*Sorru for the late update. So so busy. Kuna raina*
Wani sama sama yake jinshi. Karar motocin dake wucewa can yake jinsu nesa. Saboda abu dayane kwakwalwarshi ke iya processing a yanzun.'Yar' shi na da cancer'. Can sama sama yake jin kamar muryar sofi na kiranshi. Bai ko bi takanta ba saboda bata gabanshi a yanzun.
Komai na rayuwarshi a gefenshi yake a ajiye. Nana ce kawai ya rike gam tun daya sauke idanuwanshi akanta.
Da gudu safiyya ta karasa bata damu da mutanen dake wurwucewa ba. Tasha gabanshi. Kallonta yake ya daquna fuska alamar bai fahimci me take yi ba.
"Badan na damu ba. Nana ta farka tana tambayarka........"
Jin sunan nana yasa shi ware idanuwanshi akanta sosai. A tsorace yace.
"No bazan iya ba. Bazan iya facing dinta ba.........."
Kallonshi safiyya take yanda yake girgiza kai yana daga hannuwa. Lokaci daya taga girman da fu.ad yayi a jikine kawai da fuska.
Har yanzun zuciyarshi akwai yarinta fal a cikinta. Sosai ta kalle shi.
"Shisa nace karta sake ta saka a zuciya dan bakata da wajenta....."
Wani abu yaji tun daga yatsan kafarshi ya taso mishi har cikin kirji. Safiyya na son kule shi ya kula. Baice mata komai ba ya juya ya na komawa hanyar asibitin.
Dan karamin murmushi tayi tabi bayanshi. Har suka shiga cikin asibitin. Yana zuwa bakin kofar dakin da Nana take ya rike handle din yai tsaye.
Gabanshi faduwa yake sosai. Nan safiyya ta karaso ta same shi. Kallonta yai kaman zaiyi kuka.
"Em' scared sofi......."
Sauke ajiyar zuciya tayi. Tana jin yanda duk inda ta cika da tsanarshi a zuciyarta ya fara gogewa. Sauke idanuwanta tayi.
Ta karasa ta raba gefenshi ta tura kofar ta shiga tabarshi anan tsaye. Kaman mai ciwon wuya yadan zira kai ya leqa.
Nana na zaune kan gadon suna hira da Ansar dake gefenta.
"Mai katon kan nan bai tafi ba kenan......"
Ya fadi kasa kasa. Shiga yai a ciki. Sai lokacin nana ta ganshi. Wani murmushi da tai mishi baisan lokacin daya mayar mata da martani ba.
Karasawa yai har inda Ansar yake zaune kan kujera. Hannuwa yasa bayan kujerar yaja ta baya ji kake wani qiiiiiiiiii.
Dariya ce ta kusan kubce ma safiyya ganin yanda Ansar ke ware idanuwa. Da alama ya tsorata sosai dajin yanda fu.ad yaja shi.
Yarinta nacin fu.ad har yanzun. Bata kuma san ranar dazai girma ba. Ko kallon su fu.ad baiba ya zauna gefen gadon Nana.
Hannu yasa yai cupping fuskarta yana kallon ta da murmushi a fuskarshi.
"Na dauka ka tafi. Mum tace mun kana nan. Na kasa yarda ne kawai. Kayi hakuri bani da lafiya ranar daka zo...."
Da sauri ya girgiza mata kai hadi da fadin.
"Shhhhh Nana. Wani abu na miki ciwo? Em' here now. Komai zaiyi dai dai. Ni da ke zamu yaqi ko menene kina jina ko?"
Wani irin tsalle zuciyar safiyya tayi jin kalmar nan ta 'ni da ke'. Mikewa tai da sauri ta karaso inda fu.ad yake. Cikin idanuwa ta kalle shi.
"Ina son magana dakai"
Ta buqata. Wani yatsina fuska yayi.
"Ina jinki."
Hanyar waje ta nuna masa da dan yatsanta idanuwanta cike da masifa. Kallon Nana yayi yace.
"Yanzun zan dawo......."
YOU ARE READING
Akan So
Romance"Tun daga ranar da ka shigo rayuwata komai ya dai daita" Da murmushi a fuskarshi yace "Bansan akwai abinda na rasa a tawa rayuwar ba sai da na mallake ki"