Chapter 8

9 0 0
                                    

_YA ZANYI!!..?_
_FARIN CIKIN ƳATA SHI NE BURINA!_

*BY*

_*USAEENA B. ABUBAKAR*_

*(MRS ABUBAKAR CE)*

🅿8⃣

Da sauri ya sakar mun hannu domin babban mutune zaiyi jika dani, a ƴan sanda da suka shigo ba wanda ya kula dani har na tsogona a gaban shi, kallon shi nake cike da rashin fahimta zuciyata ta gama bushewa bani da burin da ya wuce na d'auki fansa akan shi, facemaks din fuskar shi na cire da wani irin mugun sauri na bude idanuna waje a hankali nace" kai nee! ?..."

Shi dai kallo na kawai yake zufa na keto mai ta ko ina, tsira mai ido nayi sosai tabbas duk yanda akayi na tab'a ganin shi a duniya ta, to amma a ina? amasar da na gagara bawa kaina kenan  juyawa nayi naga babu kowa d'aga gani sai shi cikin wani mugun sauri na fincike wukar dake wuyan sa, bayan na rufe hannu, da sauri ya dafe wajen da hannu shi idanun sa na sama da kasa, cikin azabar radadi yake kallo na a hankali yace" ko da bamu samu na nasara  a yanzu ba to tabbas zamu samu a gaba, ki sa a ranki komai daran dad'awa mahaifina bazai barki ba! d'aga haka yace ga garin ku nan bayan bak'ar wuyar da ya sha!...

Wani irin kuka na saki zuciyata na radadi shigowa su sakeyi shima aka fita dashi, nima bin bayan su nayi inda aka nufi asibiti damu baki d'aya, taimakon gagawa aka shiga bawa iyaye ne...

Bayan awa biyu Sauddat ta farfado da yake ita tsabar buguwace Abba na kuwa sai da yayi kwana biyu ana jinyar shi bulet biyu aka cire mai a kafa, sai dinki da akayi masa a gadon baya, gashi ya bugu sosai a kai a kwana na uku ne ya farfado bakin shi dauke da sallati munyi murna marar musaltuwa a sailin , lokaci su Hajiya babba da Hajiyar Sauddat su iso, murnar mu ta sake ninkanta baya, akal sai da yayi sati biyu akwance sannan ya fara magana, abokan shi sunyi mana k'ok'ari sosai musamma aminshi kullum sai yazo duba shi har iyalen shi ya kawo,  sai nan dani yake tamkar mahaifina...

A yau ta kama jumma'atu babbar rana, musalin karfe 1:30 jikin ABBA ya rikice sosai har baya gane wanda ke kan shi, kuma lokacin duk muna tare dashi, mun shiga tashin hankali kware da gaske likitoci suka shiga bashi taimakon gagawa da yake Allah yayi wannan karan bazaa tashi ba, ko minting ashirin baiyi ba yace ga garin ku nan, munga tashin hankali na suma har ban san iyaka ba, Umma na kuwa tunda tayi dogowar suma baa samu kanta ba har ranar uku babu wanda ya rai da zata tashi...

Fadar irin tashin hankali da muka shiga baki bazai iya furta shi ba, a duniya duk wanda ya rasa mahaifi yayi kuka, domin kayi rashin babban jigone a rayuwar ka,   mun shiga tsaka me wuya gashi abin bakin ciki har yanzu baa san wanda ya aikata mana wannan mumman aikin ba, labari marar dadi ma sai cewa sukayi wai an nemi gawar Yan fashin a rasa kafin ayi bincike...

Tunda d'aga lokacin walwata ta d'auke haka mahaifiya ta, kullum muna zaune ne cikin jimami babu ranar da baza muyi bakin ciki ba, kullum da kunci  muke wuni, Hajiyace ta dawo wajen mu da zama har Umma ta fita a takaba...

Na koma makaranta inda ita ma ta koma bakin aikin ta, duk da da farko taki ne sai da aminni Abba ya sa baki sannan ta koma, Hajiya ta koma gidan ta gida uku gareni a yanzu duk da bamu da wata ta zara me yawa, Hajiya babba ta bani d'aki guda a gidan ta, duk asabar da lahadi a can nake kwana, hajiyan Sauddat kuma wuni kawai nake in Umma ta dawo d'aga aiki ta biyo mu wuce gida, ina samu gata fiye ma dana baya matsala ta daya yanzu gaba d'aya haleyata sun sauya, bana shakar na gaya maka duk wani abu da zaizo baki na, bana wasa da kowa kullum ni kad'ai nake rayuwa a d'aki na, ko Umma bana sakarwa fuska yanzu, ina bala'in sonta kamar me amma ina jin wani irin yanayi wanda na gaza fahimtar shi, bana son aikin da take zuwa a ganina ai mata da maza ne kuma zaana gane min uwata, in na tuna yanda suke da ABBA na ranar wuni nake kuka...

