_YA ZANYI.?_
_FARIN CIKIN ƳATA SHI NE BURINA_By.
_Usaeenah b. Abubakar_
_(Mrs Abubakar)_Tsakiyar falon muka dawo zuciyoyin mu cike da kewar juna, Ina kwance akan cinyarta tana shafa kaina tace" rashin ji a kusa dani babbar illace Baby, nayi jinya har na fitar da ran zan tashi, nayi jiran na zuba ido ko zaku nemeni amma shiru, tabbas na hau dokin zuciya marar tushe na san ban kyauta miki dan Allah ki yafe min a karo na biyu?.."
Murmushi nayi cike da k'aunar ta jin har ciwo tayi akaina, "karki wani damu Umma har yanzu ke ba lefi bace a wajena duk abinda kikayi dai-dai ne Amma alfarma d'aya nake nema a wajenki ki rabu da wanna bak'in mutumin wallahi har zuciyata bai kwanta min ba, sam bana k'aunar sa.."
Gaban ta ne ya fad'i tuna irin kalaman da nayi aka salisu sai gashi akan Alhaji Najeebu, na sake maimata mata, cikin sanyin jiki tace'" Najeebu ba kamar salisu bane shi mutunne me nagarta da mutunci ba ruwan shi da sakawa kowa ido, ga iyali yana dashi mata da maza kuma shi matar sa d'aya ina ji a jikina bazai aikata wani mummanan abu ba, dan ALLAH ki sawa zuciyarki salama, insha ALLAH ba abinda zai faru..
Shiru nayi bance mata komai a zuciyata ina tunanin san aure irin nata, taya zan bullo mata nee...
" KE KE Saude wanne irin iskacine naga kin cire min kayana daga d'akina ki saka na mace a ciki? wanne irin haukane yake damunki ne ke kenan kullum maganar mutun biyu yau kiyi ta mamaci da anjima ki dauko ta wata Baby, dan wulakacin har da mayar da picture dinshi da nasaka a ajiye shi d'akin shirgi ki ma rasa inda zaki ajiye sai cikin d'akina?.." cike da masifa yake maganar kamar zai kai mata duka...
Cikin mamaki take kallon shi duk da yaci ace ta saba da cin mutuncin sa, " kaya kuma Najeebu?.."
"Eh zan miki karyane!.."
Wani irin bak'in cikine ya cika mun zuciya ganin yanda yake nuna ma uwa hannu kamar wani ubanta, na mike nima a hankali nace" Umma zanje na kwanta sai da safe!.."
" Baby ki tafi d'aki na gobe zan saka mero ta gyara miki d'akin ki, rukky ma tana Chan.."
" A'A bana so na sake kwana a cikin shi, na zab'i wanda yafi mun ko wanne a cikin gidan karki damu!.." banjira cewarta ba na wuce..
Shiko bakin cikine ya kama shi gani tana magana dani dan ta raina shi ma yana mata magana shine tayi kamar bataji shi ba..
KE Saude ni bana daukar rashin nutsuwa kinji ko! a ina kika zuba min kayana? Sannan kije ki cire mu mamacin da kika maka mun a d'aki, domin bazaa tsoratar dani a banza ba!.."
Najeebu wai me yake damuka ne, uban y'ata ne fa kuma a gabanta ai ka karanta mata ko bazakayi domina ba, maganar Allah baka tab'a b'ata mun rai irin na yau ba, muje na gani ni ban san da wasu kaya ba.."
" Iyee lallai yarinyar nan wuyanki yayi kwari har ni kike kallo kai tsaye kike gayawa magana? karki manta aljanarki na kasan kafata sai kinyi mun biyayya zan d'aga ki shiga, in banyu raayi ba kuma na murk'usheta, wallahi tallahi in baki shiga hankalinki ba zan miki abinda nakewa Sadiya ina d'aga miki kafane kawai sabida rashin lafiyarki, ki kiyayya ranar da zamu had'u dake..."
Kasa tayi da kanta jin yanda ya fara mata ciwo a hankali tace'" kayi hak'uri muje na gani bana son hayaniya please!.." tayi maganar cike da shagwab'a..
Wani irin mugun kallo ya wurga mata, fuskar nan tashi bik'ikirin da ita yace" muje!.." tana gaba yana binta a baya da dirkeken cikin sa...
Bak'in cikin mugun mutumin nan ya hanani barci sai juyi nake akan bed din inajin sanda suka taho nayi kamar ina barci...
Galala ya saki katon bakin shi, had'i da kama hab'a yace" yau naji ikon ALLAH kinga wannan abar akan bed dinna! Aiko wallahi sai kin sako Dan ubanki!.." ya fad'a da k'arfi cikin sauri ya hayo gadon yana shirin jefani k'asa...

YOU ARE READING
YA ZANYI farin cikin yata shine burina
Short Storylabari ne me tab'a zuciya hadi da cakwakiya me zafi