_YA ZANYI_
_(FARIN CIKIN ƳATA SHINE BURINA)_BY.
_HUSAEENA B. ABUBAKAR_
*(MRS ABUBAKAR)*
💫 *DA BAZAR MU WRITER'S ASSOCIATION* 💫
*We _are here to make you happy, smile, educate and to realized that we are the best among all...DA BAZAR MU MUKE TUN'KAHO.*
🅿4⃣
Sauddat Umar tun farkon rayuwar ta bata taso ta wayi iyayin ta ba, tana da shekara biyu Allah ya amshi ran su, a wajen kakar ta Hajiya Balaraba ta taso, ta samu gata da tarbiya ma na garciya, yarinya ce me nutsuwa da hankali tayi karatun boko tun da matakin farko har zuwa ƙarshe, cikin amincin Allah ta samu aikin bank wani matashin saurayi yayi mata hanya, layin su daya ko wajen aiki tare suke zuwa, a hankali shaƙuwa me ƙarfi ta shiga tsakanin su, da yake shi babba ne a bank din suna bala'in samu a harkar aikin nasu, sun gama fahimtar junan su sosai, gashi tsakanin hajiya da mahaifiyar sa akwai fahimta sosai...
Sai da sukayi shekaru shida suna soyayya me tsafta da nagarta, a lokaci Sauddat ta zama wata ƙ'aramar Hajiya, ta tara kuɗi sosai tana kuma wadata kanta da kakar ta, shima Jabeer ya sakar mata kuɗi kamar hauka wani lokaci har ƙin amsa take, ga kaya na alfarma da yake siyo mata...
Ana ce son gama jini Sauddat tana ma Jabeer San mutuwa yayin da shi yake mata wata irin ƙauna me wace tafi da nutsuwar shi, ganin halin da suke ciki ya saka iyayen su amincewa a cikin wata biyu akayi bikin su anyi shagali kamar bazaa daina ba, bikine na masu kudi ko wanne yana nuna iyakar farin cikin sa ne....
Bayan auren su da watani biyu ana kan cin amarci suka koma bakin aiki domin hutun da suka dauka ya kare, sosai suke ƙ'aunar junan su a wajen aiki ma ba wanda bai san da wannan soyayyar taso ba...
Bayan shekara biyu Allah ya albarkaci su da samu karuwa, murna a wajen wannan family din bazata faɗu ba, hutu suka dauka ba dan komai ba sai dan kula da abinda ke cikin ta, sam cikin baizo mata da laulayi ba sai ma kara mata kuzari da yayi wajen kula da abun ƙ'aunar ta, shima ya sake zage damtse wajen basu kulawa ita da abinda ke cikin ta, da hutun su ya kare suka koma bakin aiki, kwanci tashi a sarar me rai sai gashi Sauddat tazo tashi ma da kyar take yin sa, ciki ya girma kullum suna saka ran haihuwar ta, sai da ciki yayi wata goma cif sannan Allah ya kawo ranar fitowar sa, burin su shine su haifi mace, sai gashi su samu abinda suke bege murna da farin ciki bai faɗuwa a waje su, nan aka dauki son duniya aka ɗaurawa yarinyar wace taci sunan maman Jabeer Asiya, ta ko ina take samun gata anyi masifar shagwaɓa ta, duk girman abu in tace shi take so bata ake, a haka take rayuwa a sangarce amma tana da bala'in nutsuwa ga tarbiya, bata da raini ko kadan tana shekara goma sha biyar tayi saukar alƙur'ani me girma, duk wannan sangarcin da take tsakanin ta ne da iyayen ta bata hawa jikin kowa d'aga na mahaifin ta sai na Umman ta, gaba ɗaya duk wata ƙaunar da suke ma juna sai suka mayar kan ta, Abban ta mutune me kishi tsiya da yake wajen aikin su daya bashi da yanda zaiyi dole yake jurewa tund matar tasa akwai kiyayewa duk da macece ita me farin jini jama'a ba mata da maza...
