Twenty-five

5.8K 538 24
                                    

*Votes da comment dinku zai sa insa kuna jin dadin labarin. Zai kuma karamun son updating kullum*

Karfe uku da rabi a crescent tai mishi. Sai da ya fara shiga sukai magana da matar da zata dinga zuwa gida tana koya ma safiyya karatu.

Ba wata babba bace ba can. Yoruba ce sai dai taji hausa kaman ba gobe. Duka ba zata shige shekaru ashirin da hudu ba.

Magana sukai ta fahimta. Fu.ad yai mata kwatancen gidansu. Kusan unguwarsu daya ma. Layi uku ne tsakaninsu.

Suna gamawa ya fita waje ya tsaya jikin motarshi yana jiran safiyya ta fito. Sai ware idanuwa yake yaga ta inda zata bullo.

Hango ta yai rungume da litattafai. Wani murmushi ya kwace masa. Hango shi tai itama lokaci daya yaga murmushi ya bayyana a fuskarta.

Jinshi yake wani iri. Kamar da duk takun da take ta karaso wajenshi har iskar wajen canzawa takeyi.

Kaman ya ruga ya rungumeta. Tana karasowa tai masa kyautar wani murmushi daya taba mishi zuciya.

"Ina wuni"

"Sofi yan makaranta. Sannu da kokari"

Ya amsa. Dariya tayi. Ya bude motar ta shiga. Ya zagaya shima ya shiga yaja motar.

"Ya makarantar? Badai wata matsala ko?"

Girgiza masa kai tayi.

"Dukkansu suna da kirki sosai. Wasu ma sun karbi litattafaina zasu tayani rubutun da aka wuce ni"

Yaji dadin hakan. Yanda suka karbar masa safiyya.

"Babu wanda yai miki wulakanci dai ko? Daga daliban zuwa malamai"

Kai ta girgiza masa. Dan ita kanta ta yi mamakin yanda sukai mata karamci. Da sun fara mata turanci. A kunyace tace musu bata ji.

Mamaki kawai taga sunyi maimakon raini. Da alama dukkansu yan manyan gida ne. Dan haka ta amsa fu.ad da.

"Haka ma sukace zasu taimakamun. Gaskiya suna da karamci"

Jinjina kai yayi. Dan Allah ne kadai zai rabashi da duk wanda ya nemi ya raina masa safiyya ko ya wulakantata.

Suna isa gida tai mamakin ganin an bude musu gate. Kallon fu.ad tai yagane tambayarta tun kamun ta bude baki.

"Dazun yazo. An samo mana mai aiki ma"

Tadan ji dadi. Ko ba komai taji motsin mutum banda su cikin gidan. Tayata daukar litattafan yayi yana fadin.

"Anjima sai muje a siyo jakar makaranta"

Tare suka shiga ciki. Tun daga bakin kofa ya cire takalmin da socks din daya siya mata a makarantar.

Kauda su tayi waje daya. Sannan ta shiga ciki. Fu.ad yabi bayanta. Kan kujera ya ajiye litattafan nata.

Zuciyarta taji ta wani doka da su inna suka fado mata. Tana tuna yanda baba yaso ta ci gaba da makaranta data nuna tana so sai dai bashida karfin.

Zata so ace sun ganta a yanzun. Sunga yanda take makaranta data tabbatar tana da tsada sosai.

Tasan zasu ji dadi suga ta samu ci gaba a rayuwa. Ita tana nan bata san halin da suke ciki ba.

Bata san wasu hawaye sun zubo mata ba saboda wani nauyi da zuciyarta tayi.

Yaga tunani take. Hawayen dayaga ni a fuskarta yasa shi tashi da sauri ya koma kan kujerar da take.

Hannuwanshi yasa ya tallabo kafadunta. Jinshi da duminshi ya sa taji ta karasa karaya.

Akan SoDove le storie prendono vita. Scoprilo ora