_YA ZANYI.?_
_FARIN CIKIN ƳATA SHI NE BURINA_By.
_Usaeenah b. Abubakar_
_(Mrs Abubakar)_Sirinyar ajiyar zuciya na sauke a baiyyane nace" kai da y'arka ana maka iko akai. Gyara mata kwanciya nayi ta yanda sosai zan jita a jikina, tana ta barcin ta hankali kwance yayin da ni kuma nake aikin kallonta zuciyata fal kaunar ta, sam bana so abinda zai rabani da ita yanzu, a haka barci b'arawo ya saceni...
Washe gari duk abin buk'ata nayi mata kafin kowa ya fito har na shiryata tsaf wani irin dadi nake ji a raina, sai naji ina ma tana da uba da sai na kaita ta gaidashi kafin ta wuce makaranta ko ma ya kaita da kan shi, wajejen 7:30 Hajiya ta shigo gidan mu hannuta dauke da kayan makarantar Khausar mamaki ne ya kama ta gani yarinya a shirye tsaf, sai ta boye mamakin ta tace" a'a yar gatan Anty har an shiryaki kenan!.."
Itama yarinyar cikin jin dadi take nunawa Hajiya saban kayanta da kayan mak'ulashen dana zuba mata a jikin jaka, sai murna take tana zaro su d'aya bayan d'aya...
Na mik'e jikina a sanyaye ina jin tausayin ta har cikin raina, a kasalance nace" Hajiya kun tashi lafiya! in ba damuwa daga yau zai na kaita makaranta!.."
Shiru tayi tana karantar yanayi na ko me ta gani oho sai cewa tayi" sai dai in kin yarda zaki fara aikin da Aliyu ya nemo miki!.."
" Inda zaki bani y'ata zanje ko ina ne dominta kawai zanyi duk abinda kuke so, nima farin cikin y'ata nake nema yanzu!.."
" Da kyau Asiya haka nake son ji, baki da matsala gaki gata nan inda zakiyi biyayya, sai abu na gaba muddin kina so ki sakance da y'arki tofa sai kinje kin bawa Aliyu hakuri akan rashin d'aar da kika mai, sannan ki fad'a uwarki ta janye maganar sakin da take nema a wajen sa, in kinyi haka to ga yarki nan in kuma bakiyi ba a gobe zan amshi y'ata!.."
Shiru nayi ina nazari zuwa chan nace" to zanyi inda zaa bani y'ata!.."
Murmushi tayi mun kafin ta fice a d'akin, zama nayi ina tunanin mafita me aikin hajiyace ta shigo domin itace zata rakani makaranta danni ban sani ba!.."
Duk wani sharad'i da hajiya ta fad'a na bi, nima ranar monday zan fara zuwa aiki, sababin kayan naje na siyo mana nida khausar hata wayar hannuna sai da na sauyata, takalma yari ba abinda ban siyo ba, naje wajen salon aka gyara mun gashina kumbata idanuna, ba abinda baayi mun duk Ummana ta biya kudin, khausar ma anyi mata dai-dai nata, daka nan muka dawo gida Har gidan Umma ta kawoni domin furnaki komawa gidanta...
Nayi wani irin kyau ga haske da na kara jikina yayi wani luf-luf, gwanin ban sha'awa yarinyata na kallo na tayi dariya da sauri na dubeta ina b'ata fuska nace" dariyar nan fa ta meye?.."
A hankali tazo gabana d'an k'aramin hannunta ta daura akan kuncina a hankali kuma tace" kina da kyau Anty!!!.."
Wani irin dadi ne ya cika mun zuciyata na sakar mata tatausan murmushi nima nace" kema ai kyakykyawace d'iyar momy!.."
Yau ta kama Monday Aliyu da kan shi yazo d'aukata, sai da na gama shirina tsaf sannan na fito gaba d'ayan su mikewa suke suna kallona, wata fitinaniyar dogowar riga na saka me bala'in kyau da tsada ta masifar amsar jikina nayi roling da wani sirin mayafi ga bakin gilashi da ya mamaye mun rabin fuskata, hannu na dauke da laptop dinna sai wayoyina da suke cikin jakata, nayi bala'in had'uwa ni da kaina ina ji a jikina lallai ni din kyakykyawace, sai wani irin kamshi nake me daukar hankali da saukar da nutsuwa, tsinin takalmina kuwa in mutun ya sake na taka shi da shi ba kawo sai yayi targad'e...
" ina kwana Abbana!!."" Na fad'a yanayin da nazo gaban Aliyu, ya sake baki yana kallona cike da mamakin sunan da na danganta shi dani!.."
Su hajiya na gaisar sai kallona suke kamar sunga wawan zama, sirin tsaki na saki na fice a gidan gaba d'aya...
Wata had'ad'iyar mota na gani wanda darajarta ya wuce tunanin me karatu, ina nan tsaye cike da k'osawa Aliyu ya fito su hajiya na mara mai baya, da kanshi ya bude mun gidan baya na kalle shi da murmushi a fuskata, na wuce gidan gaba mazaunin tuk'i ina tada motar, na kalle shi bayan na sauke gilas din motar nace" lokacin da abbana yake rayya wani lokaci ni nake tuk'a su son da yake mun ne ya hannashi bani damar zuwa duk inda nake so, ina so ka zamo Abbana na gaske ina fatan zan samu wannan alfarmanr?.." cikin sanyi murya da karya harshe nayi maganar alamar maganar ta tab'a mun zuciya..
Jikin sa a sanyaye ya shiga baya, yanayi dana fara tuki so Hajiya na daga mana hannu...
Babban kamfani ne muma nufa ba kowa suke dauka aiki ba sai wanda ilimin sa yakai inda ake buk'ata kowa harkar gaban sa yake musamma matan dake ciki, shigowa ta wajen da yanayin takuna shiya jawo hankalin mazan dake wajen guna, gaba d'aya suka mayar da hankalin su ga kallona yayin da ni kuma na zama tamkar makauniya naki bari na kalli kowa bare kuma na san halin da suke ciki, tafiya mukayi me nisa a cikin kamfanin daga baya muka tsaya jikin wani dank'areren office gaskiya ya had'u tun daga kofar kafin ma mu shiga ciki a wasu kujeru muke zaune masu laushi da kamshi, ba muji ba wata yarinya wace a girme na san na girme mata ta fito cikin shigar riga da wani gotsin siket bakin ta cike fal da cigum tana ta cakal-cakal cike da iyayi tana wani yauk'i ta dube mu a walak'ance tace" zaku iya shigowa!.." tana rufe bakin ta ta shige ciki!.."
Aliyu ya dube ni cikin sigar lalashi yace" taso muje!.."
Raina a b'ace na bi bayan sa, ina saka kafata a ciki gabana yayi wata mumunar fad'uwa, da sauri na koma da baya ina ji jikina yana d'aukar rawa...
Mrs abubakar ce

YOU ARE READING
YA ZANYI farin cikin yata shine burina
Short Storylabari ne me tab'a zuciya hadi da cakwakiya me zafi