BABI NA ARBA'IN

5K 596 64
                                    

Suna isa gida Part ɗin Daddy suka fara shiga, suka tarar da ya fita, a nan suka nufo part ɗin Momi, a parlour suka tararda ita zaune tare da bakinta suna tattaunawa, shigowar su yasa ta sallami bakin tana kallon fuskokin su,
Baba karami ne ya fara labarta mata abunda ya faru kamin Nasir ya ɗora da nasa, Saif ya kunna mata Audio recording ɗin taji komai, ba lamarin Huda ne ya bata mamaki ba na Safiyyah ne ya kiɗima ta sosai ganin a gidan ta tashi kusan ma itace ta raine ta amman ace ita ce ta shirya wannan mugun kulli gashi yarinyar a fuska kamar saliha,
sai a lokacin Momi ta soma tunano wasu abubuwan da taga Safiyyah nayi da kuma irin son da take yi ma Saif, sun taɓa wannan maganar ita da Lubna har Lubna takr cewa tana zarginta da shirya ma Minal wannan sheri amman Momi tace a a ganin kamar ba zata iya aikata mugun abu irin wannan ba,
Baba Karami ya nisa ya kalleta a natse

"Yanzu ni abinda nake gani shi ne kije asibitin gurin Huda ki duba lafiyar ta"

"Babu inda Momi zata je akan me? Wallahi Baba kaji na rantse ko toh wallahi ko sama da kasa zasu haɗe bazan mai da Huda a matsayin matata ba balle har naje duba ta dan haka Momi ma ba zata je duba ta ba dan xuwa duba ta zai sa tayi tunani ko za a yafe mata ne"

Saif ya faɗa kamar da faɗa, Momi ta kalleshi

"Ba kai ke da ikon yanke hukunci ba Saif sai Mahaifinka yazo duk yadda yace haka za'ayi"

"Ba zan ki yi muku biyayyah ba Momi, amman wallahi ba zan sake zama da Huda a matsayin mata ba"

Nasir ya kalli Momi

"Momi ni abunda nake gani shine a barta har tayi nadamar abunda ta aikata, mu mai da hankali gurin Minal yarinyar nan lafiya ma bata ishe ta ga kuma baby dake cikin ta, idan muka bata kula har ta haihu a nan ne zamu tabbatar da baby na Saif ne ko kuma ba nashi ba"

Shiru Momi tayi alamar nazari ita kanta tana ji a jikin cikin da yake jikin Minal na ɗanta ne, sai dai tabbaci ne ba tada shi ta daɗe tana son taga ɗan Saif gudan jininta,

"Haka ne amman Sai mahaifin ku ya dawo duk yadda yace haka za'ayi"

Da wannan sukayi mata Sallama kowa ya kama gabansa.
A asibiti Saif ya tare, bai dawo gida ba sai dare a gidansa ya fara isa sai da yayi wanka ya canja tufafi sannan ya fito ya nufo Gidan gurin Momi, Kannensa kawai ya tarar a part ɗin dan momi tana part ɗin Daddy.
Bayan ya ɗan zauna ya nufi dinning ya zuba ma kansa abinci, yana cikin ci wayarsa tayi ringing ɗauka yayi ya duba ganin number Daddy yasa shi saurin yin picking,

"Ina nan gida, toh gani nan zuwa"

Shine kawai abunda ya faɗa ya sauke wayar, ya tashi daga cin abincin da yake ya zari kyale ya goge bakinsa ya nufi part ɗin Daddy,
Da sallama ya shiga Momi ta amsa masa bayan ya zauna ya gaida Momi da Dad momi ce kawai ta amsa Daddy kan harara kawai yake watsa masa,

"Ashe baka da hankali Saif, na yi tunani kasan mutun ci ashe ba ka san shi ba suma sunyi tunanin hakan shiyasa suka ɗauki yar su suka aura maka
A tunani na kasan meye aure ashe kai wawa ne kana girma kana cin kasa kana son zubar ma da kanka mutunci kana son ɓata tarbiyar da na shekara ina gina ka akai buɗewar ido yasa ka manta kowa a gaban ka ka aikata abunda Allah baya so, har yaushe zaka zama cikakken namiji mai daraja ka rasa inda zaka sakar musu ya sai a gaban idon su bayan ka gama aiban ta musu ita,
Daman kasan baka isa aure ba kaje ka nema! ba kai ne na frko da na fara aurar ba babu wanda ya taɓa zuwa min da wata matsala sai kai ka tsiri auren mata biyu da kuruciyar ka, yanzu kuma kana son ka maida kanka mai auri saki ko.?"

Sai a lokacin ya ɗan dago kai ya kalli Daddy,

"Wallahi Dad ba haka bane ita da kanta ta amsa ta aikata kuma ina da sheda akan haka Dad....."

Dad ya katse shi a tsawace

"Shedar banza da wofi, na fahimci ka fara shaye-shaye kuma har yana kokarin taɓa maka kwakwalwa ya mai da kai mahaukaci har yar uwarka kana kokarin yi mata sheri"

BABBAN GOROOnde histórias criam vida. Descubra agora