Thirty-four

6.1K 683 59
                                    

*PLEASE DON'T BE A SILENT READER. IF YOU LIKE MY STORY VOTE AND SHARE PLEASE. COMMENT LEMME KNOW WHAT YOU THINK ABOUT MY STORY. THANK YOU ALL*

Da sallama ya tura kofar yana shiga dakin gefen gadon Nana ya zauna. Idanuwan nan nata ta ware kan fuskarshi.

Yai mata murmushi hadi da fadin.

"Ruwan nan kawai zai kare mu tafi gida"

Safiyya dake gefe taja numfashi tare da cewa.

"Me kaje kayi?"

Cikin fuska ya kalleta. Ya wani yi narai narai da idanuwa.

"Nikam me zanyi?  Rokonta nai kawai"

Tabe baki safiyya tayi dan tasan roko yana karshen littafin fu.ad da ba kowane yake gani ba. Da fara.a Nana tace.

"Thank you M"

Da confusion yake kallonta.

"M?"

Ya maimata da alamar tambaya. Puppy eyes Nana tai tana fadin.

"Oh-oh......"

Daga mata gira fu.ad yai yana dan daquna fuska alamar ita yake jira tai masa bayani. Kallon safiyya tayi tadan daga mata kafada dake nufin ita ta fara saita karashe.

Sauke numfashi Nana tayi. Cikin sanyi murya tace.

"Mumy ta fadamun kana stunts da. And ana kiranka da Moh. Ina tsoron kar in claiming wani dangantaka tsakanin mu kaqi dawowa.

Shine nake kiranka M. M koda yaushe"

Wani abu yaji yai squeezing a kirjinshi. Safiyya ya zuba ma idanuwa yana tunanin meye abinda ta gaya ma Nana dazai saka ta wannan tunanin.

Tambayar shi take karanta cikin idanuwanshi batare daya furta ba. Hade fuska tayi dan bata son meyake so da ita ba. Bayan ya watsar da ita tsahon shekarun nan.

Tun dawowarshi safiyya ke bata mishi rai. Kaman duk tsahon shekarun nan data ja mishi nisanta da ita bai ishe shi ba. Saita kara da saka ma yarshi wannan tunanin.

Baisan lokacin dayace.

"Shekararta nawa?"

Yana jin wani zafi a kirjinshi. Batare da fahimtar dalilin tambayarshi ba safiyya tace.

"Eleven...."

Lumshe idanuwanshi fu.ad yayi yana dafe goshin shi dayake jin wasu abubuwa na mishi yawo. Shekaru sha daya na rayuwar Nana ya rasa.

Mikewa yai. Yana son fita yadan sha iska kamun ya fadi wata maganar da baya so Nana taji. Jiyai an riko hannun shi. Juyowa yai ya kalli Nana da idanuwanta suke cike da hawaye.

Girgiza mishi kai tayi.

"I am sorry na kiraka M. Bansan wanne suna kake so ba. Please karka tafi"

Wani irin rauni zuciyarshi tayi. Numfashi yake fitarwa da sauri sauri saboda yanda yake jin gara ace asibitin nan ne ya baje da hawayen dake cikin idanuwan Nana.

Da sauri ya samu waje gefenta ya zauna. Hannuwanshi yasa ya tallabi fuskarta. Muryarshi a dakushe yace.

"Babu inda zani Princess. Ina nan tare dake........."

"Ummmm"

Safiyya ta fadi alamar bata kama zancen ba. Yana jinta hakan kuma ya mishi ciwo ba kadan ba. Zai sauke mata in basa gaban Nana.

Zai iya daukar duk rashin kunyarta data koya yanzun. Banda gaban Nana. Karshen abinda zaiso shine tasa ma yarshi yi mishi wani kallo na daban.

Mikewa safiyya tayi ta fice ta na dan doko kofar da karfi. Yabita da kallo kamun ya mayar da kallonshi kan Nana datai murmushi tace.

Akan SoWhere stories live. Discover now