Prologue

17.1K 730 23
                                    

****

NEMAN MOH DA GAGGAWA!!!

Kai babana ne!!!

Bansan abubuwa da yawa ba akanka.Nadai san sunanka Fu.ad. Kuma kai dan wasan kwallon kafa ne saidai bansan ko wanne club ba.

Sannan da jimawa kana shaawar wasannin mota na stunts. Mutane suna kiran ka Moh.

An gayamun bakasan dani ba. Ancemun zan fahimta wata rana.

Ni nawa mai sauki ne.

Wannan shine : shekarata goma sha biyu. Mutuwa zan.

Nasan mamata ba zata taba jin dadi ba. Inaso inganka kamun in mutu.

Wata rana zata gane. Har yanzun tana sonka sosai.

Moh idan ka karanta wannan dan Allah ka dawo. Ba ma saika zama babana ba. Ba saikace kana so na ba ko kabani hakuri.

Kawai kazo kaganni.

Ina jira amman banida lokaci sosai.

Nana.

*

Ana gama karanto wasikar mug din coffeen dake hannunta ya subuce ya fadi ya ko tarwatse ko ina na kitchen din.

"Nanaaaa..........."

Sofi ta kwala mata kira cikin tashin hankali.

***     ***

".............Jana kin daina damuwa damu ko? Aikinki yafi maki muhimmanci? Good!"

Kamun tace wani abu ya fice ya doko kofar da karfi.

Wasu siraran hawaye suka zubo mata. Ta cire glass dinta ta goge su. Zuciyarta duk bata mata dadi tasan patients nacan sunata jiranta.

***     ***

Wani irin mari ya dauke ta dashi.

"Jakar ina ce ke? Bance miki bana son kara ganin waccen matar a gidana ba???"

Azabar marin da take ji baikai ta zuciyarta ba. Ga wani tsoro daya rufe ta.

"Dan girman Allah nawaf kayi hakuri wallahi........"

Wani marin ya sake wanketa dashi da sai da taga wani haske ya gilma mata kunnenta yadan daina jin iska sosai.

Wani mugun kallo ya watsa mata yace.

"Just two minute na baki ki fita ki sallame ta ki dawo ina jiranki............"

***    ***

"...........Na shiga uku zainab......!!!"

Ta karasa maganar tana durkushewa a wajen. Ta nemi hawaye ta rasa.

Numfashinta take jin yana wani sama-sama. Zuciyarta na barazanar daukewa.

Zainab kanta kallo daya zakai mata kasan ta girgiza. Murya na rawa tace.

"Suhaila muje asibiti a duba ni ban yarda da wannan test din ba......... "

Girgiza kai kawai suhaila take yana ganin abinda ta aikata ma kanta AKAN SO......!

***********

Kaddararsu tasha banban da juna sai dai zatai yawo ne akan titi daya.

AKAN SO labari mai taba zuciya cikin salo naban mamaki. Salon da baku taba ganin irin saba.

                   "Th£ £xceptioπαl"

          COMING SOON!!!

#AkanSo

Akan SoWhere stories live. Discover now