Fourty-two

5.9K 499 57
                                    

*Tabbas duk wata daukaka bata zuwa ma bawa babu jarabawa a cikinta.*

*Da yawan kusancinka da Mahaliccinka da yawan kaddarar dq zaka fuskanta. Allah ya bamu hakurin zama da juna. Allah ya bamu juriya da kauda kai daga zagin da muke sha a kullum*

*Habibtee Allah ya kara daukaka. Allah ya kara hakurin zama da mutane. Ki kauda kai. Ki toshe kunnenki.*

*#AnaTare*

Hannun Inna safiyya ta kara kamawa ta rike cikin nata. Dan gani take kaman zata bace kowanne lokaci. Dayan hannun ta kamo mayafinta tana goge hawayen da suke zubo mata.

Muryarta a dishe saboda kukan da takeyi tace.

"Inna kun yafemun da gaske?"

Kwalla Inna ta share tana daga ma safiyya kai. Ta mayar da kallonta zuwa wajen baba dake zaune yana kallonta ciki  da wani yanayi.

"Baba...."

Girgiza mata kai yayi alamar tayi shiru.

"Mun yafe miki safiyya. Duniya da lahira. Kema ki yafe mana bacin rai ne yasa muka ko....."

Da sauri safiyya tace.

"Baba kabari. Bakuyimun komai ba. Wallahi bakumin komai ba...."

Kasa karasa maganar tayi saboda wani abu daya tsaya mata a wuya. Kokarin hadiye shi tayi ta kasa.

Muryarta kasa kasa tace.

"Ina yaya?"

Wani murmushi Inna tayi da safiyya taji tana son ace itace sanadin bayyanarshi. Murmushi ne dake cike da alfahari.

Irin murmushin da kowanne da zaiyi farin ciki ace shine sanadin bayyanarshi a fuskar mahaifanshi kamun tace mata.

"Yana nan lafiya safiyya. Yana aiki a gidan radio. Da matarshi da ya'ya biyu"

Murmushi safiyya tayi kamun lokaci daya wani abu na daban ya maye gurbinshi. Har ranta take jin shekarun data rasa tare dasu da bazasu taba dawowa ba.

"Zanso ingansu"

Ta fadi a sanyaye komai na dawo mata.

"Zaizo ya kawo su anjima da yamma"

Baba ya fadi da kalar murmushin dake fuskar inna. Hade hannayenta safiyya tayi tana son taga sun kalleta da irin alfaharin nan.

"Kinbar mijinki a waje. Ba zakice ya shigo ba"

Inna ta fadi. Kallonta safiyya tai da sauri hawaye na sake taruwa cikin idanuwanta. Girgiza ma inna kai take wani kukan na kwace mata.

Ranar da fu.ad yabarta na dawo mata kaman lokacin abin ya faru.

****

Kofa take kallo tana son ta gasgata da gaske fu.ad yasa kafa ya fice bayan furta mata kalmar data wargaza duniyar da suka gina.

Kalmar dake barazanar tsayar mata da bugun zuciyarta. Mikewa tai hannuwanta na rawa take kallonsu. Kamun ta mayar da kallonta zuwa ko ina na dakin.

Da sauri ta karasa wajen kofa ta kama handle din ta bude jikinta na rawa. Kallon hanyar waje tayo taga ko alamar fu.ad bata gani ba.

Ya tafin da gaske. Zame jikinta tayi wajen kofar tana zama. Wani irin kuka ta saki daya fito tun daga zuciyarta da take jin tana tarwatsewa.

Sautin kukanta ne ya shigo da mama indo data zo wucewa taji ta. Ganinta durqushe tana wani irin kuka yasa mama indo karasowa inda take da sauri.

"Subahanallahi. Safiyya lafiya?"

Kamata mama indo tayi. Safiyya ta makale jikinta tana wani irin kuka mai taba zuciya.

Akan SoWhere stories live. Discover now