_YA ZANYI.?_
_FARIN CIKIN ƳATA SHI NE BURINA_By.
_Usaeenah b. Abubakar_
_(Mrs Abubakar)_Muna shiga na shige bayi na dauki lokaci sosai kafin na fito a zaune na same ta tana wasa da hannunta kallo daya nayi mata na dauke kaina, ta matso kusa dani a hankali murya kasa-kasa tace" niko Baby na tambayeki wani abu bazaki ji babu dadi?.."
Da kyar na bude baki na a gajiye nace" ina jinki!.." Cike da zumud'i irin na munafika tace" yauwa dama akan maganar da naji ne akan ki, yanzu kuma da na ganki sai naga kamar bazaki aikata ba da gaske ne a k'ananun shekaru irin naki nan kina da y'a yar shekara uku?.."
Ta fada tana tsira mun idanuWata irin fad'uwar gabace ta kamani a dadafe nace" ke ko waya gaya miki wannan zancen ku da ba a nan kusa kuke ba?.."
Shiru tayi tana tunani me zata ce mun dabarce ta fado mata ta saki murmushi tace" wallahi Abbamu ya gaya mana labarinki abun tausayi Baby, Allah ya saka miki Allah ya toni asirin koma waye, ki cigaba da hakuri kinji yanzu ina y'ar taki?.."
Tsare ta idanu nayi zuciyata na tafasa wato ma mutumin nan a gabanmu yake nuna mana kauna a bayan idanun mu ya ringa gulmar mu, wato har y'ay'an sa ya tara dan tsagwaren munafirci ya gaya musu ni ba me mutunci bace, ba kawa sai ya gane bashi da wayo dole ne ma shima ya kama gaban shi munafiki kawai!
Ajiyar zuciya ta sauke tana satar kallona, ganin irin kallon da nake mata yasa ta mike tsaye bari na d'an zaga nima!.." ta fada tana bin ta bayana ta wuce...
'''ohh Allah na gode maka bata ganoni ba, duk tsiya ai bazata raina mu uwata ba tunda nace abban mu ya fada mun to yanzu in xancen nan ya koma kunne sa ya zanyi? gaba daya maganar ma ni naje da ita gidanmu gashi in mama taji shima cass ne babba, yarinyar kamar taji babu dadi kuma? To ya zanyi yanzu?.."'''
Ita kadai take wannan tunani a hankali kuma ta fito..Ummace ta shigo dakin lokacin da ta fito hannun ta rike da ledai tace" Memma ga wannan ki saka ki cire wannan kayan na jikinki!.." ta fada tana ajiyewa a gefen da nake cikin sanyi ta dube yanayi na tace" ke kuma wani abu ya sameki naga kinyi wani iri?..'
Nayi saurin boye damuwata a hankali nace" a'a ba komai kawai bana jin dadi ne!.."
"Kin tabbatar Baby na!?.'" ta fada cike da kulawa ga soyayyata kwance a kwayar idanunta....
" Yarinya tana samun irin wannan kulawar wace damuwa ce zata dameta? daga gani an shagwabeki da yawa Baby gaskiya ya kamata a tsageta! yanzu fa ita ba yarinya bace tunda itama ta haifa!.." Cewar Memma dake dora hannunta akan kafadata, da sauri na dago kai ina duban Ummana sare itama taji zancen a wani iri amma sai ta dake a hankali tace" ni kullum a yarinya nake kallonta tunda ita kadai gareni bazan tsageta kulawata gareta ba har karshen numfashi na, ko da yara shirin ta haifa!..."
Memmi tayi murmushi tace" haka ne Umma Allah yakara muku lafiya ku dai!.."
Jikin Umma a sanyaye ta fice a dakin zuciyarta cike da tunanin ya akayi suka sani? ko da yake zancen duniya ai baya boya ko dai Aliyu ya fada musu anyya bazayi haka ba!.." Ita kadai take wannan tambaye-tambaye a ranta..
