_YA ZANYI.?_
_FARIN CIKIN ƳATA SHI NE BURINA_By.
_Usaeenah b. Abubakar_
_(Mrs Abubakar)_🅿1️⃣9️⃣
Tun a ranar muka dawo gida, na cigaba da kula da y'ata inda su Kaka suke ganin rashin kunyata arara, zaune muke a falo kowa harkar gaban shi yake, yarinya ta na hannu Hajiya numfashi na ja alamar zanyi magana, gaba d'aya suka zuba mun ido...
Murmushi nayi kana nace" Hajiya ya kamata a yiwa yarinyar hud'uba, domin ina so inji sunnata a bakin kowa na gidan nan..."
Tunda nake rashin kunyar Umma Bata tab'a tanka mun ba sai dai ta bar wajen, yau kam da alama na kureta tashi tayi cak yarinyar ta amso a hannu Hajiya ba wanda yayi mata magana, a cinyata ta dire min ita cike da kunar zuciya, cikin wata murya me kaushi tace'" y'a dai takice ba wani ya haifar miki ita, kamatar da kika hango na a saka mata suna, ke zaki rad'a mata tunda ke kad'ai kika san ubanta, wai shin kin manta ta hanyar da aka sameta ne? haihuwar taki ta tsutsayi haihuwar kaddara, kaddarar ma mummuna ke duk kawai cin da muke miki bai isheni kiyi hankali ba? yau da ace da aure aka haifeta ba wanda zai kaimu farin ciki, duk da haka bata baci ba muyi murnar samun ta domin ko mik'i ko mun so dole ne mu kirata da jinin mu, kin san yanda nake ji a raina in na gana kina wani rawar kai akan yar da baa san asalinta ba? ko dama kin san ubanta ne??? na jima da fahimtar kinayi komai ne domin ki b'ata mun sabida tun asali lefina ne! bance karki nunawa yarki soyayya ba amma karki manta ita din ba komai bace illa kyakykyawar kaddarar ki, ki sa haka a ranki rashin kunyarki ta isheni, in nice bakya son gani zan tafi na bar miki gidan..."
Tunda ta fara maganganun ta zuciyata ke tafasa, sai yanzu ta sake tunatar dani ita din kaddarace a gareni, tabbas haihuwar ta wani shafin kunci ne na daban a rayuwata, amma meye lefina y'atace fa nima, sam banga rashin kunyata ba, hawaye na share karewa yarinyar kallo nayi tuno yanda ubanta ya wulakanta mun rayuwa nayi, irin kuka da magiyar da nayi mashi duk da bana cikin nutsuwata, amma ya nuna zallar rashin imani sa..
tausayi da kuka akan kaddarar ta damuwa akan rayuwata, shiga kunci tare kuma har yanzu suna cikin kuncin sai iyayena, me yasa zan zab'i kuntata musu...
Sake gyara rukun yarinyar nayi da kyau Ina kallonta hawaye na tsiyaya a idanuna, a karo na farko uwar da ta haifeni goranta mun! me zai faru gaba? _ko dai kin santa ubanta ne_ cikin sauri na sausauta rukonta Ina zaro ido waje a masifar firgice...
Da kyar na iya had'a kalaman bakina zuciyata na kuna ina sonta yata so me tsananin, wani bangare na zuciyata ya tsaneta tsana mafi muni, amma nafi son uwata akanta sau dubu, a hankali nace" zan iya hakura dake hak'uri na har abada, domin tun farko ban faro rayuwa dake ba, gaba d'aya k'aunar ki ko wata banyi da farata ba, na tsaneki na tsaneki..."
Nayi wani mugun wurgi da ita zuciyata na kona, cikin tsananin fusata Sauddat ta wanka mun wani mahaukaciya mari, wanda yasa jina da gani na ya dauke na wucin gadi...
Cikin sauri Hajiya ta d'auke ta Allah yaso akan kujera ta fad'a, aiko ta tsanyare da wani gigitacen kuka, kukanta har cikin raina nake jin sa na lumshe idanuna hawaye na shatata, cikin sanyi murna nace" shikenan ko Umma? haka yayi miki? akan soyayyarki zan iya komai muddin bai sab'a musullcin ba, na rabu da ita zaki zauna dani?..."
