Please do include a brother in you du.a Mustapha. May his soul rest in peace. Who knows you or you or me might need the same tomorrow or now.
May Allah ease our departure. Amin Ya Rabb.
Safiyya ya kalla yace.
"Barin ga haneef a waje"
Kai ta daga masa. Ya fice da sauri. Tun daga nesa daya hango haneef jingine jikin mota. Jikinshi sanye da manyan kaya ya daga hannuwanshi alamar surrender.
Yana karasawa ya wani yi rau rau da idanuwa hadi da fadin.
"Dan Allah kace ba fada zakaimun ba. Wallahi iya ba jiya ma nayi sub din wata biyu"
Haneef bai san lokacin da dariya ta kubce masa ba. Fu.ad ya wani dafe kirji dai dai inda zufiyarshi take yana sauke numfashi.
"Hankalina ya kwanta. Ina wuni"
Daure fuska haneef yai. A ranshi yana fadin. Dole ka gaishe dani tunda baka da gaskiya.
Idanuwa kawai ya zuba mishi. Abinda yasan baya so. Gara kai masa masifa a wuce wajen.
Cike da kosawa yace.
"Alright kamun fadan...."
Shirun dai ya sake masa.
"Please..... "
Hakan yasa haneef fadin.
"Bansan me zance maka ba fu.ad. Kome na fada ta gefen kunnenka zai wuce"
Da sauri yace.
"Zai tsaya ciki. Da gaske nake amman karkamun fushi. In babu kai bazan iya fuskantar su abbah ba"
Yanayin daya karasa maganar da wani sanyi yadan taba haneef din. Kallon shi yai da kyau.
"Bakajin magana. Abinda kai ba karami bane ba. Bance bazai yafu ba. Auren da aka gina ta hanyar da ya dace ma yana zuwa da matsala fu.ad.
Ballantana naku da babu amincewar iyaye ballantana albarkarsu.
Kasan rayuwarta ta gama canzawa kenan?"
Cikin ido ya kalli haneef yace.
"Nasani. Ina sonta sosai. Bani da wani zabi ne shisa"
Sai da haneef ya sake gyara tsayuwa tukunna yace.
"Na yarda baka da zabi. Amman kana da son kanka da yawa. I really hope zaka so ta rabin yanda kake son kanka"
Dariya fu.ad yai.
"Em' noh' dah' selfish fa. We good?"
Girgiza kai haneef yai.
"Not even close"
Mota fu.ad yaga yana niyar shiga ya riko masa riga da sauri.
"Fu.ad meye haka kaman yaro. Sakemun riga karka dakuna mun...."
Haneef ke fadi yana kiciniyar kwace fu.ad dayake rike dashi dam.
"Allah sai kace we good sannan"
Ikon Allah haneef ya ware ido yana kallo.
"Wai kai bakasan ka girma ba? Kana da aure fa yanzun. Haka zakai yara kai kanka yarinta bata gama sakinka ba"
Rigar haneef ya saki ya wani dakuna fuska yana fadin.
"Banda wajen yara a zuciyata. Naku kawai sun isheni....."
Girgiza kai kawai haneef yai yana bude murfin motar. Sake riko shi fu.ad yai.
![](https://img.wattpad.com/cover/99634546-288-k596773.jpg)
KAMU SEDANG MEMBACA
Akan So
Romansa"Tun daga ranar da ka shigo rayuwata komai ya dai daita" Da murmushi a fuskarshi yace "Bansan akwai abinda na rasa a tawa rayuwar ba sai da na mallake ki"