Chapter 14

14 0 0
                                    

_YA ZANYI.?_
_FARIN CIKIN ƳATA SHI NE BURINA_

By.

_Usaeenah b. Abubakar_
_(Mrs Abubakar)_

🅿1️⃣4️⃣

Cikin matsanancin firgici na juyo a hankali ga mamaki na Umma ce a tsaye fuskar ta babu annuri, a hankali take bina da kallo tashin hankaline ya baiyyana karara akan fuskar ta bakin ta har rawa yake wajen tambaya ta,  " me yasa meki baby ?.."

Sai a lokaci wani irin kuka me cin rai yazo min, na dake nima ina mata kallon mamaki ban amsata ba ila tambaya da na watsa mata, " dama idanun ki biyu???..."

Shareni tayi game da cewa" ki amsa mun tambaya ta me yake faruwa dake ne?.."

Fizgi hannu na ina jin wani irin haushi a raina, kafin ta sake magana na shige dakina, a matuk'ar tsorace sai da na lik'a ko ina sannan na dawo bakin gadona na shiga rere kuka gwanin ban tausayi...

Washe gari da sasafe na kwashe kayana tas na wuce gidan Hajiya babba,ko sallama banyi wa Umma ba domin itama banga kyar ta ba...

Kwana biyu  Umma ta biyu bayana babu bin ba'asi ba komai sai maruka da na amasa a hannunta a gaban Hajiya ta kaf min woning akan duk sanda na sake fita ba tare da izzininta ba to na tafi kenan,  cikin fushi ta juya tai ta tafiyar ta akan innaga dama na biyota..

Hakik'a uwa uwace zan k'asance me mata biyayya ko da zan rasa raina ne ko mayafi ban d'auka ba na bita da gudu, ko kallo na batayi ba har na shiga gidan gaba a mota har makaje gida ba wanda yayi magana...

Wasa² sai da nayi kwana biyu Umma bata kulani ko gaishe ta nayi bata amsawa na shiga damuwa sosai, na bi na takure bana ko k'aunar fitowa falo kullum Ina dakina  da naji motsin ta zan fito na tsaya ko zata kalle ni amma sai naga ta dube gefe...

Motsi naji alamar ta fito cikin sauri nayo waje nima ga mamaki na sai na ganta da akwati karama, gaishe ta nayi kamar ko yaushe shiru babu amsa sai ma gyara mayafi da take, a hankali naje gaban ta durkusawa nayi cikin rawar murya nace" ki gafarce ni Umma wallahi banyi domin na sab'a miki ba, bana samun kwanciyar hankali muddin dare yayi a gidanan, kullum cikin rudani da fargaba nake kwana, tun ana tsorata ni har ya kai ido da ido nake ganin me bibiyata, in nazo wajenki sai kiyi kamar bakya numfashi gashi mijinki baya taimaka min, to YA ZANYI ne Umma? sabida naje gidan hajiya a gaban idanun ta kika manta  ko ni wacece a wajenki kika wawanka mun mari har ban san iyaka ba, wannan bai isa ba yanxu har gaisuwa ta bakya amsawa, anya anyi min adallici kenan ? Umma dan Allah dan girman zatti, domin soyayyarki ga fiyayyen halitta, ba danni ba badan halina ba kiyi hak'uri ki yafe mun, fushinki babbar masiface a gareni naji na amince kiyi min ko da wanne irin hukucine amma banda fushi dani, kiyi hak'uri dan Allah Umma!!.."

Cikin matsanancin kuka nake maganar a hankali ta dube ni zuciyar ta a karye cikin sanyin murya tace" Ni ba fushi nake dake ba kece bakya jin magana ASIYYA, ya isa haka share hawayenki kiyi min alkawari ko da bana cikin gidan nan bazaki sake zuwa ko ina ba muddin bani nace kije ba?.."

Kallon ta nake cike da tausayin kaina nace" insha Allah Umma!...."

Murmushi tayi min kana tace" Ni yanzu Alhaji salisu yana jirana zamuje  garin su kwana biyu kawai zamuyi, mairo zata dawo kwana dake kafin na dawo ki kula da kanki! sannan akwai sakon da na bata zata baki, sai na dawo ko!..." ta fad'a tana murmusawa..

Ji nayi kamar na daura hannu aka amma na jure gudun kar na daurawa kaina wani lefin, Allah ya tsare nace jikina a sanyaye shikenan ni kuma tawa ta kare...

Kamar yanda tace sunyi tafiyar su ita da mijin ta inda ta barni ni kad'ai sai me aikin mu...

Gaba d'aya jina nake a cikin wani saban tashin hankalin, ko da dare yayi in shiga dakina nayi sai cewa nayi mero tazo muje d'akin ta, bata musa min ba sosai nayi addu'a kafin na kwanta lafiya kalau mukayi barci ranar har makara nayi...

YA ZANYI farin cikin yata shine burinaWhere stories live. Discover now