Chapter 21

5 1 0
                                    

_YA ZANYI.?_
_FARIN CIKIN ƳATA SHI NE BURINA_

By.

_Usaeenah b. Abubakar_
_(Mrs Abubakar)_

Kuyi hakuri my friend🥰



Gaba d'aya ana sauya d'akin picture din da nagani a falo shine a jikin bangon d'aki cikin rawar jiki na isa gareshi kallon shi nake cike da tsana tamkar yana kallona, ciki azama na tsigi shi ban jira zuwa da dawowar ba na rafka shi da k'asa, take ya tawarewatsi sai takkadar dake tsakiya, duk wani shirman kayan shi sai da na fitar dasu a d'akin dakina da suka mayar da tara shirgi can na mayar dasu, kayana na duko nima na shirya d'akin tsaf dashi, picture din ABBA na dawo dashi mazaunin shi tarkacen sa da ta mayar can na dawo dasu mahallin su..

Na gama komai har zuwa dare shiru basu shigo ba, abinda aka dafa naci na koshi na koma d'aki na kwanta, agogo na duba 7:43 har yanzu shiru tsaki nayi a raina nace ko ina suka tafi oho, mimik'ewa nayi Ina tunanin kalar rayuwar da zanyi a zamana tare dasu...

Sauddat ta dubi matar Alhaji dake tsaye a harabar gidan tayo mata rakiya, " to maman baby ko? na gode da ziyyara Allah ya bar zumunci ki gaida gida..

Murmushi Sauddat tayi kana tace'" ba komai yanzu ai ana zama daya nice da godeya..

Salama sukayi da matar inda Alhaji ya jima da shiga motar ita kad'ai yake jira, k'aramar yarinyar sa wace a yanzu take hannu Sauddat kuma tana gidan baya a zaune tana kare mu su kallo,  motar ta shigo a zuciyar tana jijina barikin irin na Sadiya, a gaban mijin su ta nuna mata so da k'auna amma in su biyu sai masifar kishi, a baiyyane tace ALLAH sarki baby na!.."

Waigowa yayi ya dubeta da mamaki yace" wace babyn?.. babyi tawa mana!.. ta maida mai da amsa cikin sauri..

"Ohh  ke Sauddat har yanzu bazaki cire yarinyar nan a ranki ba, tunda suma sun manta dake! ki duba da kwanan kika mik'e daga ciwon nan nak'i kuma duk akan Baby, yanzu dah ba Allah ya taimakeki na shigo rayuwarki cikin sauri ba, ai dah ba karamar wahala zaki sha ba, ki d'aure ki cireta a ranki tunda ga baby rukky nan Sadiya ta baki...

"Hmm lallai ka cika son kan ka da yawa yanzu kai in nace ka manta da Abdul zaka iya?.. wato babban d'an shi..

Had'e fuska yayi ko kallon ta bai sake ba, bare ta sa ran zai bata amsa, itama din shiru tayi tana tunanin sai yaushe zasu nemeta?.."

Tunda ta fito take mamaki ganin motar baby a harabar gidan, ji tayi gabanta yayi wata mummanar fad'uwa cikin sauri tace'" baby rukky fito!.."  ko da tazo inda take hannunta ta kama jikinta a sanyaye ta dube Alhajin dake kallon ta shima cike da mamaki yace" waye ya ajiye mana mota ba tare da neman izinin me gidan ba? ko kinyi bak'i ne suna ciki suna jiranmu?.."

Murmushin k'arfin hali tayi kana tace" eh zata iya faruwa mu shiga ciki koma dai waye zamu gani..."

Tun daga yanda aka hautsin falon Sauddat ta gama rikicewa, cikin sauri ta nufi d'akin Baby zuciyarta nayi mata wani iri, ko da ta duba bata ciki a yanda ta bar d'akin ma haka yake sai wasu kaya da ta gani daban bata kawo komai a ranta ba ta fito...

