nace wallahi bazan kwana da itaba ta firgitani tun yanzu ina kuma in dare ya raba, kuka na saka wiwi.. Allah sarki uwata hak'ik'a Ummana tana kaunata rarahina tayi cike da so tace" karki damu bazan takuraki ba asubata gari, zata kwana a falo... Da yake yarinyar ba kunya gareta ba sai cewa tayi" sai kace marar gata wallahi nima bazan kwana a faloba, sai dai a mayar dani wajen mome.." ban kula yarinyar ba sai ma hannu Ummana dana riko ina hawaye a hankali nace" ki yafe min Umma tabbas yau na san na bak'anta miki amma ba da niyya nayi ba, dan ALLAH kiyi hak'uri na kasa jurewane gani yana shiri aikata kuskure ba tare da kin tsawatar ba a matsayinki na uwa me adallci...". Na fahimceki Baby abinda nake so dake shine ki ajiye wanna zafin ran da kika dauko a gefe, insha ALLAH komai yazo k'arshe, zan jure komai amma bazan jure k'untata miki ba zan k'asance me yak'i da kuskurena dan ganin ban sake aikatawa ba, hakan yayi Miki?...". Murmushi na saki me sauti ina hawaye na rungumeta itama bayana ta shafa a hankali tace ki kwanta kiyi barci zuwa safi zan kira waya akawo miki taki babyn... Cikin sauri na riketa nace" dan Allah karki min haka! bana so ina ganin ta a kusa dani hakan yana tadda min da hankali da tunanin me zance mata nan ba gaba, ki sani Umma a unguwar nan ba wanda bai san da faruwar lamarin nan ba zanso tayi rayuwarta cikin salama ba tare da tsangwama ba, a can ba wanda ya sani sai mai gadin su da yan aiki, a nan kowa burin shi ya gani ko dan a watsa mun bakar maganar, zan jure wace zaa jefeni da ita amma ba zanso a jefi d'iyar cikina ba zuciyata bazata jureba, ina son zama dake ne shiyasa na barta na biyoki...". Wani Sona da kaunata ne ya sake cika mata zuciya rabon da taji wanna sanyayan kalaman har ta manta, kiss tayi min agoshi game da cewa Allah yayi miki albarka y'ata... Hannun rukky ta kama suka fice, tashi nayi na kulle d'akin game da zuba musu sakatu domin Ina tsoroa kwana da wani a gida d'aya muddin ba maharamine bane, musamma wanna bak'in mutumin da bai da kyan kallo... A zuciyata nake fad'i ko me ta gani a oho ita sarki son aure... Wallahi wanna wayar bata da dadin typing ba yanda zaayi na Danna cipes kuyi hak'uri da wannan
YOU ARE READING
YA ZANYI farin cikin yata shine burina
Short Storylabari ne me tab'a zuciya hadi da cakwakiya me zafi