*Kuyi hakuri. Saboda chapter din tayi tsaho bazan samu saka sakonninku ba. Kuci gaba da turomun ra.ayoyinku AKAN SO. Zamu hadu a chapter na gaba in shaa Allah. Nagode*"Ni dai ba surutu ba. Yunwa nake ji kazo ka dauke ni please"
Dariya lukman yayi ta cikin wayar sannan ya amsa da.
"Ni nace kazo babu sanarwa. But seriously ban sa ranka yau ba. Duka satinka uku ko?"
Daquna fuska fu.ad yai hadi da fadin.
"Oww lukman. Surutun nan in kazo munyi. Ka taho nidai"
Dan jim lukman yayi kamun yace.
"Ba wani dan ladabi"
"Please.."
Fu.ad ya fadi yana kashe wayar da alkawarin shake lukman in ya karaso.
So yake yaga fuskar sofin shi saboda sam bata sa ranshi ba. Daya kirata jiya harda kukanta saboda yace bazai dade ba yana kuma gaya mata saiya kara kwana goma.
Murmushi yake tayi shi kadai. Yana hango soyayyar da zai nuna mata yau din nan. Ji yake kaman yai tsuntsuwa ya karasa gida.
Motar lukman ya hango. Ya mike bashida kayan komai sai jakar system dinshi. Hannunshi cikin aljihun 3-quarter dinshi ya taka zuwa inda lukman yai parking.
Ya bude motar yana fadin.
"Allah yai maka yanda kamun lukman"
Dariya yai yaja motar.
"Ya hanya?"
Lukman ya bukata. Hararshi fu.ad yai ya sake yin dariya.
"Da na taimaka nazo? Bacci nake wallahi ka wani tashe ni"
Wannan karin fu.ad din ne yai dariya.
"Haneef na kira nace yazo ya daukeni. Zagina ma yai"
"Madallah. Nima kawai saboda safiyya. Da sai dai ka shiga taxi"
Hira suke jefi jefi da lukman har suka karasa. Bai shiga da motar ba iya kacin shi kofar gidan fu.ad din.
"Zan shigo anjima in shaa Allah. Ka gaishemun da hajiya please"
Tabe baki lukman yai.
"In ka shigo kaje da kanka"
Ficewa fu.ad yai daga motar yana fadin.
"Zanzo dinne ai. Sai anjima"
"Ka gaida safiyya....."
Wucewa fu.ad din yai. Lukman ya juya da motar.
*
Zaune take kan kafet tana yanke farce. Kwankwasa kofa taji anyi. Bata kawo ma ranta komai ba tace.
"Shigo....."
Zatonta ma anty laurat ce. Tunda suna hutu yanzun. Wani lokacin indai ta fito takan biyo su gaisa da safiyyar.
Dago kai tayi dataji an turo kofar. Wani ihun murna ta saki ta tashi da gudu ta karasa ta rukunkume shi.
Dariya yake shima hugging dinta yai sosai. Sun jima a haka sannan ya sake ta yana sumbatarta.
"I miss you sosai sofi"
Ta kasa daina fara.ar da take yi. Hannu tasa tana jan kumatunshi.
"Shine kace mun sai nan da kwana goma ko"
Rike hannunta yai yana fadin.
"Wayyo sofi. Yi hakuri ina son surprising dinki ne fa"Jakarshi tasa hannu ta cire daga bayan shi tana kama hannunshi. Kan kujera ta ajiye jakar a hankali dan tasan system dinshi ce a ciki.
YOU ARE READING
Akan So
Romance"Tun daga ranar da ka shigo rayuwata komai ya dai daita" Da murmushi a fuskarshi yace "Bansan akwai abinda na rasa a tawa rayuwar ba sai da na mallake ki"