Luβπα Sufyαπ
*19/02/2017*Farar suit dinta ta dora saman kayan jikinta sannan ta sanya qaramar hijab itama fara.
Tayi matuqar kyau. Ta dauki qatuwar jakarta sannan ta manna glass fari mai ratsin zaiba.
"Honey J zamu fita tare ne?" Ta buqata.
Tun jiya yake sha mata kamshi. Tayi lallashin duniya. Yauma sanda ta tashi tagama hada komai.
Tabar Atika ta karasa shirya mata umar dan yasir ya iya komai da kanshi.
Bai jirata ba yai breakfast dinshi. Gaisuwarta ma dakyar ya amsa.
Idanuwansa da suke dagula mata lissafi ya kafa mata.
A daburce tace"alright bara na wuce kawai may be........."
Katseta yai da fadin
"Jana wato rayuwar wasu tafi maki muhimmanci akan tamu right?"
Ta lumshe idanuwanta ta budesu sannan tace
"Na dauka mun gama maganar nan fa"
Saukowa yai daga kan gadon yazo inda take ya tsaya suka fuskanci juna.
Idanuwansa ta kalla sosai yauma rikici yake ji ita kam ba zata biye masa ba.
Juyawa tai da niyyar tafiya ya janyo hannunta hadi da fadin
"Jana kina da hankali kuwa?"
Zuciyarta ke wani irin dokawa duk da hakan ba baqon abu bane in har jikinsu zai hadu ita dashi.
"Ikram ce kwance a daki"
Ya furta a dake.
Saida ta hadiye miyau dan bakinta ya bushe sannan tace masa
"Nayi mata komai da take buqata bacci ma take and Honey J ikram ba qaramar yarinya bace dan qaramin zazzabi duk ka wani damu"
Kallon da yake mata yasata yin shiru. Har wani huci yake,muryarsa daqyar take fita yace
"Karamin zazzabi? Jana kin daina damuwa damu ko? Aikinki yafi maki muhimmaci? Good!"
Kamin tace wani abu ya fice ya doko qofar da qarfi.
Wasu siraran hawaye suka zubo mata.
Ta cire glass dinta ta sa hannu ta goge su.
Ji take zuciyarta duk bata mata dadi. Tasan yanzun haka patients nacan sunata jiranta.
Fitowa tai zuwa falo. Ta samu Jabir zaune kan kujera. Tazo wucewa ta kalle shi ya watsa mata wani kallo.
Har takai qofa taji ikram tace mata
"Mami yauma fita zakiyi?"
"Ya Allah"
ta furta cikin ranta ta bude baki zatai magana jabir yace
"ikram dakin koma kin kwanta ni zan zauna tare dake."
"Thank you pa"
Ikram ta fadi tana wucewa.
Jana ta kalli jabir da ya dauke fuska yana ta dacin rai.Addu.a tai sannan ta fita daga cikin gidan zuwa inda motarta take.
*
Kafa yasa ya ture table din dakin yana fadin.
"Damn it"
Wayarshi ta soma vibrating cikin aljihu. Ya dauko ya duba.
Ayna ce. Ya daga hadi da fadin

VOUS LISEZ
Akan So
Roman d'amour"Tun daga ranar da ka shigo rayuwata komai ya dai daita" Da murmushi a fuskarshi yace "Bansan akwai abinda na rasa a tawa rayuwar ba sai da na mallake ki"