Dama haka rayuwa take kai kana rayuwar ka tsakani da Allah ba tare da wani ko wata ya tsulo maka ido ba sai kaga wani kullum burin shi shine yaga bayan ka, to haka ce ta ke faruwa da su Sauddat arzikin su bai rufe musu ido ba amma duk da haka basu tsira ba...
Asiya tayiwa iyayen ta farin sani ko saɓani suka samu tana fahimta ta hanyoyi da dama, domin tana da mutuƙar wayo kuma tana bala'in ƙaunar su kamar ranta...
Akwai Babban abokin Abban ta wanda wajen aikin su ɗaya, suna abota ne tsakani da Allah sun shaƙu sosai babu wanda bai san halin da dan uwan shi yake ciki ba, shima akwai abokiyar aikin su wace a ko wanne lokaci take nuna mai ƙauna, da yake yana da mata har biyu sai yaƙi amince mata Salisu kenan me ƙyan hali...
Yau kowa yaci kwalliya kamar me cike da soyayyar junan su suke hira, me aikin suce ta fito cikin shirin tace" Hajiya na kamala komai zan iya tafiya?..."
Cikin murmushi Sauddat ta dube ta tace" eh zaki iya tafiya, amma kin haɗawa baby kayan ta wanda na ware?.."
" Eh Hajiya komai yana shirye!.."
" Good .." daga haka bata sake cewa komai ta mayar da hankalin ta kan, Baby dake cinyar ta rabin jikin ta na kan cinyar Abban ta, hannun ta akan ƙaramar wayar ta...
Musalin uku da rabi na dare Jabeer na tsaye akan sallaya yana sallah kamar yanda ya saba duk daren duniya, yana sallame wa ya ji kamar motsi a bayan window din ɗ'akin su, cikin sauri ya miƙ'e bakin shi ɗauke da sallati, leƙawa yayi amma abin mamaki sai yaji shiru gaba ɗaya sai yaji zuciyar sa taki aminta cikin sauri ya tashi Sauddat haɗin da cewa" tashi mana ni fa ji nake kamar an shigo mana!.."
Cikin sauri ta watseke tana faɗ'i " an shigo mana koma? waye zai shigo mana a cikin wannan daren? .." ta faɗ'a tana duba a gogon dake manne jikin bango ɗakin...
" Allah dai ya tsare tashi ki dubo min Baby!.."
Bata ce komai ila miƙewa da tayi zata wuce, cikin sauri ya dawo da ita zuwa jikin sa kamar me mata bankwa murya kasa kasa yace" ki k'asance me haƙuri a duk halin da zaki tsinci kanki, ina mutuƙar ƙaunar ki farin ciki na!..."
Murmushi tayi itama ta shafa gashin kan sa tace" Ina alfhari da kai mijina, kullum sai ka gaya min wannan kalamar insha Allah zan ƙasance yanda kake fata!.."
" Baza kiyi kuka ba?.."
" Kamar ya!.."
" Ki amsa min kawai eh ko AA?.."
" Muddin ina tare da kai bana jin akwai ranar da zanyi kuka inda bana farin ciki ba, Ina ƙaunar ka Abban Baby!.."
" Ina mutuwar sonki maman Baby! Allah ya bani ikon kulawa daku.." ya manna mata kissing a goshi cikin farin ciki ta taho ɗaki na...
Sake gilmawa yaga anyi da gudu, cikin sauri ya juya da ƙarfi kuma yace" waye a nan?..."
Gani tayi kamar an gifta ta cak ta tsaya da tafiya, zuciyar ta na bugawa da ƙarfi, hanyar da zata sadata da makunar haske ta nufa...
Ƙ'asa ƙasa nake rere kuka na domin bakon lamarin da ya firgita ne, mummana mafarki nayi zaa sace ni ina farkawa kuma sai gashi naga ana gilmani, cikin sauri na gudu ƙarƙashin gadona sabida dubu bana ko ganin tafin hannu na, tsoro ya gama cika min zuciya...
Comments
And
Shared
Please
Mrs Abubakar ce

YOU ARE READING
YA ZANYI farin cikin yata shine burina
Short Storylabari ne me tab'a zuciya hadi da cakwakiya me zafi