Fourty-One

6.1K 531 64
                                    

*Hakila babbar kyauta da zaka samu a duniya itace ta 'Ya'ya. Idan har ina jin yanda nake ji a zuciyata idan na dauki yaran wasu. Zan so sanin me ake ji randa zan rungumi nawa yaran. Allah ya azurta duk wani mai bukatar haihuwa da Yara masu albarka*

*Soyayyar iyaye wata baiwace da wanda Allah ya azurta da ita ne kawai zao fahimta. Allah ka sakama iyayen mu da mafififin alkhairi*

*TO ALL MUMS and DADS. Thank you for loving duk da ba zamu taba muku rabinta ba*

*#AnaTare*

Three piece suit yasaka Baki da fari. Bai sha wahalar dora ta saman ba dan baya son takura ko kadan.

Yanzun ma dan inda zashi baya son a mishi kallon karamin yaro kuma bashida wasu manyan kaya ko daya.

Dacan ma ba sakawa yake ba. Ballantana yaushe rabonshi da nigeria. Turaruka ya feshe jikinshi dasu sannan ya fito.

A falo ya samu su momma suna karyawa. Ya gaishe dasu a ladabce sannan ya zauna. Wata irin yunwa yake ji.

Sosai yaci dankali da kwan da momma ta zuba mishi ya hada da tea sannan ya mike yana fadin.

"Momma barin je in kawo Nana din. Amman ina so in biya ta gidan lukman dan karya fita aiki kamun in wuce in dauko ta"

"A dawo lafiya. Ka gaishe da lukman din. Nace kwana biyu bai kawomun junior ba"

Murmushi fu.ad yai hadi da daga mata kai. Ya maida hankalinshi kan abbah.

"Abbah bakaimun addu.a ba"

Murmushi abbah ya mayar mishi.

"Allah ya tsare ya sanya albarka"

"Amin. Hassan bai tashi bane?"

Fu.ad ya bukata. Momma ta amsa shi da.

"Ai ya tsufa wajen aiki. Yana rigan kowa tashi"

Wucewa fu.ad yai yana fadin.

"Alright. Saina dawo"

****

"Mumy dan Allah in kwana?"

Dan jim safiyya tayi tana jinjina maganar Nana din. Bawai bata so ta kwana bane. Tasan kewa zata dame ta.

Amman tana bukatar sanin dangin babanta. Suma su santa. Ko ba komai sun nuna mata kauna lokaci daya.

"Sai dai zaki tafi da magungunanki. Ki bama momma su duka"

Da sauri Nana tace.

"I promise zan sha duka. Nagode mumy"

Murmushi kawai safiyya tayi mata. Ta dauko mata kayan da zata saka da kuma wasu kala biyu sai na bacci sa takalma guda biyu.

"Mumy kibani cikin wanda dady ya siyo mun jiya."

Dan dafe kai safiyya tayi. Ta manta da kayan shaf. Mikewa tai taje ta dauko mata su. Ta zazzage wa.ancan daga leda ta saka mata sababbin.

Purple hijab din data dauko mata zata mayar. Ta rike da fadin.

"Zan sa wannan"

Sakar mata safiyya tayi. Ta barta anan tana daukar wani riga da pencil trouser cikin wanda fu.ad ya siyo mata. Tasan Nana bata son a tayata shiryawa inba bata da lafiya sosai ba.

Dan haka ta shiga wanka tabarta anan tana shiryawa abinta.

****

Fu.ad bai samu junior a gida ba. Kasancewar juma.a ce ya tafi makaranta. Yau dai saida lukman yaja shi har cikin gidan suka gaisa da zainab.

Akan SoWhere stories live. Discover now