To Memma irin mutanan ne masu shegen tambaya da surutu, ga fadi baa tambayeka ba duk abinda ta gani sai ta tambaya, ba wai dan basu dashi bane aa kawai shirune bazaayi ba, kwanan mu biyu da ita amma gaba daya ta fice mun a raina, ga wani tsanar abbansu data saka min rai duk abinda zatace sai tace shi ya gaya musu, ni kam abun yana bani haushi...
Yau zata wuce an had'a mata sha tara ta arziki sai murna take tana godiya, ta juyo wajena tana yashe mun baki a hankali tace" to Baby sarkin muskilanci ni zan tafi sai kiyi da bango! kuma ina nan dawowa dole ne ki kaini naga y'arki!.."
Da ido kawai na bita na ma kasa magana, Ummace tace" in dai Khausar kike son gani har gida zan sa a kawo miki ita!.." Dariya tayi tana fadi" da naji dadi wallahi, domin ina son yara amma maman mu tak'i sake haifo mana, dan Allah Umma ke ki haifo mana ko a bamu Khausar din?.."
Wani mugun kallo nake aika mata zuciyata na tafasa jin wai abata Khausar a zafafe nace" Khausar din ai ba sweet bace da zaa bada ita kamar ruwan fanpo, kiyi addu'a kawai Maman naki ta haifo muku taku!.." Ummanace kawai ta fahimci a yanda na bada amsar amma ita da ba sani na tayi sosai ba ta dauka a haka nake magana, tunda babu hargowa a cikin maganar sai zallar nutsuwa, kafin ta bani amsa nayi cikin gida abu na...
Sallama sukayi da Umma ta wuce ji take kamar kar ta tafi gidan yayi mata dadi, abinda ta fahimta su bama su surutu bane hasalima in ka dame su sai su kama barci, amma akwai soyayya me karfi a tsakani su gasu kyakykyawa tubarkala, a fili tace" zan so naga Khausar din domin daka gani zatayi kama da Maman ta..."
Zama tayi akan kujera tana sauke ajiyar zuciya gaba daya Memma ciwon kaice, gata babba amma sam bata abun manya girman jikine kawai da shekaru, zama tayi a kusa dani tana murmushi ban san murmushi na meye ba, na kalleta fuskata a murtike da girta na tambayeta murmushi na meye? itama da kafada ta nuna mun bakomai ba...
A zuciyar Umma kuma tana jin dadi yanda na nuna kulawata ga Khausar yanzu ta sake yarda tsakanin d'a da mahaifi sai Allah!...
To kamar yanda take tunani a ranta nima ji nayi ina son gani y'ata tashi nayi da sauri na hau had'a kayana kadan na dauka nace Umma zanje gidan Hajiya!...
Murmushi taji kana tace" yau yoyewa zakuyi ku barni a gidan ni kadai, shikenan ki gaida su ki biya ki siyawa Khausar abin motsa baki, kice in jina ina nima ina nan zuwa ki gaida su, amma karki manta makarantarki!.."
" insha Allah bazan jimaba zan dawo..."
Da ido ta bina har na fice, cikin sauri ta dauki wayar Kaka ta kira tana dariya zuciyarta cike da farin ciki tace" albushirinki yau jikarki zatazo ganin y'arta ga ta nan har siyayya tayo mata, Allah yasa tana gidan?.."
" Sauddat bana irin wannan wasa dake da gaske kike Asiya ganin Khausar kawai ta taho?.." ta fada cike da zumudi
" Wallahi da gaske nake Kaka!.."
" To ina zuwa!.." Kitt ta kashe wayar..
Hajiya tayi murmushi jin me kaka tace " Allah ya kawo ta, muma lokacin mu ya fara..."
Mrs Abubakar ce
YOU ARE READING
YA ZANYI farin cikin yata shine burina
Short Storylabari ne me tab'a zuciya hadi da cakwakiya me zafi