_YA ZANYI_
_farin cikin ƴata shine buri na_By.
_Husaeena b Abubakar_
_(Mrs Abubakar)_🅿️1️⃣8️⃣
_Masoya na ku kara haƙuri dan Allahu_
A cikin su ba wanda ya tambayi inda yarinyar take burin su bai wuce su ji lafiyata ba...
Basu bada damar ganina ba sai washe gari da safe, a hankali na fara bude kumburarun idanuna, cike da jin nauyin jikina na ware su akan Umma dake saitin fuskata, tamkar me jirana..
Murmushi ta sakar mun da sauri na lumshe idanuna ina tuno abinda ya kawoni asibiti, cikin sauri na daura hannuna bisa cikina, zafin da naji ne yasa nayi sauri daukewa Ina mayar da idona...
Tausayina ne ya kamata a hankali ta shafa kaina cikin sanyin murya tace'" sannu Baby Allah ya baki lafiya.."
Ta gefen ido na dube ta dah har bazanyi magana ba sai kuma nace" ina ciki na?.."
A yanzu kam da sauri ta dube ni, cike da mamaki tace'" ana samu baby girl tana dakin hutu itama!.." d'aga haka ta mike d'aga inda nake...
Allah cikin ikon sa satina biyu a kwance asibiti, amma har yau su Umma basu bani yata ba, na zuba ido nayi shiru nayi alkunyar har na gaji, yau kam tunda ba inda bana iya zuwa duk tsiya sai na gano abata, gaba d'aya na kosa naga abunda na haifa, ba irin tunanin da banyi ba gashi nonowa na sai ciwo suke mun..
Bayan ya gama dubani a hankali nace" doctor ina son gani y'ata?.."
Murmushi yayi mun a hankali yace" kina nufin har yanzu baki ga yarta ki ba? "..
A k'age nace" eh !.."
Mamaki karara a fuskar shi amma sai cewa yayi ki godewa Allah da ya baki iyaye na gari, tabbas ke din yar gatace kuma abar a jinjinawa iyayenki, suna matuk'ar kaunarki ..." d'aga haka ya fice..
Ni gaba d'aya ban fahimci inda ya dosa ba, tashi nayi nima na biyo bayan sa, a zaune na tarar dasu ko wace ta zuba ta gume, Kaka na duba ganin farko na gane yarinyartace a hannun ta, domin ta sakata a cikin hijab, wajenta na nufa zuciyata na zullo, Allah Allah nake na isa..
Ina zuwa na zauna a kusa da ita, banyi shakar kowa ba ko fargaba nace" Sannun ku Hajiya, Kaka kawota?.."
fad'a ina mika mata hannuna..Gaba d'aya su kallona suke zuciyar su cike da kad'uwa, gani kallon da suke min bana kare bane yasa na daga hijabin Kaka, ban bari ta miko min itaba na d'auke y'ata, wani irin farin ciki na ratsa min ilahirin jikina da jijiyata, bude fuskar baby nayi ban san lokacin da na furta "tubarkalah" na shagaltu da kallonta, wata mahaukaciyar soyayya ta na fizgata, a hankali na rungumeta tsam a jikina, cike da k'aunar y'ata nace" Allah ya albarkaci rayuwarki yata, Allah yasa kinzo a sa'a, Allah ya kare mun ke da karewar sa, Allah ya hadaki da kyakykyawar kaddara, Allah ya tsare munke a duk inda kike y'ata, Allah ya bani ikon tarbiyantar dake bisa tafarkin isalam, ina sonki sosai abar kaunata!..." Wasu munafikan hawaye na bin kuncina...
Tunda na fara sunbatu Umma ta bar wajen hata Kaka k'asa jurewa tayi, Hajiya ce kawai a zaune tana bina da amin...
A tunanin sunje su dawo ne, ina zaune da yarinyata a hannu sai kallonta nake, Hajiya tace'" in kin gama kawota ki koma, zuwa ana jima ma zaa bamu sallama..
Murmushi nayi mata kana nace" Hajiya ina jin sonta sosai a raina, me yasa kuka hanamu ganawa sai yau?.."
Gefe ta kalla kana tace'" haka Allah ya kaddarto, sai yau din zaku gana.."
" Wa yake bata nono?..."
Dan shiru tayi zuwa can kuma tace'" Madara ake bata..." " meyasa ni bazan bata?.." "wanna kuma aikin uwarki ne, acewarta har yanzu kina nan a budurwarki! tunda ba haihuwa kikayi ba shayarwa ma bazakiyi ba.."" D'aga yau zan cigaba da kula da y'ata, kuma zan shayar da ita kamar yanda akeyiwa ko wanne d'a, maganar budurci kuma halan ta manta abinda ya faru kenan? A yanzu bani da wani sauran tatali kuma, a barni na raini yarinyata cike da k'auna irin yanda ko wace uwa takewa Ya ya ta, dan Allah Hajiya ku fahimceni!.." Ina kaiwa nan na shige ciki da y'ata a hannu...
Ban jira zuwa kowa ba na mik'a mata nono, Allah sarki baiwar Allah ta kama ji kuke tsoti-tsoti, kamar ta shekara bata ciba, tausayin game da k'auna me k'arfi ya sake ratsani...
Kiyi hak'uri Dan Allah bana jin Dadi kwanan biyu nan
KAMU SEDANG MEMBACA
YA ZANYI farin cikin yata shine burina
Cerita Pendeklabari ne me tab'a zuciya hadi da cakwakiya me zafi