*Ina godiya sosai da dukkan support dinku. Luβπα Sufyαπ love you all.
Keep voting, commenting and sharing if you really like my story. Thank you*
Tana yin sallar la.asar ta koma falo ta zauna tana kallo. Tun da suka ci abinci fu.ad ya sake fita.
Anan ya sameta da ledoji a hannu da safiyya tasan kayan ciye ciye ne a ciki. Tun tana mamakin kalar cin abincin fu.ad harta daina.
Kasa ya zauna yana ajiye komai. Robobin ice cream ya fiddo guda hudu ya ajiye. Ya kalli safiyya da idanuwanta ke kanshi.
"Sakko mu sha"
Batai mishi musu ba ta sakko. Ta dauko roba daya ta bude. Harya soma koya mata yan ciye ciyen nan.
Bata ko shanye rabi ba ta ajiye.Dan yanzun tana iya fara tari. Sam basa shiri da sanyi.
"Kinyi me kenan?"
Fu.ad ya bukata yana ajiye robar daya shanye ya dauki wata ya bude.
"Na koshi. Saika yi mura ko?"
Ware idanuwanshi yai akanta. Yana ci gaba da shan ice cream dinshi. Hankalinshi ya maida kan film din da take kallo na hausa zuri.a.
"Wai duk yaran ta ne wannan ukkun?"
Ya tambayi safiyya ta amsa shi da.
"Eh mana. Abin sha.awa ko"
Yamutsa fuska yai hadi da fadin.
"OH-OH ..."
Da mamaki take kallonshi.
"Basu burgeka ba kenan"
Girgiza mata kai yayi.
"Ko kadan...."
Dariya ya bata.
"Inka haifi naka zasu burgeka"
Ware idanuwanshi yai akanta yana fadin.
"Wa? A duniyarmu babu yara sofi. Daga ni sai ke"
Dariya ya bata. Fu.ad akwai zolaya ta fadi a ranta bata ce mishi komai ba har akai magrib. Sannan ya fice masallaci.
Kwashe robobin ice cream din daya shanye guda uku tayi. Sauran nata kuma ta bude fridge ta saka in mama indo ta shigo ta bata.
Kamun ta wuce dakinta.
*
A kwance ta fito daga wanka ta same shi kan gadon yana danne danne da wayarta.
Zama tayi gefenshi. Ya dago ya kalle ta. Sosai yakai kanshi jikinta yana shakar kamshinta.
"Wanne irin turaruka ne wannan?"
Dariya tadanyi.
"Bansan sunan su ba. Anty fatima ta hadomun randa mukaje gidan tan nan"
Sake shaka yai yana wani sauke numfashi. Sun mishi dadi sosai.
"Nima a shafamun"
Hannunta ta goga a fuskarshi.
"Gashi nan"
Rike hannun yai.
"Wayau ko sofi?"
Boye kanta tai a jikinshi. Sumbatarta yai sannan ya jata sosai suka koma tsakiyar gadon.
Wata irin soyayyarshi yake nuna mata mai tsayawa a zuciya. Dakyar yakai hannu jikin switch din ya kashe musu kwan..........."
*
BẠN ĐANG ĐỌC
Akan So
Lãng mạn"Tun daga ranar da ka shigo rayuwata komai ya dai daita" Da murmushi a fuskarshi yace "Bansan akwai abinda na rasa a tawa rayuwar ba sai da na mallake ki"