Bayan shekara uku komai ya gama sauya min girma yazo min saban halina ya zamewa kowa jiki, ni kaina na saba karatuna kawai na saka a gaba yanzu,  gidan hajiyan ma na daina kwana sai da ita tazo, kwantsam na dawo d'aga makaranta yau na sake tarar da Alhaji salisu aminin Abbana ba wannan ne karo na farko ba dana tab'a ganin shi yanzu ba, amma haka kawai naji sam ban yarda dashi ba, a wulakace na dube shi na wuce abu na ko gaishe shi banyi ba...

To abinda ban sani ba soyayya suke da Umma na har magana ta kai gaban magaban ta, kullum yanzu shi yake ajiyata in suka dawo daga aiki tunda waje guda suke yanzu, itace take haye matsayin ABBA nata matsayi kuma aka bawa sakatariyar shi..

Tana zaune a falo na shigo gaba d'aya jikina a mace yake, a sanyaye nayi sallama har zan wuce sai kuma na dawo da baya, nace" barka da hutawa sweet Umma!.."

Murmushi tayi min cike da jin dadi hannu ta bude mun alamar nazo ba musu naje jikin ta na kwanta, cikin raina sosai nake yabawa k'ok'arin ta ganin ta sanyani a farin ciki,  a hankali na dube ta murya cike da shagwaba nace" Umma! ina so zanyi magana dake Allah yasa bazata bata miki rai
ba!.."

A goshi na ta manna min 😘 hadi da cewa" baki da matsala yata ki fad'i abinda ke ranki muddin ina raye zanyi miki shi, yarinyar Abban ta amma yanzu kije kiyi wanka in kika rage kayan jikin ki sai kizo muyi maganar..."

"To."
nace zuciya ta fari kwal...

Sai da nayi komai na gama a nutse da kan tazo daki na, yau ban nuna mata komai ba, har ta zauna a hankali na matso gaban ta, cikin wata murya da bata san ni dashi ba nace" Umma!! lokaci da Abba yake raye kinyi mishi alkawari duk wuya duk rintsi bazai bari a wulakantani ba ko ba haka? kice zaki kasanace me kula mai da abinda yafi so a duniya, kin san menene abinda yafi so a duniya?.."

Na fad'a Ina tsireta da ido, murmushi tayi min tana k'ok'arin boye damuwar ta tace" min kware da gaske mahaifinki ba abinda yafi so a duniya sama dake, kuma nayi mishi alkawarin zan kula dake iyakar iyawa ta, menene ya kawo wannan maganar yanzu?.."

Hawaye suka wanke min kunci na, cikin muryar kuka nace" a'a Umma bani bace, duk duniya d'aga Hajiya babba sai ke kune abinda yafi kauna a rayuwar sa, sai ni da aka sameni d'aga baya, Abba na yana miki san so yana miki soyayyar da har ki koma ga mahalinci mu bazaki tab'a samun kalar ta ba, duk wanda zaice yana sonki bayan shine, nayi imani da Allah da yana raye bazaki sauya min kamar yanda kika sauya min yanzu ba, yaushe raban da kizo dakina in dare yayi? yaushe raban da kin tambayi lafiyar ta ko kije makaranta ki dubo ni kamar yanda kike a baya? sam yanzu baki damu dani ba Umma, bakya gane a wani halin nake ciki yanzu ke da kullum burinki shine karki makara a wajen aikin ki, lokacin da mahaifina yana raye sai kin tabbatar da nayi barci kike tafiya d'akin ki, yanzu kuwa fa?  wannan shine alkawarin da kika dauka? me yasa kikayi min shi alkawarin da bazaki iya cikawa ba, yaushe rabon da kinje gidan Hajiya babba? a yanzu ko ni bana fahimtar ki amma salisu yafi kowa sani a wacece ke yanzu! kina...."

" KE!!!..." ta fad'a min a tsawace idanun ta sun furfuta waje, a kausashe tace" min ki kiyayye ni!..."
d'aga haka ta fice a d'akin...

Kwanciya nayi ina kuka raina kamar zai fita, Umma tana d'aya d'aga cikin abinda yasa na sake sauya haleya ta, ta saba min da kwanciya ajikin ta a duk lokacin da nake buk'atar hakan, ta saba min  da rarashi ko da ko ina cikin farin ciki ne,  ko nasihar ta ma ina jin dadin ta har cikin zuciya ta, menene lefina da nayi mata tuni a yanzu? ina mutu'kar buk'atar kulawar ta ba wai ba tayi bane aa yanzu bani kad'ai take bawa kulawa ba, ta sauya min kamar yanda nima na sauya, menene sila?...

D'akin ta ta shige soyayyar Jabeer na sake ruruwa a cikin zuciyar ta, sosai take kuka domin kullum ne sai ta tuna da abin k'aunar ta, baby baza tab'a ganewa ba sabida yawan tunani har hawan jini gare ta yanzu a wanna kananun shekarun nata, ya ake so tayi ne?  tanaso ta koya ko yayine ta manta dashi na wani lokaci amma abu ya faskara, dalilin da yasa zata auri aminin shi kenan ko hakan zai rage mata rarad'i, da me ta ragi baby yanzu ? me ta nema ta rasa ? wace kulawa ce bata samu? ...

Mrs Abubakar

Comments

Duk wace ta karanta tayi shared  please💗

YA ZANYI farin cikin yata shine burinaWhere stories live. Discover now