Chapter 11

13 0 0
                                    

_YA ZANYI.?_
_FARIN CIKIN ƳATA SHI NE BURINA_

By.

_Usaeenah b. Abubakar_
_(Mrs Abubakar)_

🅿1️⃣1️⃣

A hankali ta dubi fuskata cike da soyayya ta ce" fushi kike dani baby ?,  dama akwai ranar da zaki iya guje mini ? yanzu akan wani dalili daban zaki iya mancewa da k'aunar dake tsakanin mun? ni ban isa dake ba ko baby ? kin san halin da na shiga a lokacin da kika tafi  ? kin san irin tashin hankalin da na fuskanta duk a ta dalilinki?  wannan shine sakamako na baby ?..."
Cikin raunin murya ta ida zancen...

Jikina yayi sanyi, tausayin mahaifiyata ya sake ratsani, kallo d'aya nayi mata na hangi ramar dake tare daita, na sausauta muryata ta yanda zatayi saurin saukowa, gwiwwoyina a k'asa nace" ki gafarce ni Ummana!!! ba dan halina ba dan girman zatti ? nafi kowa sanin lefin da nayi miki babbane kuma zaiyi wuya ki yafeni cikin sauki haka, ina me sake rok'on gafarki a karo na farko a rayuwata da na aikata miki lefi mafi muni dan Allah kiyi hak'uri ki kuma yafe min ?....""
Har cikin zuciyata nake jin ban kyauta mata ba...

Tun d'aga ranar ba abin da ya sake shiga tsakanina da mahaifiya ta, ba wai chanzawa tayi ba a'a soyayyar su ma sai abin da yaci gaba, na cire su a raina ba abin da nake sai karatuna in ranar hutu tazo na tafi gidan Hajiya babba...

Bayan wata shida kwance nake domin yanzu zaman gida nake  na gama karatuna tsaf ina jiran fitar sakamako, cikin sallama ta shigo d'akin  da faraa a fuskarta ta ce" Mamanmu bakiyi barci bane ?..."

Dariya ta bani jin wani saban suna da ta saka min, na mik'e zaune akan lintsimeman bed dinna, hannuna ta kama cikin nutsuwa take cewa" kina jina baby dama zan gaya miki ne  *sati me zuwa insha Allah zaki samu new father gobe ki tashi da wuri zamuje gyaran jiki!, kinji yarinyar Umma!..."*.
ta fad'a idanunta cikin nawa..

Sosai naji babu dadi a raina, na ma rasa me nake ji akan Umman tawa, ido kawai na zuba mata har ta fice a d'akin, a hankali na koma na kwanta take rayuwar su da ABBA na  ya fad'o min a rai, najima a cikin yanayi marar dadi d'aga bisani nayi mata addu'a had'i da fatan alhairi  gaba na yana tsanan ta faduwa...

Kamar yanda tace haka ne ya k'asance washe gari da sasafe tazo daki na a gaba ta sakani har sai da tatabbatar na shirya kana muka fice...

Tun daga ranar sauran walwata ya dauke rashin kulawa ya karu akan na baya, wani lokacin in Alhaji salisu ya kirata sai ta ce na dauka nazo na saka mata a k'unne, ido nake zuba mata babu ko kifftawa har sata zungureni kana nake dauka nazo na tsaya har ta gama, in naga  tana dariya kawai dan sunawaya dashi ji nake kamar na shek'e kaina, sosai nake kishin Ummata tsantsar tsanar Salisu na sake narkewa a cikin zuciyata ko me sunan shi bana k'aunar naji ance bare shi kan shi...

Yau ta kama alhamsi tun farar safiya muka fara ba'kin kawayen ta, sunzo sun cika gida hayaniyar su ce ta tasheni cike da bakin rai na fito kai tsaye madafa na nufa can kasan kanta na shige bayan na d'aura ruwan tea wani kukane yazo min daban san dalilin zuwan shi ba, abin da nasani shine yau ina cikin bakin ciki marar musaltuwa, a dadafe na sha sannan na fice na koma dakina, ta gaban kawayen ta na wuce ba wanda na kula kamar yanda suma ba wanda yayi gigin kulani...

A takaice da ranar banga idanun Ummaba sai can dare naji motsin ta, lamo nayi akan bed din tamkar ina barci zama tayi a kusa dani tana me shafa min gashin kaina wanda babu hula akai, cikin sanyi muryarta tace" Allah yayi miki albarka baby na, tun safe ban sakaki a idona ba gaba d'aya ji nake kamar bani da lafiya , ya Allah ka bani ikon kula da yarinyata ya ALLAH kasa ta fahim ci halin da nake ciki, Allah yasa tayiwa saban mahaifin ta biyayya kamar yanda take min..." Addu'a tayi min kana taja min kofa..

YA ZANYI farin cikin yata shine burinaDonde viven las historias. Descúbrelo ahora