BABBAN GORO...!
NA
KHADEEJA CANDY
_I dedicated this page to my special good friend of mine, Sweetheart you can do it no wrong, my happiness is all yours._
_More grace to your shining star's ROSE OKAFOR Rosy Lurv_WATTPAD @khadeeja_candy
BABI NA GOMA SHA BIYAR__15
Tana shiga ta faɗa saman gado tana kuka,ta tsora ta sosai da yadda taga Saif irin wannan ranar take gudu, daman hausawa suncd rana dubu ta ɓarawo,ɗaya ta mai kaya.
Wayarta dake saman kujera ta baɗo mata a rai,cikin rawar jiki taje ta ɗauka, ta shiga neman number Mummy. Sai da tayi mata kira biyu sannan ta ɗauka,“Dan Allah Momi kizo gidan nan yanzu ki ceci raina”
Cikin kuka take maganar tana gurfane a kasa kamar mai rokon gafara. banji mi akace mata ba na dai ga tana girgiza kai
“Eh Momi Saki zaiyi dan Allah kizo yanzu”
Nan ta kashe wayar, ta faɗi kasan carpet gana kukan dake zuwa mata har cikin ranta, ko kaɗan Huda bata son taga Saif yayi fushi da ita, musaman yanzu da take fushin nashi har a fuska, Saif mutun ne mai hakuri duk abunda take masa yakan shanye ya kyale ta idan har taga fushinsa a fili toh lallai ranshi ya ɓace sosai.
Cikin mintuna Ashiri da wani abu Momi ta iso gidan,Huda najin tsayawar Motar ta ta fito da gudu daga ɗakin ta nufo downstairs, Saukowarta yayi dai-dai da shigowar Momi falo, faɗawa Huda tayi jikin Momi tana kuka
“Faɗa min mi kikayi masa miya haɗa ku?”
Momi sai Tambayar take abunda ya faru,ita kuma ta kasa magana sai kuka take, duk hankalin Momi ya tashi,
“Saif ɗin yana nan ne?”
Daker ta iya ɗagawa Momi kai sai wani kara narkewa take kamar wadda akayi mutuwa
“Saifullah! Saifullah!!”
Kira Momi take kwala mishi kamar zata tada gidan,
Yana daga kwance ya soma jin kiran bai amsa ba dan bai ɗauka Momi bace duk da yaji kamar muryar ta, Sai da yaji kiran ya tsanan ta sannan ya tashi a kasale ranshi kuma aɓace ya nufi kofar fita,
Tsaye Yayi bakin Stairs ɗin yana kallon Momi da ke lallasar Huda tana harararsa, haka ya nufo downstairs yana mamakin abunda ya kawo Momi yanzu a gidan dan ba kasafai take zuwan gidan ba. Wata zuciyar tace masa Huda ce ta ta kira ta, Baki ya ɗan tsosa a ransa yana zata iya tunda ba kunya ne da ita ba,Har ya Karaso Momi bata daina Harararsa ba, cikin girmamawa ya gaisheta
“Momi ina wuni”
Bata amsa masa ba sai kawai ta haushi da masifa,
“Mi Huda tayi maka da zaka sake ta?”
Zaunawa yayi saman kujera yana maida numfashi, ganin hakan yasa Momi ta katsa masa tsawa kamar wani karamin yaro
“Ba da kai nake magana ba kayi min shiru ko nima shashancin zaka yi min?”
D'agowa yayi ya kalleta,
“Momi..-”
Sai kuma yayi shiru, Kallonsa Huda tayi da jajayen idanunta kamar munafuka wani ɓangare na zuciyarta tsoron abunda zai fito bakinsa take dan tasan Momi ma bazata raga mata ba sai tayi mata nata faɗan,
Ido cikin ido ya kalleta yana magana da Momi“Momi matsalar mu ce da kika sani ta baya Huda ba zata taɓa chanajawa ba sam,nayi faɗa har na gaji bata ji ni kuma na gaji gaskiya da halinta kuma nasha faɗa miki tun baya yau ba”
YOU ARE READING
BABBAN GORO
RomanceNOT EDITED ⚠️ "Kayi kuskuren fahimta Saif, babu soyayyarka a cikin zuciyata ko kaɗan" Kara matsowa yayi kusa da ita, ta yadda tana iya juyo bugun zuciyarsa, yace "Ki kalli kwayar ido na ki faɗa min baki sona ki karya ta kanki da kanki indai har da g...