Sixteen

5.1K 464 5
                                    

             Luβπα Sufyαπ

*Ina godiya mai yawa ga masu mun fatan alkhairi. Allah ya biya muku bukatunku. Kuna zuciyar Luβπα ako da yaushe*

A daki yai sallar isha.i sannan ya fito ya sauka zuwa falo. Kujera ya samu ya zauna. Kowa nakan dining table suna cin abincin dare.

Hussaina ce tace

"Bro kazo kaci abinci"

Kai ya girgiza mata kawai. Baya son ko bude baki yai magana. Tasowa tai daga inda take zuwa tsakiyar falon.

Hannunshi ta kama tana kokarin janshi. A kasalance yace

"Hussaina ki kyale ni nikam. Em' not hungry"

Girgiza masa kai tayi cewar bata yarda ba.

"Ka taso kawai"

Kanshi yaji ya soma daukar chargy. A tsawace yace

"Wai bakyaji ne. Nace bana ci!"

A tsorace ta saki hannunshi tana matsawa. Kowa ma kallon shi yake. Yana da fada sun sani.

Amman su da wahalar gaske yai musu. Barshi can da yan aikin gidan. Balle ma hussaina da bayaso yaga ta bata rai.

Mikewa yai yanajin wani iri. Ko kallon inda suke baiba. Da gudu ya ke hada steps biyu a lokaci daya yahau sama.

Dakinshi ya shiga ya doko kofar da karfi kaman ita tai masa laifi. Kan gadon shi ya fada a kwance.

Ya rasa me yasa ya kasa controlling abinda yake ji. Bai kamata ace hussaina ta zama punching bag dinshi ba.

Wayar shi ya dauko. Ya nemo num din hussaina yai dialing. Ta dauka cikin sanyin murya tace

"It's okay bro. Kawai kome yake damunka ka fadama momma ko su yaya. Bama son ganinka haka"

Kai ya daga kaman tana ganinshi. Dan wani abu ya tsaya masa a wuya ya hana maganar fitowa. Yanaji tace

"Allah ya tashemu lafiya. Just be safe please"

Jin yai shiru yasa ta kashe wayar. A hankali ya saketa ta fadi gefenshi.

Yau ko kaya bayajin zai iya cirewa. Bacci yake jira ya dauke shi. Yasan mafarkinta zaizo. Zai dan ji sauki.

Amman yau baccin kanshi kokawa suke yi. Kokarin janyo shi yake yi yana kubcewa.

Har karfe biyu yana nan kwance. Juye juye kawai yake. Duk yanda ya kwanta yaki masa dadi.

Ga wani ciwon jiki da yakeji dabai san dalilinshi ba. Iskar dakin har wani kadan take masa. Saukowa yai daga kan gadon ya shiga toilet.

Alwala yayi. Yazo ya shiga sallah. Ita kadaice take samar masa da nutsuwa. Shima daya idar yake sake jin shi ba dai dai ba.

Nan kan daddumar bacci ya dauke shi wajen hudu. Kan kunnen shi aka kira asubah. Ya shiga yai brush ya sake yin alwala sannan ya fita zuwa masallaci.

Koda ya idar nan yai zamanshi. Ji yake kaman karya koma gida. Dan masallacin yana soothing mishi wasu wajaje da suke masa ciwo.

Har wajen shidda da rabi sannan dakyar yaja kafa ya dawo gida. Dakinshi ya shige ya kulle daga ciki.

Wanka ya shiga. Tunani ya masa yawa cikin kai. Yakai minti talatin cikin bathtub banda kafa babu abinda yake wankewa.

Sai da yaji ana kwankwasa mishi kofa sosai sannan ya dawo hayyacin shi. Da sauri ya karasa wanke jikinshi ya dauro towel ya fito.

"Waye?"

Akan SoDonde viven las historias. Descúbrelo ahora