Galala take kallo na zuciyarta cike da mamaki na! a kaina kike rabu da yar?.."
" Please ki amsa mun zaki zauna dani? kin yarda ban san ubanta ba?..."
sai yanzu Sauddata ta hango katon kuskuren da ta taffaka b'acin rai ya sake dagula komai...
Hajiya tajowani d'aga gaban Sauddat cikin rarashi tace'" amsheta ki b'ata nono ko zatayi shiru!.."
Janye hannu na nayi zuciyata a tsinke nace" dama na kwana biyu tasha, d'aga yau ba zan sake bata nono ba!.."
" ASIYYA kina hauka ne? me yake damun kanki ne? ki amsheta ki b'ata tasha nace!.." cikin karsashi Umma tayi maganar!.."
" Ita din shegiya ce ko ba haka bane? menene lefina dan na nuna mata so? Ni na bawa kai na da zan tsaneta? kince ita mummanar kaddaratace ko? ni kyakykyawar kaddarar na d'auke ta, duk ta yanda Allah ya baka d'a abun so ne ba abun k'i ba, kin san bazaki kaunarce ta ba me yasa kika k'i yarda da batuna na zubar da cikin tun kafin yanzu? wai ya ma ake so nayi da rayuwata ne? ya kike so ki ganni ne, in nayi kunci ki shiga kunci in nayi farin ciki ace nayi rashin kunya, tunda kunci kike son gani naji na amince zan rabu da y'ata amma a rahiri kawai kuma dominki zanyi haka, a zuciyata soyayyar bata tab'a goge mun ba, haka yayi miki?..."
A yanzu kam Sauddat ta gana tsinkewa da batun Aisya cikin karaya hawaye na zuba a idanuta tace" Dan ALLAH na rokoki ki bar zance nan ki amsheta ki b'ata nono, zamuyi magana d'aga baya!.."
" Baza ta sake sha ba!!.."
_lallai na yarda ni ba kowa bace a wajenki idan har da gaske son da kike min na gaskiya ne ki amsheta ki b'ata nono.."_
Cewar Umma gani ina shirin bari wajen, ga kukan yarinyar dake damun su har tsakiyar kai, har a zuciyata nima kukan nata na damuna amma yanzu da Ummana, cikin rawar hannu na amsheta a hannu Hajiya, d'aki na shige da ita ina kuka tamkar zuciyata ta fad'o...
Hajiya ta karewa Sauddat kallo tsaf a hankali tace" ya kamata ki koma gidanki, zamanki a nan ba abinda yake kara mana sai tabarb'arewar lamari, dan ALLAH kiyi nisa damu ko zamu samu sausauci!!.."
" Hajiya! Cikin sauri ta dakatar da ita ta hanyar d'aga mata hannu, kafin ta sake magana tuni ta bar wajen, ta kalli Kaka dake zaune tamkar bata wajen marairaice fuska tayi hawaye na zubo mata, murmushi tayi mata a hankali tace" nima ina buk'atar tafiyarki Sauddat!..."
A wajen ta zauna kuka me k'arfi na kwace mata, gaba daya ta kasa fahimtar komai, menene lefinta ? d'aga fad'ar gaskiya sai kowa ya d'auki fushi da ita, shikenan ita bata da ikon yuwa y'arta fad'a sai magana ta zama babba, shikenan zan tafi in na tafi kuma da kan ku zaku nemeni!.."
Ko da na shiga daki zama nayi a k'asa dirshen ina rizgar kuka, " kaman yanda kika umarceni haka zanyi, zan shayar da ita amma ba batun nuna kauna a zahiri..." rungumeta nayi har cikin zuciyata nake jin sonta...
My Fan's wai Dan Allah a cikin su lefin waye ne? Waye babban me lefi a cikin su....?????
Mrs Abubakar CE
KAMU SEDANG MEMBACA
YA ZANYI farin cikin yata shine burina
Cerita Pendeklabari ne me tab'a zuciya hadi da cakwakiya me zafi