Cikin  muryarta me kama da shirinyin kuka tace" irin k'aunar da kika nuna mun kenan? wannan shine so na gaskiya kenan? amanar kenan akan ki narasa mutuncine da darajata na y'a mace akan ki na rasa duk wani farin ciki nawa, inayi komai dominki ne Umma me yasa ke bazaki kwatanta mun son da nake miki ba ko yaya ne? hak'ik'a da kina mun son da nakewa Khausar dah ba inda zaki tafi ki barni! shekara gudu kin manta dani kin kaffa sabuwar rayuwa, yaushe zaki bar aikata kuskure ne Umma? a baya kin ce rubutacinyar kaddarace sai kin aure Salisu yanzu me kike nufi na sake aure ba tare da kin sanar da iyayenki ba? ko da gaske kin barmu kenan?.."

Kamewa Sauddat tayi jin tona sililin da Asiya ke mata domin ko da wasa bata gaya mai ta aure Salisuba bayan abbana ba, haka kuma ta boye mai asalin labarina...

Gaba ta na dawo gani ganin tana shirin wucewa hawaye har ya fara wanke min fuska nace" wai me kike nema ne? Umma shekara fa? dama zaki iya guje min a rayuwar? yaushe zaki fara sani farin ciki ne?..."

Hawayen ta share a sanyaye tace'" rukky ki wuce daki  ki jirani.."

Alhaji ya shafa ti'kek'en tumbin sa yace" akan me zo nan y'ata!.."

Har cikin ranta taji babu dadi, a hankali ta matso gaba na hannu na ta kama kamar wata bakuwata tace'" Baby na! kinfi kowa sanin irin k'aunar dake tsakanina dake har abada bazan taba tafiya na barki ba, a zahiri na tafine amma a zuciyarta da jinin jikina kece kullum kike yawo, a dalilin nesa da nayi dake kullum cikin fargaba nake kwana nake tashi, lefine daya ne kawai amma shi ya zamar mun dole nayi, dan Allah ki fahimci Ummanki! bana fatan ranar da zan sake aikata kuskure burina shine naga kina farin ciki, bana so na sake ganin hawaye akan  wanna kyakykyawar fuskar taki! ki yarda dani y'ata kece farin cikina duk akanki nake komai!.."

Soyayyar ta da tausayin ta gaba d'aya sun gama kashe mun jiki, ganin tana hawaye hakan ba karamin taba mun zuciya yayi ba, tabbas ina masifar kaunar uwata, bazan so ta k'asance a haka ba, jikina sanyaye na sunkuya inda take nima ina hawaye nace" bana so ki sake zubar da hawaye a ta dalilina burina kiyi farin ciki da ganinna, hak'ik'a ke uwace ta gari matsakarki d'aya tak Umma shima ina miki fatan nan gaba ki gane abinda muke nufi..."

" Zan gane ASIYYA insha Allah zan gane, kuma ku gane halin da nake ciki!.."

Ta fad'a tana rumgume ni hawayenta na zuba a gadon bayana, mun d'auki lokacin a haka kana na janye jikina ina share mata hawaye nace" meyasa kika tafi to?.."

" Ya zama dole ne! da na tafi ai kin samu damar kula da y'arki ko?.."

Murmushi nayi me had'e da kuka nace" ki bar zancen ta Umma , me yasa kikayi aure?.."

Zan gaya miki komai amma ya kamata mu barwa safiya!.." cikin lalami tayi maganar..

" Y'ar taki bata iya gaisuwa bane Sauda?.."

Cikin bazata maganar tazo mana..

Kallo na tayi had'i da marairaice fusaka, ji nake kamar ana soka mun mashi domin na fahimci me take nufi, a dak'ili nace" ina wunin ku?.."

Bai amsa ba sai ma hannu y'ar shi da ya kama yayi gaba, a raina nace zaka dawo ne...

...

Kuyi hakuri da wannan zaa cigaba insha Allah

YA ZANYI farin cikin yata shine burinaWhere stories live. Discover now