*This is how much i appreciate your comments and votes.
This chappy is for rukkzz and tatuh for being first to vote and comment. Thank you*
Kallon kanta take a mudubi. Wannan ne kaya na biyar data saka tana cirewa. Yanzun riga da skirt ne na atamfa brown.
Ya karbeta sosai. Ba wata kwalliya a fuskarta banda jagirar datai. A sati dayan nan da khadija ta koya mata jagira ta zama kwararriya.
Kaman ba ita ba. Ga hannunta ya sha kunshi. Har gida su khadija suka kawo mai kunshi jiya tai nata jan lalle da baki. A hannuwa da kafa.
Murmushi take ita kadai. Ba karamar kewar fu.ad take ba. Ji take yaki sauri ya karaso.
Sai kamshin turaruka take. Musamman humrar da anty fatima ta bata. Inta shafa saita wuni da ita a jiki.
Falo ta fita ta sake duba dining. Komai a shirye yake. Mama indo ta tayata gamawa tun dazun ta koma nata bangaren.
Window ta leqa ko zata ga ta inda zai bullo. Ta gaji da tsayuwa a wajen ta koma bedroom.
Sam ta kasa zama waje daya. Sai yawo take cikin gida. Dakin shi ta shiga da ta feshe da turaruka.
Ta zauna kan gadon. Ta lumshe idanuwanta ta bude su. Ta kagu yazo yaga yanda duniyar shi ta canza ta.
"Sofi........."
Muryarshi taji da sauri t bude idanuwanta. Baya cikin dakin. Zuciyarta na son fita daga kirjinta tabi inda taji kiranshi da yanda take doka mata.
"Sofi........."
Ta sake ji. Bata san sanda kafafunta sukai hanyar fita dakin ba. Tsakiyar falo taganshi tsaye hannunshi rike da akwati.
Sai jaka rataye a hannunshi. Tun daga takalmin kafarshi ja ta soma kallo zuwa crazy jeans din dake jikinshi blue. Sai hoodie din da yake sanye ita fara da ja.
Sannan ta tsaya kan fuskarshi. Hannuwanshi ya bude mata yana tarbarta da wani murmushi daya sa zuciyarta ci gaba da kokarin fita daga kirjinta ta same shi.
Kafafuwanta har sarkewa suke kamun ta karasa inda yake. Taimaka mata yai ta hanyar kamo hannayenta.
Su ya fara kaiwa bakinshi yana kissing babu kakkautawa. Ji yake kaman ya hadiyeta ya ciccike ramukan missing dinta dayai sannan ya fito da ita ya kare mata kallo.
Lumshe idanuwa tai tana jin dumin hannayenta cikin nashi. Labbanshi kan hannuwanta.
Sai taji kaman wani abu ya dan matsa cikin zuciyarta da batasan ba dai dai yake ba sai yanzun.
Dagowa yai ya kalli fuskarta. Wani abu ya fadi can kasan makoshi da ta kasa gane wanne yare ne. Kamun ya jata jikinshi yai hugging.
Tana jin yanda ya sauke wata ajiyar zuciya. Hannuwanta tasa a bayanshi tana kankame shi.
Cikin kunnenshi take fadin.
"Sannu da zuwa. Nayi kewarka sosai"
Kissin gefen fuskarta yayi kamun yace
"Ba sosai ba tunda kina iya dorawa akan kalamai"
Murmushi tayi. So take ta sake kallon fuskarshi amman zuciyarta na mata ihu saboda tunanin rabata da jikin fu.ad data keyi.
A hankali ya kamota yana dawo da ita zuwa ga dubanshi. Idanuwanshi ke yawo kan fuskarta.
Sai kace ba sofin shi daya tafi ya bari ba. Ta kara wani kyau. Sai yaga kaman yankan idanuwanta sun kara girma da wani haske.
Sumba ya manna mata a kowanne ido. Muryarshi can kasa yace.
"Kinyi kyau sosai"
Itama tashi fuskar take kallo. Akwai abinda ya canza mata. Gashin kanshi take kallo. Haba tasan ya canza ko yaya ne.

YOU ARE READING
Akan So
Romance"Tun daga ranar da ka shigo rayuwata komai ya dai daita" Da murmushi a fuskarshi yace "Bansan akwai abinda na rasa a tawa rayuwar ba sai da na mallake ki"