Seventeen

5.4K 469 10
                                    

             Luβπα Sufyαπ

This page goes to ummu basheer for being the first to comment
And to the first to vote on page 16 am so sorry i couldn't place your name.

Let's see who are the winners of chapter 18.

Thank you all.

"Inalillahi wa ina ilahi raji.un....."

Momma ta fadi hayan haneef ya gama gaya mata kome yake faruwa.

"Yanzun duka fu.ad din nawa yakeHankalin kirki bashi da shi haneef"

Jinjina kai yai ya gyara zama yace.

"Nasani momma. Amman ki kalli fa abinda yake yi. Wallahi zai iya samun matsala. Nikam dai a taimaka aje aji"

"Hmm bayan tozarcin dayai musu kana zaton zasu saurare mu neKafi kowa sanin halin abbahnku. Da wahala yaje"

Shiru haneef yadanyi kamun yace

"In yaga yanda fu.ad ke shirin zaucewa zaije. Nasan bashida wani hankalin kirki. Amman wallahi yana sonta. Kema kinga alama ai"

"Kai. Oh Allah na"

Momma ta fadi tana sauke numfashi. Wannan wacce irin kaddara ce.

Ita tunda take inba a film ko a littafi ba. Bata taba ganin irin wannan abu ba.

Bama tasan ta yanda zata fara tunkarar abbah da wannan maganar ba.

"Barin je sallah"

Cewar haneef yana mikewa. Kai kawai momma ta iya daga masa.

*

Da yammacin ranar abbah ya dawo daga abuja. Sai da yaci abinci yai wanka ya huta sannan momma ke fada masa fu.ad bashi da lafiya.

Akan SoWhere stories live. Discover now