Thirty

5.7K 521 51
                                    

*The love da kuke da for this book shi yake karamun karfin ci gaba da updating. Sakonninku suna isomun sosai. Nagode nagode nagode*

Tun jiya ya kasa samun wani wadattaccen bacci. Haka ya daure yaje aiki. Yana tasowa ya wuce gida. Wanka kadai yayi.

Abincin ma dan zee ta tusa shi gaba babu inda zai fita babu komai a cikinshi yasa shi danci kadan.

Wani irin abu yakeji cikin zuciyarshi daya jima da manta yanda yake.

Tunani da mamakin yiwuwar samun ya a wajen fu.ad kawai yake yi. Tunani yake zuwansu nawa da shi da haneef gidan fu.ad.

A kulle sai maigadi. Karshe ma cayai musu an siyarma da wasu gidan. Har bichi sukaje asalin gidansu safiyya akace musu sun tashi.

Baisan ko haneef ba. Amman shi ya sake gwadawa bai samu safiyya ba sannan ya hakura. Wayarshi ya dauko ya kira haneef yaji ko yana gida.

Dan bayason ya karasa kuma ya samu baya nan. Kanshi tsaye ya wuce rijiyar zagi inda gidan haneef yake.

*

"Wai lukman sai kace wani bako"

Cewar haneef bayan sun gaisa da lukman din. Murmushi lukman yadanyi hadi da fadin.

"Ba jimawa zanyi bane shisa. Ya su ummie?"

Jingina da mota sannan ya amsa shi da.

"Suna nan lafiya. Ina junior da zainab?"

"Yana islamiyya daga nan zan biya in dauke shi."

Wayarshi lukman yasa hannu a aljihu ya dauko ya budo sakon da hamza ya turo mishi kamun ya mikama haneef.

Karba yai ya karanta saqon. Cike da rashin fahimta dakin yarda da abinda idanuwanshi suke ganar mishi ya dago ya kalli lukman.

Wani murmushin takaici lukman yai hadi da fadin.

"Yar fu.ad ce haneef....."

Girgiza kai haneef yake cikin rashin yarda.

"Bazai yiwu ba lukman. Kawai dai wata ce daban. Ta ina?"

"Wallahi yar shi ce. Naganta da idanuwana. Idanuwanshi. Fuskarshi komai haneef........"

Sau uku haneef na bude bakinshi yana mayarwa ya rufe. Ya rasa meya kamata yaji.

"Na kira shi jiya. Na fada mishi ya dawo kamun ya sake wani kuskuren.

Bamu kadai zai rasa ba wannan karin. Inajin ba tada lafiya yarinyar. Tana bukatar shi"

Wayar haneef ya mika ma lukman yana jin wani abu ya tsaya mishi a wuya.

"Da baka bata lokacinka ba. Ba dawowa zaiba lukman. Kanshi kadai yasani. Bana tunanin zai dawo saboda wannan yarinyar"

Jinjina mishi kai lukman yai. Dan yafi kowa sanin halin fu.ad. Ga shi baima fada mishi dalilin daya sa yace ya dawo ba.

Saikace baisan yanda fu.ad yake da umarni ba. Sauke numfashi yai yace.

"Safiyya na garin nan haneef"

Wani abune ya fadoma haneef. Kar dai ace safiyya bata bar gidan nan ba. Kawai tasa ace bata nan ne.

Kallon lukman yai yace.

"Kasan me. Jeka dauko junior daga islamiyya. Zan dubo safiyya i will call you ko me ake ciki.

Zan manta yanda na tsani fu.ad a yanzun saboda indai wannan yarinyar yarshi ce tana bukatar family dinta"

Dariya lukman yai ya girgiza kai kawai ya bude motarshi ya tafi. Tsanar fu.ad itace abu na karshe da yasan zuciyarsu ba zata iya ba.

Akan SoWhere stories live. Discover now